← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 19 OF 52

Sashe 19

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Kausar ce ta matso amma mom bazamu qyale husnah ba dole muyi maganinta, mom tace sosai kuwa alhj ko bakayi wani abun ba ni wlh bazan qyaleta ba, doctor ne yazo yace patient dinku ta samu isashshen jini, kuma she is stable now, saidai kuma sanadiyar buguwar da kanta yayi tayi dogon suma, she is in comma right now, amma muna tunanin is temporary ko da nan da 3 days ne zata farfado, yanzu zamuyi shifting dinta zuwa ICU, u can all see her there, hamdala kowa yayi tareda ajiyar zuciya, da fatar Allah ya ba ameerah lfy.
Saleem ne ya kira kausar yana airport azo a tafi dashi, shine kausar ta gayawa mom, mum tace shi saleem bai tashi dawowa ba sai yanzu, tun kwana baya muke especting dawowarsa, sai yanzu ana crises zai dawo? Alhj yace ai kuma yariga ya dawo, ina kausar tazo suje da khaleed su daukoshi airport din, amma aka nemi khaleed aka rasa.
[9/14, 1:50 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/22, 8:41 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
7⃣4⃣ khaleed kuwa yana fita daga asibitin police station ya wuce, dama comissioner of police abokin dad dinsa ne, yau sai ya koyawa husnah hankali, bazata qara gigin qoqarin kashe ko waye ba a duniya, koma waye ubanta a qasarnan sai ya daureta.
Kiran saeed ya shigo wayarsa, buddy where are u? Yace ina asibiti kai kana ina? Yace ina police station yanzu gidan deputy governor zai wuce, he'll teach dat stupid girl a lesson, mota saeed ya shiga da sauri, mom, dad da kausar suka bishi, ya kama hanyar gidan deputy governor yasan halin abokinsa idan yayi fushi ba sauqi, khaleed kuwa da yayiwa comissioner bayani motar en sanda 3 aka hadashi dasu direct sai gidan deputy governor.
Deputy na zaune da matarsa suna shaqatawa yafara ganin police na diro masa gida kamar daga sama, cikin tashin hankali ya tashi, ya daka musu tsawa wannan wanne irin rashin hankali ne, zasu fado masa gida kamar police head quater, khaleed ya shigo yace alhj kafito da husnah batareda 6ata lokaci ba dan she must pay 4 her crime, deputy cikin rashin fahimta yake tambayar what crime, meh 'yata tayi? Inspector yace ana zarginta da qoqarin kisa, ta kade matar da khaleed zai aura da mota dazu, kuma ta gudu wanda ya tabbatar da cewa tayishi ne da gan-gan, haj ra miqe dis is rubbish, husnah bata qasar nan tin jiya taje america ta ya zata kashe mutum yau? Inspector ya bada umarni afara searching gidan lungu da saqo kar abar ko ina.
Bayan sun duba ko'ina sun tabbatar bata gidan, khaleed ne yaje ya chakumi wuyan deputy governor ya shaqeshi, wlh duk inda husnah take ka fito da ita kafin kaima na qarasaka, daidai nan su saeed suka shigo, tsawa dad ya sakawa khaleed akan ya saki deputy governor, amma ina daqyar saeed da wasu police suka qwaceshi, idon nan sunyi turu-turu sunyi ja, cewa yake alhj khalipha ka fitarmin da mahaukacin yaronka a gida, nagodewa Allah da 'yata bata auri mahaukaci ba.
Daidai nan wayar matar deputy governor tayi ringing, cewa tayi ga ma husnah din nan ta kira dan ta lura number america ce, Inspector yace tasa wayar a hands free, ta daga muryar husnah ce kuwa, haj tace husnah ki fadamin gaskia, ke kikayi qoqarin kashe matar da khaleed zai aura? Husnah tace common mom ai kinsan ni idan bansamu abu ba ba wanda zai samu, kawai na nunamuku na haqura ne dan kawai ku dena damuna, but d truth is haryanzu ina son khaleed, dad yace amma husnah jiya kikabar qasar nan, taya akayi hakan ta faru? Dariya tayi dad kai kamar ba dan 9ja ba? Ae visa ta yau ne da yamma i just landed, kawai na cemuku jiya ne karku 6atamin plan, mom just tel me wannan ameerah din ta mutu nafara celebration ta fashe da dariya, mom tace amma Allah ya tsinemiki albarka husnah, deputy governor yace daina tsinema 'yata, ga tsinannen yaron da zaki tsinewa nan duk laifinsa ne, now i lost my daughter, haj zubewa tayi qasa tans kuka gwanin tausayi, Allah ya isa tsakanina dakai alhj duk kai ka lalatamin ' ya ka nunamata, duk abunda takeso zata samu shiyasa batasan tayi tawakkali ba, gashi ka juyen mahaifa bare na qara haihuwa, ni wlh alhj ka cuceni, mom ce ta tasheta tafara bata haquri.
Deputy governor tsawa ya saka a fice masa daga gida, Inspector yace your excellency inaso kasa a ranka ko yaushe 'yarka ta dawo qasar nan sai mun hukuntata sannan suka fice.

A mota kuwa kowa shiru yana jimami, dad ke nasawa a zuciyarsa yaso ya tafka babban kuskure a rayuwarsa amma ya gode Allah da ya ganar dashi da wuri, kudi ba su ke sa yaro ya samu kyakkyawar tarbiya ba, dan ga husnah duk gatanta da kudin mahaufinta takasa samun tarbiyya, shi ya godewa Allah nashi yaran Allah ya shurya su amma dan sunyi dacen uwa ta gari ne, shima daga yau bazai qara shiga rayuwar yaransa fa zaimusu fatan samun abokan rayuwa na gari, ga alama kuwa khaleed yayi dace dan yarinyar ya lura tanada kamun kai da nutsuwa, tsanar da yayiwa talaka yasa yaqi yarda da hakan, amma not anymore da haka suka isa gida kowa yayi side dinsa.
[11/23, 12:02 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
7⃣5⃣ da safe dad ya samu mom tana shirye-shiryen zuwa asibiti, yace aisha magana nazo muyi, haj ta zauna, dad yace a ganina dan yarinyar na batada lfy bai kamata a janye daurin auren nan ba, haj mamaki tayi dan batayi tsammanin wannan maganar tafito daga bakinshi ba, amma tayi matuqar farin ciki, hakane alhj a daura auren kawai idan yaso daga baya ayi bikin, tace bari na kira son namasa bayani, dada yace niko na lura yaron nan kamar ba natsuwa a tare da shi, ki kira wannan abokin nasa shi ya shirya komai, mutanen da sukaji labarin accident din ya gayamusu still akwai zancen daura aure, wanda baijiba ma shikenan. Hakan akayi kuwa mom takira saeed ta masa bayani, sannan tace shikenan idan sunje asibiti tayiwa maman ameera bayani ta sanar a gefenta.

Saeed da ya tashi dakin khaleed ya nufa, ya sameshi yayi wani zugum duk ya wani kode yayi rama, saeed ya ta6ashi aboki wai meh ke faruwa ne? Khaleed yace aboki kafi kowa sanin abunda ke faruwa salmah taqi saurare na, yanzu kuma ga abunda ya faru ga ameerah, kuma duk ni naja mata, amma is not too late da Allah ya tashi kafadunta zan warware wannan auren da muka shirya, saeed yace lallai kuwa ni zantafi, zanje asibiti na duba ameerah, khaleed yace ka jirani mutafi a tare yafito suka wuche.

A mota kuwa shiru sukayi kowa da bikin zuciyarsa, saeed na nasawa a ransa ba sai ya gayawa khaleed zancen daurin aure gobe ba, yaji yana qudurin janye auren, idan ya gayawa su mom gaskia, abun bazaiyi dadi ba, gwanda ya barshi kawai, beside ma salmar da yakewa fighting ya lura, ba wani damuwa tayi dashi ba, tun farko da tana sonshi bazatace yayi keeping r. Ship dinsu secret ba, duk da yake iyayenta da na khaleed aminaine, akan wani uzurin karatu, gwanda khaleed ya auri ameerah kawai, dan yana zargin ameerah son khaleed take, da bazata iya yimasa haka ba, duk da yake bai tabbatar da zarginsa ba, amma yana fatar haka ta kasance.
Saeed ya katse shirun yace khaleed meyasa ba'a nemeni ba jiya da aka kawo ameerah asibiti? Duk da kasan ina asibitin, khaleed yace aboki nikaina bansani ba mom da dad kawai suka jani asibiti, daz where i found out everything, beside ma kaida kake likitan mata meh zaka iyayi? Saeed yayi dariya wa ya gayamaka gynocologists basu iya komai ba sai aikin mata? Dariya sukayi da haka suka isa asibitin.
[9/14, 1:54 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/23, 3:24 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
7⃣6⃣ koda suka shiga gun da ameerah take, mamace da aliyu da su suhaila kowa yayi zugum ba mai magana, suka duqa suka gaida mama ta kar6a da dan sakin fuska, sukace ya mai jikin? Mama tace to alhamdulillah za'ace amma bawani chanji har yanzu, saeed yace doctor ya dubata? Mama tace eh yace qalau take kuma anasa ran ta farka a kowanne time.
Mama tace khaleed dafatar ba wannan abun kasa ranka ba naga duk yanda ka yamutse jiya kawai? Shidai ya sadda kai a qasa a ransa kuwa cewa yake dama damuwar da ke damuna akan hatsarin ameerah ne kawai, saeed kuwa sai kallonsa yake, sai yanzu ya qara ganin yanda abokin nasa, yayi rama yayi duhu, girgiza kai kawai yayi, a ransa yace dole na fito dakai daga wannan jarababbiyar soyayya, bari ma na tashi na qarasa rabon katin aure, mama tace saeed ka riqa bawa abokinka baki kar damuwa tamasa illah, daidai nan su mom suka shigo da kayan breakfast, mom tace son ka kwantar da hankalinka ba abunda zai samu ameerah, kacigaba da addu'a kawai ka saki ranka, kada kai kawai yayi suka miqe, saeed yace mom mu zamu tafi, sai munshigo anjima, bandir din kudi khaleed ya ajiye koda ana buqatar wani abun suka fice.
Chapter 19 · 0% Book details