← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 1 OF 52

Sashe 1

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

[9/14, 12:55 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/8, 8:03 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul 1⃣ Tsaye nake bakin titi amma hankalina gabadaya baya jikina, tinanina kachokan ya dunguma a tunanin dream man dina, inata tsara irin rayuwar da zamu tsara a gidan aurenmu, amma abinda zai baka haushi shine kwata-kwata wanda nake tinanin bai masan abunda nakeyi ba, hasalima ko sunansa bansani ba, qarar wata babbar motace da ta doso wurin ta dawo dani hayyacina, da gudu na tsalakka titin tareda haushin kaina da nikeji, watarana sai na halakka kaina akan tinanin abunda bazan ta6a samu ba.
A haka na doshi gidanmu, na tura dan qyauren gidanmu na shiga gida, na kama hanyar wucewa dan akurkin dakina naje na dasa aya a inda na tsaya na tinanin abunda bazai fishsheni ba, tsawar da mama ta dakamin ita ta katsemin hanzari, wai ke meh yake damunki zaki shigomin gida ba ko sallama, sannan maimakon ki gayamin saqon da na aikeki, kin wani wuce soqoqo zaki wuce daki, ki kwanta kina tinane tinanen iskancin da kika saba, dan narasa meh yake damun qwaqwalwarki,
juyawa nayi da niyar inkoma inyi sallamar da banyi ba, mama ta katseminb hanxari hanyar tambayata saqon da ta aikeni.
Nace mama wlh hajiya abu tace wai ita batada kudin da zata ranta miki, ko wanda ta baki kwanan baya sai daqyar kika........ Mama ta dagamun hannu ya isa haka, badai biyan buqata karki isheni da surutun banza wuce ki ban wuri, na wuce dan dakina ina qunquni, toh ni miye laifina daga zanfadi abunda aka gayamin, mama cikin tsawa tacemin ni kike zagi? Na wace dai ban tanka mata ba.
mama kenan mutum ce mai fada da saurin fushi, amma kuma akwai saurin sauka, ni har na saba da halinta shiyasa ma idan tana masifarta bana tankamata.
[11/8, 8:53 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
2⃣ daki na fada na kwanta bisa lotsatstsiyar katifata da tasha jiki, da wani kodadden bed sheet dina, da wani pillow na kamar an latse bread, ina jimami, duk da mahaifiyata masifaffiyace amma ina tausayinta, tin bayan rasuwar mahaifinmu itace taketa dawainiya damu danida qannena guda 4, nice first born khadijah amma anfi kirana da ameerah, sai qanena mai bimun Aliyu, sai suhaila, fatima da kuma autanmu umar but muna kiransa da khair.
Mahaifinmu shi kadai ne a wurin mahaifiyarsa, but yanada step brothers guda biyu, mahaifiyata ma haka ita kadaice a wurin mahaifiyarta, amma tanada alots of step brothers and sisters, kuma mahaifiyarta er dangi ce sunada yawa a famly dinsu, but duk da wannan en uwa na mahaifiyata ba mai taimakamana da qwandala, idan ba wata er yayar mahaifiyarta ba da ta tashi a wurinta, itama din ba wani qarfi ne da ita ba, dan haka mama ce ke fadi tashi na ganin munsamu rayuwa mai kyau tareda ingantaccen ilimi.
Inada burin na tallafawa mahaifiyata tareda qannena amma ba dama, dan yanzu nake 200level a jami'ar usmanu danfodio da ke sokoto, inda nake karanta biology, wanda ada burina baya wuce inzama likita amma kuma nayita nema bansamu ba, mahaifina ne ya qaramin qarfin guiwa na kar6i abunda na samu arzikin mutum baya wuceshi, a haka na haqura nake karanta biology.
Ina 100 level ne Allah yayiwa mahaifina rasuwa, wanda mutuwar sa taso ta zautani coz my father is my best friend, da taimakon addu'oi da mama tasa akemin aka samu nadawo hayyacina.
[11/8, 9:13 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
3⃣ qwallamin kiran da mama tayi ya dawo dani daga duniyar tunanin da na tafi, na tashi da sauri na fito dan inji kiran da mama kemin, nera hamsin ta miqomin kar6i wannan kije wurin isuhu ki samo kayan miya ki dora ko jolop rice ce kafin qannenki su dawo su isko ba abinci a gidan, na koma daki na zunbulo qaton hijabina na fita siyen kayan miya,
Tafiya nake kaina a qasa, kamar ance dago kanki, idona karaf akan kyakkyawar fuskarsa mai cike da annuri, tsaye nayi na zama statue a wurin na saki baki da ido ina kallonsa bana ko qyaftawa, tamkar wata mayya ina ayyanawa a zuciyata wannan hadadden guy din idan yazama nawa zan shana, dan na huce takaicin da namiji a duniya, karaf najini ta ti6is a qasa, na qwalla qara, ashe wasu shanu ne sukazo wucewa nikuma na tafi dream land, banma lura ba, shine har wata ta tureni nasha qasa😢 tashi nayi na kakka6e jikina ina qwalla gashi na goge a qafa, Allah dai yasa ban karye ba😂, mai kiwon shanun ne yayo kaina yana fadar enmata shannu, inji bakaji ciwo ba, naji kamar in falla masa mari, nace cikin tsawa eh malam wuce kabani wuri kabarni naji da daya, da qasar da nasha zanji ko da asarar ganin dream man dina da kamin zanji, shidai bai fahimce mai nike nufi ba ya miqomin ledar nono wai ga wannan, har da zanqi kar6a sai naga da inyi 2-0 gwanda na kar6i kindirmon, na qwata da qarfi nace angode nayi gaba abina
[11/9, 12:30 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
4⃣ agurguje na wuce ina jefa qafata, naje na siyo kayan miya, da sauri - sauri na dawo gida dukda naji ciwo a qafata, koda nashigo gida su khairi sun dawo, mama ce takemin kallon tuhuma, meh ya tsaidake, nafara inda-inda, wlh mama shanuwa ce ta tureni a hanya shiyasa na makara ina qwalla😢 jibi qafata duk na goge, su suhaila ne suka kwashe da dariya, na tashi nayi kansu, mamace ta tsaidani karki illatamin yara, ai indai baki daina wannan yawan tunanin da kike ba to wlh watarana ma sai ansaceki a hanya baki saniba, bani kayan miyar nan, ta zabce leda tabarni anan tsuru-tsuru kamar anturke 6arawo, ina wani rau-rau da idona alamar zanyi kuka, mamace tace 6acemin dagani sakarya kina girma kina chin qasa.
Da gudu na wuce dakina ina fadan nidai gidannan duk antsaneni ba mai sona, sudai su suhaila sunsamu abun dariya, niko duk na qule, na shige daki na rufo qofar, mama tace ku qyaleta idan yunwa ta isheta a fito dan kanta.
Haka akayi kuwa ina daki ina sana'a dan nashiga duniyar tunanin dream man dina, nama manta da abunda ya faru, yunwa ce ta tasani gaba, nafito waje ina neman abinci na, haka nasamu kitchen wayam, nafara zare ido, naje nasamu mama ina wani 6ata fuska, mama banga abinci na ba, ta kalleni ta watsar kije tunanin da kike ya baki abinci. Haushi da takaici ne ya kamani, na koma akurkina na kwanta ga azabar yunwa inaji, chan na tuna da kindirmo na, haka na tashi jikina har rawa yake na dauko leda na kafa kai, nonon ko suger babu amma haka na shanyeshi tas, sannan najini nadawo normal, na godewa Allah sannan na godewa dan fillo da yau yunwa ta illatani.
[11/9, 3:29 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
5⃣Suhaila ce ta bankado qofa ta shigo, mama tace ga abincin nan idan kinga dama kici, nayi kamar banjita ba, ta gaji da tsayuwa toh bari naje na gayamata kince bazakici ba ta kama hanyar fita, miqewa nayi cikin hanzari na kar6o kwanon, marar kunya bani nan kuma ki fice kibani wuri, tafita tana dariya ashe kowa yace duhu baiji zawo ba, duk da yanzu banajin yunwa nasan kindirmon da nasha ba wani riqeni zaiyi ba, inhar nabari ta tafi da abincin na kade dan mama bazata saurareni ba.
Komawa nayi na kwanta ina aikin da nasaba, Aliyu ne ya banko qofar ya shigo, miye haka zaka fadowa mutane a daki ba ko sallamah, tsaki nayi najuya mishi baya, haba sweet sis daga nazo na ganki naga kindaina zama a waje duk sanda na shigo bana ganinki wai meh ke damunki ne sweet sis, bakomai nace masa banajin dadi ne.
Hmm sis kenan ai kinsan in zaki 6oyewa kowa damuwarki alinki bai dace ki 6oye masa ba, miqewa nayi zaune na nisa sannan nace my sweet bro bakomai wlh wani guy ne yake chazamin qwaqwalwa, ya hanani sakat tunanin sa nake day and night, Aliyu ne ya sake baki yana kallona, sannan ya kwashe da dariya saida yakai qasa, sis kece kike gayamin wani guy yana chazamiki brain.
Cow face nayi nace kaga idan dariya zakamin gwanda tun muna mu 2 ka kama gabanka
[9/14, 12:55 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/9, 3:43 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
6⃣ Aliyu yace sorry sis abunne da mamaki keda kikewa maza kallon banza bakya kula kowa yau kece da fadan haka, Aliyu baku fahimceni bane, ina mace baikamata na riqa kula kowanne namiji ba, idan har banaji ina ra'ayinsa ba shiyasa kaga bana kula kowa dan banaso na 6ata time dina a banza, kuma ma samarin yanzu majority duk en iska ne aliyu.
....... Toh sis yanzu dai ba wannan ba ma who is dis lucky guy, ya sunansa kuma a ina yake, rau nayi da ido sai hawaye Allah nima bansani ba bro, kamarya dai bakisani ba sis, joke apart plz nace wallahi bansani ba aliyu, lura da yayi yaga hawaye a idona yasa yayi shiru na dan wani time, anya sis ba gamo kikayi ba kuwa, Aliyu ba wani gamo, mutum ne kamar kai, miqewa yayi lallai sis abun naki azimun ne, toh ki dage da addu'a Allah ya za6amiki abunda yafi zama alkhairi, nima kuma zan tayaki, nace daz my lil bro daz y i love you alot, yace i love u too sweet sis nidai nafita, nace adawo lfy ina murmushi.
Aliyu kenan yaro mai tunanin manya qanena ne amma munshaqu sosai rigimar nan ta mabiyi da mabiyi duk bamayinta, indai kaji ina fada a gida toh da su suhaila ne.
[11/9, 4:08 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
7⃣ ranar dai ahaka na wuni a daki na kwana sallah ce kawai ke tadani, gari na wayewa bayan na tashi na taya mama ayyukan gida, na gama na kwaso kayana nafara wankewa, mamace ta kwasomin kayan su suhaila ta zubomin gashinan ki wanke, dan naga yanzu tinda kina hutu ba aikin da kike sai zama a daki, na rasa meh kike qullawa a ciki, baki na turo alamun zanyi kuka, haba mama ni gaskia bazanyiwa marar kunyar yarannan wanki ba da girmansu, ni kayan khairi kawai zan wanke, saidai idan naki zaki kwaso, mama tasan halina indai banyi niyyar abu ba ko ta tilastani yinsa bazanyi mai kyau ba.
Kamar tasan meh ke raina ta kwashe kayan su suhailan ta qaromin na khairi, nayi murmushin mugunta nace wlh da tsundumasu a ruwa kawai zanyi in tsame in shanya, mama dai juyawa tayi Allah ya shiryeki nace ameen ina dariya.
Koda nagama wankin duk nagaji zuwa kawai nayi na kwanta sai bacci, ban farka ba sai 3.pm da sauri na miqe nayi alwala na bada azahar sannan na shige wanka koda na qare shiryawa ankira la'asar nayi sallah naci abinci
Ji nayi kawai zaman gidan ya isheni, nafita waje nacewa mama zanje gidansu saudah, batayimun gaddama ba tace adawo lfy.
[11/9, 6:03 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
8⃣ saudat qawa tace da muka taso tun muna yara muna qawance, saidai ita daga secondry school muka rabu dan ita bata cigaba ba, duk da tanada ra'ayin hakan amma gidansu daga ankammala secondry sai aure, saidai idan mijinki ya amince kicigaba a gidansa.
Tafe nake ina saqar zuci ai gwanda nayi keeping kaina busy ko nasamu sarari a zuciyata, nashiga gidan tareda sallamah ta, mamar saudat ce ta kar6a a'ah yau su ameerah ne a gidan ai na dauka ko ba kya gari ne, murmushi na saki na sunkuyar da kai a qasa, a'ah mama wlh inanan, mutuniyar fa tacemin tana daki, hakan yasa na wuce da saurina na fada dakin, na tarar da ita tana linke kaya, kallona tayi ta watsar, na 6ata fuska haba qawas nasan banida kirki amma amin afuwa please.
Tayi murmushi ai kedince wlh sai a slow bakidamu da wanda ya damu dake ba, sai faman zuwa nike gidanku amma ke shiru ba kya leqoni, haba mutuniyar bansanki da yawan fushi ba ki yafewa qawarki mana, kinsanfa banida watche tafiki, muka tafe muna dariya. Nafara tayata linke kayan ta kalleni, amma qawas meh ke damunki u are looking so pale, kuma duk kin rame, nace kedai bari qawas wlh soyayyah ce ke dawainiya dani.
Chapter 1 · 0% Book details