← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 21 OF 52

Sashe 21

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 4 min read

Khaleed yace ok u win, ya rufe toilet din ya fara wanka, kafin ya fito saeed ya fito masa da kayansa da ya dinka masa dan kawai daurin aurensa, yana fitowa ya goge jikinsa kawai saeed ya miqamasa kayan yafara sakawa, saida yasa saeed ya miqo masa babban riga da tasha aikin kamar sarkin musulmi, khaleed yace ar u mad? Ni ango ne da zansa wannan kayan? Saeed yace masa ai theme din daurin auren ne haka, nima bakaga ita nasaka ba, khaleed yace but naka is more simpler dan mine, ni ae za'a dauka nine angon, saeed yace ba wani duk salon kar kajene, ai ango ma kalar kayansa daban mune zamusa farare, kuma ma ai kowa yasan kai babban mutum ne, khaleed ya ta6e baki, ya zura rigar saeed ya dora masa hula, sanna ya fidda kwalbar turare ya fara yimasa feshi, take ko ina ya biye da qamshi, khaleed saida ya kar6e kwalbar turaren yayi wurgi da ita, wannan ae haukace wlh Allah zance nafasa, saeed yace Allah ya baka haquri nafiso ne, da munfasa taro asan munshigo, khaleed ya hararesa to takara zamuje e yaja tsaki ya fito, saeed yace Allah aboki banta6a sanin kai maikyau bane sai yau, naji dai anata fada amma sai yau na yarda, fararen takalmi ya ajemasa ya saka, khaleed sai qyalli yake komai fari, kamar wani sarki mota ya shiga ya kame, kaxo mutafi b4 i change my mind, saeed yace sorry your excellency a farar sabuwar motar chan ta dady zamu, khaleed yace frnd motar dad fa kace, makulli ya nunamasa don't u worry, dady ya bamu aro, tsaki yayi ya fito motar saeed suka nufi motar dady suka shiga, sai qyalli suke kamar taurari dan shima saeed ba bayaba wurin kyau, saeed yaja mota suka nufi wurin daurin aure.
[9/14, 1:59 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/24, 8:02 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
8⃣0⃣ Wurin daurin auren kai tsaye saeed ya nufa, da yake wani qaton wuri ne da yake bayan gidan kawu sheshu, ya kama dan kawai daurin auren dan yanada yaqinin daurin auren zai tara manyan mutane dan yasan dadyn khaleed babban mutum ne a jahar, wurin saeed ya nufa kaitsaye khaleed kuwa baisan wurin ba dan haka, baiyi zargin komai aransa ba, koda suka isa wurin dubunnan mutane sun taru, ciki kuwa harda gwamna jahar, da tawagar sarkin musulmi, jan hannunsa saeed yayi suka kutsa taron, maroqa sai biyarsu suke suna musu kirari, duk wanda ya hangosu sai tasowa suke suna miqawa khaleed hannu, anamasa congratulations, khaleed yaga tarin abokanansa a wurin sai tsiya sukemasa, shidai kansa duk ya qulle, wai meh yake shirin faruwane, saeed ya nufa da yashige taro yana musu godiya anata dariya, da niyyar ya jawoshi, yamishi bayanin abunda ke faruwa, hannunsa yaji anjawo, dad ya gani, kafin yagama mamaki, dad yaja hannunsa, son ina kajeni kanaso kasa a makara, tindazu liman ku kadai yake jira, afara daurin aure, jansa yayi sai wani qayataccen daki inda taron manyan mutane yake, duqawa khaleed yayi yafara gaidasu, suna tayashi murna tareda sa masu albarka, kafin khaleed ya ankara sai ji yayi ana tambayar waliyin ango da amarya, gwamnan jaha ne ya wakilci waliyin ango, shi kuma kawu na amarya, su kawu sai. Washe haqora ake yau shine a layin manyan mutane haka lallai haqarsa takusa cimma ruwa.

Khaleed dai yaje dogon tunani shifa baigane abunda ke faruwa ba, meh dad da kawu keyi a wurin daurin auren abokin saeed? Ko dama diyar kawu ce zai aura shikuma shi ya gaygato dady? Khaleed bai ankara ba sai ji yayi ana sanarwa a loud speaker, ALHAMDULILLAHI ANDAURA AUREN KHALID DA KHADIJA AKAN SADAKI NERA DUBU DARI. Khaleed ya qara maimaitawa khaleed da khadijah kuma? Wai shin meh yake shirin faruwa idan nine khaleed toh waye kuma khadijah? Na shiga 3 wace khadijar dady ya auramin? Khaleed bai ankara ba akafara bashi hannu anamasa congratulations, shidai duk ya sandare saeed yake ta wara ido ya gani dan shikadai zaimasa bayanin abunda ya faru, bai ankara ba sai hasken camera ya fara gani daga ko'ina daukar hotunansa ake, jama'a sai tsayawa suke, ana daukar photo, chan ya hango saeed a cikin taro, cikin sauri ya wuce kamar mai son ya tashi sama, jama'a kuwa sai biyarsa suke, hannun saeed ya riqo, ya riqeshi gam danma kar ya kufcemasa, abokansa suka matso ango kasha qamshi tindazu muke nemanka, sai tsayawa suke tare dasu ana daukar hotuna, murmishin yaqe kawai yake musu, jan saeed yayi da qarfi sukayi gefe, chakumarsa yayi saeed kagayamin da wacce khadijar aka dauramin aure, saeed ya janye hannunsa daga chakumar da yamasa, just calm down my man, cikin tsawa khaleed yace how can i calm down, just explain dis, saeed ya lura zai tara musu jama'a dan duk wanda yake kusa dasu saida ya waigo
Chapter 21 · 0% Book details