← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 52

Sashe 11

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 10 min read

Mum ce zaune tana yiwa kausar fada meyasa taqi tsayawa taba maman ameerah haquri da taga tayi fushi, da badan dare yayi ba da sunje, tace mum bari inbaki number ta sai ki kira na dauka a dazu, mum tace yauwa bani, sukayita kira amma basu samu ba, kausar tace mum kabari muje gobe kawai, tace toh shikenan dama inason inyi magana da mamanta da banason auren ya dauki lokaci atleast nan da wata daya coz nima na matsu naga jikokina.

Khaleed ne yashigo da sallamah, mum ta kar6a da fara'a dan halak yanzu muke, zancen aurenka nan da wata daya muka saka yayi maka? Karka damu da abunda dadynka yace, indai ina raye ba wata husnah da za'a aura maka, khaleed cewa yayi mum ni nama fasa auren na haqura, zanyi rayuwata alone har sanda dady ya yarda da zabina, dady ne ya sauko kar kasake kace ni na hanaka aure, kaje ka auri er talakawanka ba ruwana, saidai ko ficika kar wanda ya tambiyeni ya ficewarsa.
Mum tace kaji ma ya amince so don't u worry nasan ma ko abunda yace yanzu dan baigama sauka bane amma zai haqura later. Khaleed yace mum nifa na haqura da auren kiyi haquri kawai ya juya zai wucewarsa, mum tace shikenan son tinda bakaso kaga ina farinciki kaje kayi yanda kaga dama, kabari baqincikinku kaida dadynka ya kasheni, tunda ku taurin kai ne daku kamar diyan shaitan, ta zauna tana share hawaye, kausar tace wlh Allah big bro bakada kirki kasa mum kuka, kuma sai Allah ya sakawa sis ameerah nida namiji ce wlh ni zan aureta na share mata hawaye.
A razane khaleed ya juyo, yazo da sauri ya duqe gun mum ya riqe qafafunta mom dan Allah ki yafemin bansan ranki zai 6aci ba wlh na amince ko gobe kikeso a daura aure, dagaoshi tayi to ya isa son na haqura kar ka sake ka qaramin zancen zaka fasa aure, bakasan yanda nake burin naga aurenka ba, kuma yarinyar nan tashiga raina Allah, ina maka sha'awanta dan nasan zakaji dadin zama da ita, yace shikenan mum bazan qara ba, ya miqe zaifita tace gobe ka shirya ka kaini gidansu ameerar, gabansa ne ya fadi amma ya daure yace shikenan mum Allah ya kaimu
[9/14, 1:06 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/17, 11:54 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
4⃣9⃣ khaleed bayan ya koma daki yayi trying wayan saeed yajita a kashe, dama yasan a rina, waya ya dauka bari ya kira salmah ko zaiji sanyi a ransa, kiran wayar yake tana ringing amma ba'a dauka, ya tura mata txt just call me bak my baby i really missed u, nagaji da rashinki ina buqatarki a kusa dani, yayi ta jiran call shiru har bacci yayi gaba dashi.
A wurin ameerah kuwa bayan ta kwashe kayan da mama ta watso mata ta maida a leda, sai tayi deciding bari taje ta nemo extension wire tayi chargen phones din, tasan zuwa da safe idan su khaleed sukazo suka gaida ita zata yarda tayi accepting kayan, fita tayi taje dakin mama tace mama.......... Mama tace idan haquri kikazo bani karma kifara, kibari kawai zuwa gobe ki tattara kayansu ki maidamusu, ni ba shashasha bace da zanyarda da zancenki, kuma khaleed dinma banta6a jin zancensa ba sai yau, so ni bazan dauki wannan shashanci ba, wato kinga ni banida kudin da zan siyamiki abunda kikeso ba shiyasa kika za6i wannan hanyar? Toh bazan lamunta ba inada rai ba wanda ya isa ya lalatamin tarbiyar da na dade ina ginawa. Kuka na fara haba mama ni kice komai amma dan Allah karkiyi zargina, bazanta6a zubar da tarbiyar da kukamin ba akan wani abun duniya, laifinane da naqi sanar dake zancen khaleed da wuri, amma wlh mama just blif me dagaske yake da aure yake nemana.
Toh idan har dagaske yake meh yasa baizo ya gaida iyayenki ba? Nace mama zaizo gobe inshaAllah, tace toh shikenan inanan ina jiransa inji da watchche yazo. Nace mama dama kaina ne yake ciwo nikeso inje chemist din chan in siyo paracetamol, tace ba inda zaki kibari a kira aliyu a waje ya siyomiki, nace mama wato baki yarda dani ba? Toh shikenan muje tareda fatima ko suhaila, tace nace ba inda zaki, khairi je waje kace aliyu yazo ana nemansa, khairi ya fita da gudu, nace toh mama ina a daki idan aliyun yazo, tace idanma wani abu kike qullawa tun wuri ki daina, tashi nayi na wuce dakina.
Aliyu ne ya shigo da sallamah, sis ance kina nemana nace, kar6i extension waya zaka siyomin a waje, yace wai sister shikenan nayi asarar galaxy din kenan? Nace no bro gobe zaka kar6i wayarka inshaAllah, cewa yayi toh sis wai waye wannan khaleed guy din? Nace your brother inlaw to be, yace bangane ba kin haqura da wanchan guy din kenan, gaskia i'm happy 4u, nace bro bafa haqura nayi dashi ba shine dai kawai, zaunawa aliyu yayi, toh ya akayi kika sameshi da sauqi haka? Nace aliyu abun sirri ne, lets just say Allah ne ya kar6i addu'armu, nidai tashi kaje kar mama ta zaci wani plan muke shiryawa, sannan ya tashi ya fita, ko da aliyu ya dawo mama tareshi tayi, tace sai taga abunda ya siyo dole ya bata, zuwa tayi a dakina, wato ke nace ki tattara kayan mutane kinqi ko? Shine harda siyo abun saka chargi wa zakiyiwa wayo? Toh kinyi asararshi kuwa a gabana ta dagashi sama ta watse ta tafiyarta, wani haushi ne ya turnuqeni nasa kuka a haka har bacci yayi gaba dani.
[11/18, 7:02 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
5⃣0⃣ Nice ban farka ba saida naji ana kiran assalatu na tashi na doro alwala, nayi nafila kan a tada sallah, naje na bubbugawa su mama, da aliyu suka tashi, bayan na gama sallar asuba na dauko azkar dina nayi, bayan nagama na buda qur'ani na na rinqa rera karatu har gari ya waye, fitowa nayi na tattara kayan wanke-wanke, da yake weekend ne na lura duk sunkoma bacci, bayan nagama wanke-wanke naje, na gyara dakina tas na share na chanja bed sheet harda saka turaren wuta, na share tsakar gida, na hasa wuta na dora ruwan zafi da yake hunturu ne anfara sanyi, zuwa nayi ina tada su suhaila su tashi, na gyara daki, mama tace karna tada mata yara yau weekend nabarsu su Huta, nace mama islamiyyarfa takwas tayi fa, sannan ta miqe ta tashe su, ruwan zafin da na dora nace su diba suyi wanka, sannan na dora dumame, nakoma gyaran dakin mama, shima na gama na chanja bedsheet na kunna tirare, itadai mama ta samin ido kawai tana kallon ikon Allah. Bayan su suhaila sungama shirin islamiyya ne sukaci dumame suka wuce skul, sake share inda suka 6ata nayi, yau nice harda mopping ledar dakin mama da nawa abunda na dade banyi ba, gamawa nayi na dibi ruwa na fada wanka, ko da nafitoh goma tayi shiryawa nayi na saka kayana cikin wanda muka siyo da saeed, nayi kyauna ba laifi dukda ba wata kwalliya nayi ba, dumame naci, sannan nace mama.......... Tace indai wurin maida kayan zaki ni ban yarda kije ke kadai ba, kibari idan su suhaila sun dawo kwa tafi tare, kuma kije ki cire kayannan na jikinki dan har su zaki maida.
Daki na koma ina share qwalla nidai wlh mama ta dauki abunnan da tsauri, zuwa nayi dole na ciresu, lesi na na sallah na dauko wani fari da zanen flowers purple, na saka hijabina purple na fito, kallona tayi sama da qasa, wai wa kikeyiwa wannan qyalqyalin? harda wani sabon gyaran gida toh wlh ki kiyayeni, ba inda zaki na gayamiki, nace mama gidansu saudah zani fa, tace ae saudah ta gayamin rabonki da gidansu tin sanda aka kawo lefe, toh fitar da kike da yamma ina kike zuwa?
Sallamar da akayi ta katse mama da tambayoyin da take shirin zubomin, nidai na lura da mama kwata-kwata yanzu bata yarda dani ba, amma kuma banga laifinta ba zamani ne ya lallace, samarin yanzu basa kashewa budurwa kudi a banza, batareda wata buqata tasu ba, hakan yasa en mata da yawa suke lalacewa akan kwadayin abun duniya.
Rungumenin da akayi yasa na dawo daga tunanin da nike, kausar na gani a gabana suprise tacemin, dan duqawa nayi na gaida mum da suke tare, ta dagoni tana murmushi muka rungume juna, mama turus tayi tana kallon ikon Allah, nace mama wannan itace mum maman khaleed, wannan kuma kausar ce kinganta jiya, mama ta saki fuska a'ah barkarku da zuwa, kuwuce ciki mana, tajasu suka wuce daki, dakin aliyu na nufa da sauri, na bashi dan sauran chanjin da suka ragemin, kayi sauri ka kar6omin exotic guda biyu a shagon Abu, da robar ruwa guda 3 karka dade, idan kadawo ka dorosu a tire, ka dauko sabbin cups dinnan na glass da mama ta siyomin suna dakina ka dora akai, ka kawomin a dakin mama, yace sis ba cups din kayan aurenki bane? nace ina ruwanka nidai kayi sauri, sannan ya tafi nikuma na koma daki.
[9/14, 1:08 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/18, 7:28 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
5⃣1⃣ koda nashiga sunata gaisawa kamar dama sun san juna, sallamata ta katsesu, mum tace 'yata zo nan kusa dani, naje dab da ita na zauna, tace ' yata tun jiya nike kiran number ki bata shiga, ko baki saka layin bane? Mama na kalla ta watsomin harara, tashi nayi na dauko wayoyin da kayan da mum taba mama na ajiye gaban mum, nace mama ce bata yarda nayi amfani da waya ba tace may b sai zuwa gaba, mom tace toh naji idan wayoyin ta hanaku amfani dashi, nata wayar fa? Sannan wannan kayan fa? Shiru nayi, mum tace maman ameerah kiyi haquri nice da laifi jiya ni na riqe ameerah a wurina har yamma tayi, kuma wayar nan ba roqa tayi ba, ni naga ya dace a siyota dan faruwan irin haka, dan da tanada waya jiya ko ke kinada da ta kira nayi magana dake, da baku tashi hankalinku ba duk da ameerah bataso ba nina matsa akan sai ta za6i wayoyin, kuma wannan kayan nice na bata ta kawo miki, bada wata manufa nayi ba, naga kamar anzama dayane tinda zamu hada zuri'a.
Mama ta sauke ajiyar zuciya toh dama ni ba qi nayi ba, kinsan halin yaran zamani ka haifesu ne baka haifi halinsu ba, shiyasa gwanda na tabbata inda kayan suka fito da kuma dalilin bayar dasu kan na yarda ta fara amfani da su, amma yanzu ai komai ya wuce na gamsu, ameerah ki kwashe kayan, dariya mukayi duka, a raina nace alhamdulillah, mum tace amma nayi farinciki kuma na qara natsuwa da zabin da dana yayi, na tabbatar ameerah halinki ta dakko bata watsar da tarbiyar da kika mata ba kuma na tabbatar khaleed yayi dacen mace ta gari da suruka ta gari. Aliyu ne ya shigo da sallamah dauke da lemo da ruwa kamar yanda nace yayi ya ajiye musu, gaisawa sukayi nace mum wannan shine aliyu, tace lallai aliyu anzama samari, tace a ina kake karatu ali? Yace na kammala secondry last yr amma banci gaba ba dan bansamu jamb ba, mum tace aliyu kanada ra'ayin karatu a egypt? Cikin fara'a aliyu yace idan nasamu meh zai hana? Tace toh karka damu daukar nan da za'ayi inshaAllah dakai a ciki zaka samu scholarship, akwai dana da yake karatu a chan sai ku riqa zuwa tare dama zaizo hutu ranar friday, sai ku koma tare yanzu ka hadomin takardunka na tafi dasu, godiya aliyu yayi muma muka tayashi, mama kuwa mamaki ne ya kwashe ta tana ganin kamar a mafarki.
[11/18, 1:46 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
5⃣2⃣ lemo na zubawa mom da kausar a cups na basu, suka kar6a, mum tace ameerah ki dauki lemo da ruwa ki kaiwa khaleed yana a waje, cikin kunya na tashi na dauki kwalin lemo daya da ruwa, daki naje na dauko qaramin tray cikin kayana na hada da cup nayi hanyar fita, tsalle naji kamar anayi a dakin aliyu na leqa, aliyu na samu yanata rawar skelewu, dariya na saka saida nakai kwance, Aliyu yace barni nayi rawa tun bayan rasuwar baba bansake samun good news kamar na yau ba, nace toh ka hada takardun ko kuwa? Yace yanzu zanhada nace shine oya kayi da sauri, na dauki lemo na fito waje.
Chapter 11 · 0% Book details