← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 40 OF 52

Sashe 40

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Abunda na lakanta shine da safe sanda yake fita aiki, zanyi shigata cikin karamar riga da mini skirt, nashiga game field ina en tsalle-tsalle na wanda dole ne duk wanda yafito daga cikin gida zaifita dolene ya ganka, tin baya kulani har takai idan ya fito waje sai ya kir-kiri tsayawa yana wani goge-gogen mota da kakkabe kakkabe wanda baisaba haka, bini-bini ina satar kallonsa sai naga ni yake kallo, sai na cigaba da abunda nake, idan yaji alamun fitowar salma sai ya shiga mota ya wuce, dan dama ita yana fita itama zata fice.

Yauma kamar kullum nasa rigana irin wannan da ake daurewa a daidai cibi, da wando 3 quarter, nafito ina buga basket ball da nagani a wurin, khaleed na fitowa yafara abunda ya saba, zuwa nayi na riko hannunsa, da mamaki yake mall on a, kannemasa ido nayi, nace the game is boring without a partner, can you play wit me please? Gyada mun kai kawai yayi, yana kallona nace kadaina kallona fa nima nan na iya games ninayi har game captain nayi a skul, yace oh really gashi kinsamu wani game captain din, nace oya let start and see the best player, mun fara buga game khaleed sai cheating yake yana saka ball da yake yafini tsayi kuma yafini karfi janyeni kawai yake ya saka ball, gefe na koma ina fushin shagwaba yazo yanamin dariya, nace Allah you are a cheater ni bazan yarda ba, janyoni yayi oya lets start a fair game yanzu bazanyi cheating ba i promised ya rike kunnensa alamun sorry.

Game muka koma muka cigaba dayi munata kyalkyala dariya wannan karon nima na nunamai kwarewata dan nasa ball da yawa har yafarayimin tafi, ball din ya karbe ya daga sama na dinga tsalle inason na kamo yaki bari, zare ido na dingayi kamar naga wani abu a gabana, juyawa yayi da hanzari danganin meh nake zarewa ido, yana juyawa na karbe kwallon na sheka da gudu ina cemasa looser, biyoni yayi muka dinga gudu a compound muna dariya, hayaniyarmu tasa salmah ta fito, mune da gudu har cikin garden sai a garden din ya rikoni ta baya, muka zube akan grass carpet muna dariya, muna maida numfashi, zamewa nayi daga kan jikinsa na koma saide dinsa but still hannunmu a rike, kallon juna muka dingayi ba ko kyaftawa kamar masu son su karanto wani abu a idon junansu.

Tabi mukaji anayi a bayanmu shi ya dawo damu daga duniyar da muka tafi, salmah ce taci uwar kwalliya, cewa tayi bravo romeo and juliet zance ko laila majnun? Wannan scene yayi kyau fa, oh sai ta ciro wayarta ta dinga daukarmu hotuna a yanda muke, khaleed ya taso a fusace miye haka? Kuma ina zakije kikasha kwalliya haka? Salmah tace meh ya dameka tinda kasamu mai debe maka kewa? Matatace ko kinada matsala da wannan? Har yaushe kika fara kula da al'amarina da har zaki nuna kishinki? Bakyason nasamu mai debemini kewa kike ko inkula da al'amurrana? Kuma nace ina zakije?

Nidai da aka bari a zaune haushi kamar ya kasheni, ji nake kamar na shake salmah ta batamin show, tasowa nayi nace malamai ku bani hanya ni zanwuce, jayemin khaleed yayi na wuce ina takuna mai daukar hankali.

Daga khaleed har matar tasa bin ameerah sukayi da ido har ta shige part dinta sannan suka waiwayo junansu, ga dukkanin alamu sunma manta abunda suke fada, khaleed hararar salmah kawai yayi yaja tsaki ya tafi yaja motarsa.
[12/16, 7:35 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣6⃣0⃣ Ameerah ta koma daki ta kwanta haushi duk ya isheta, wannan salmar nidai ta isheni Allah oh God just helo me get rid of her na daga hannuna sama alamun addu'a.

Ita kuma salmah dawowa tayi part dinta fitar ma ta kasa, sai safa da marwa take a tsakiyar parlour sai tayi kaman taje dakin ameerah sai kuma ta fasa ta dawo ta zauna. Chan kuma dai sai ta mike tsaye ta nufi sashen ameerah.

Niko bayan nagaji da kwanciya, tashi nayi dan in watsa ruwa game dinda mukayi da gudu, duk yasa na gaji, toilet na shiga na watso ruwa nafito daure da towel, nazo ina goge jikina, na duka na goge kafafuna naji ana shafamin baya, take zuciyata tafara harbawa da sauri, a raina ina chewa yau na shiga 3 na tsokanowa kaina rigima, wato khaleed biyoni yayi, daurewa nayi na mike tsaye amma idona a rufe jikina har ya fara bari, sakaloni naji anyi ta bayana yasa na bude idona, ta madubi na hangota tana wani shu'umin murmushi, a razane na waigo da karfi dan inkara tabbatar da abunda idona ya gani a madubi, tabbas salmah ce toh meh takeyi a dakina? Meyasa kuma tazo tana shafani?

Cikin tsawa nace malama meh ya kawoki dakina? Wani murmushi tayi, i never knew u ar so hot, ido na zaro nace what are you saying? Matsowa tayi ta tabani naja baya, kinga wallahi Allah karki tabani, murmushi tayi just relax deal nazo muyi dake, nasan kinason khaleed sosai amna kuma ni yakeso, ni kuma kinga kwata-kwata ba shine a gabana ba, cikin mamaki nake kallonta, idan kin amince akwai abunda nikeso kiyimin, ni kuma nayimiki alkawari zan barmiki khaleed, ni dakaina zanja ra'ayinshi a kanki, bakina na rawa nace meh kikeso? Wani shu'umin murmushi ta karayi ta lumshe idonta, it simple ta lakacemin hanci ke kawai nakeso, cikin rashin fahimta na kalleta, muryata a sarke nace mata ni kuma? Meh kike nufi da ni kikeso?

Dariya tayi kinga tin zuwana a gidannan, banta6a tsayawa na karemiki kallo ba sai a yau, you are just my type sonki ya kamani kai tsaye, kuma naji ina sha'awarki ki amince dani kawai, matsalarki zata kare, idan kudi kike bukata zanbaki, kuma zaki samu mijinki.

Har wani gumi ya karyomin inajin labari mace na neman mace amma ban yarda ba sai ayau, kokarin hada bakinta tayi da nawa ba shiri na tureta da karfi you animal just get d hell out of my room i'm nothing like you, dariya tayi kinga just relax duk abunda salmah keso zata samu, na shigo gidannan dan na fitar dake amma kuma I'm glad bukatata bata biya ba dan da na tafka asara, zan baki lokaci kiyi tinani akan abinda na gayamiki, amincewarki da bukatata shine zaman lafiyarki, amma idan kikaki wlh zakiyi da nasani dan bazan taba bari ki zauna lafiya ba, ta juya tw fita jikina na rawa naje na sawa kofata key nadawo na zauna jikina sai bari yake, dan a gaskiya na tsorata toh waini ya zanyi?
[9/15, 2:42 PM] ‪+234 706 332 8523‬: 12/17, 8:27 AM] Deejah Abdul: Dream girl na deejah abdul
1⃣6⃣1⃣ Inanan zaune wuri daya duk na takure kaina a daki da naji motsi sai na firgita, hawaye sai zuba sukemin, kiran sallah naji shiyasa na tashi naje sallah, na dauko qur'an ina karantawa, har akayi la'asar shima na tashi nayi sallah sai zabga addu'oi nake, ranar dai a daki na wuni ban ko leko waje ba, ga uwar yunwa inaji amma tsoro ya hana, bayan nayi sallar magrib naji ana bugamin kofa, muryar salmah naji da ita da kawayenta, take duk jikina ya fara rawa, wannan wacce irin masifa ce, sai cewa suke na bude kofa amma ina, sai chan naji wata tace kuzo mutafi jarababbu ku kyale er mutane, salmah tace ke nifa tinda nace muku tayimin ba hakura zanyi ba, ko yau ko gobe ne sai na biya bukatata, tinda nake a rayiwata ba macen da ta tafi da imani na kai tsaye har na rasa sukuni kamar wannan yarinyar, muryar da tayi magana dazu na karaji, atleast have some class kishiyarki ce fa, wlh dai kin bada mata kirasa watche zaki nema sai kishiya? Yanzu idan ta gayawa khaleed dinfa? Salmah dariya tayi ke aganinki zai yadda ne?

Ki duba kigani koda akayi aurenmu mahaifoyarsa bataso, haka ma kanmensa da best friends dinsa, ba wanda ya halarci event ko daya na aurenmu, mahaifinsa ne kawai yaje daurin aure amma hakan baisa ya fasa aurena ba, kuma duk zaman da muke dashi for months duk garashi da nake baisa ya hakura dani ba, kuma nasan rashin kulawar da nike mishi yasa yafara kulata, amma ku yarda dani haryanzu su ba ma'aurata bane dan ba abunda ya shiga tsakaninsu, so kunga taje ma ta fada zata bata lokacin ta ne kawai, suka sheke da dariya, buga kofar ta karayi nasan kina ciki kuma kina jinmu kizo ki bude kofar nan, tinda ina sonki bazan cutar dake ba, wata shedaniyar murya naji, common baby ameerah mufa mata ne en uwanki baikamata kiji tsoron mu ba, nidai nakoma karshen gado na takure ina kuka mara sauti, wayata naji tana ringing amma tsoro ya hanani motsawa, sai chan naji shiru andaina buga kofar na sauke ajiyar zuciya.

Khaleed kuwa yau a farinciki ya wuni, tunanin game dinda sukayi da ameerah kawai yake through out d day yana murmushi, aikin da ya tara office for months baiyi ba yau shi yake tayi, sallah kawai ke tadashi, idan yaji yunwa kuwa snacks ne abincinshi, bashi ya gama aiki ba sai 9.00 pm, sannan ya kamo hanyar gida.

Ko da ya shigo part din ameerah ya nufa, kawai ji yayi yanason ganinta, ko da yake ya tura kofar yaji gam, har zai wuce yaji kamar sautin kuka a ciki, ya dawo ya fara buga kofa, ameerah ta daka tsalle ta mike tsaye ta koma karshen gado, magiya ta fara dan Allah kuyi hakuri ku kyaleni wallahi Allah bazan iya ba, ni zanbarmuku gidan gabadaya ma, wlh Allah zan kyale miki mijinki kiyi hakuri ki kyaleni, khaleed cikin rashin fahimta ya fara magana ameerah zo ki bude kofar nan, kunnenta ya jiyo mata kamar muryar khaleed amma gani take yaudararta suke, sai kara takurewa take a bango tana magiya.

Cikin tashin hankali khaleed yayi part dinsa da gudu ya nemo spare keys, dariya yaji a falon salmah, itada kawayenta, take yayi recalling abunda yaji ameerah na fada, suyi hakuri zatabar gidan zata bar mata mijinta, does dat mean su suka tsoratata akan sai tabar gidan?
Chapter 40 · 0% Book details