← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 25 OF 52

Sashe 25

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Qarfe daya salmah ta fito hotel dinta zata fita, taje reception ta bincika idan tanada saqo, sai lokacin matar ta tunamata da wanda tace ya jirata, tsaki tayi sannan ta fito ta nufi wurin.
Khaleed ya miqe haka ya tashi ya koma hotel din, ya ganta tsaye gabanshi, wani murmushi ta sakar masa tace babyna m sorry, na zana jarabawa ne, murmushi yayi ya nuna mata wuri ta zauna, aransa yace ko mehyasa batason nasan ta gama karatu sai kuma ya basar, haquri nazo na baki salmah, kinsanj rudani na kasa sukuni, na rasa nutsuwata a kanki, kinqi ki saurari uzurina, katseshi tayi wanne uzurin ai ka riga kayi auren kuma, u break our promise, so ni bazan ta6a iya sharing dinka da wata mace ba, indai abunda ya kawoka kenan u better go, ta miqe zata tafi, sai ga khaleed a qasa ya riqe qafan salmah, ni Deejah haushi kamar na mutu baisan wahalar da nasha kan na biyo shi germany ba, amma abun takaicin da zangani kenan 😢 ba'anan ya tsaya ba khaleed harda kuka salmah ta saurareshi, ni DEEJAH kamar na rufeshi da duka, ga ameerah chan zata mutu ma kansa yazo yana kuka kan wannan mai kama da aljanun, leqawa nayi na qaremata kallo gajera ce fara tas kyakkyawa ce ainun da wasu ido, idan ta budesu sai ka firgita kan girmansu🏃🏼🏃🏼.
Dawowa tayi tazauna jikinta yayi sanyi a raina nace er qwal uba🙊 gwanda ma karki haqura, ta marmada qattan idonta, toh ina jinka, shiko gautan yafara fede mata biri har wutsiya yanda akayi ya auri ameerah, amma shi ko kadan baya sonta, nace zaka sota dan malfar uba🙈 waigowa sukayi na duqe qasan table basu ganni ba, sai cewa tayi toh shikenan naji na haqura i'll get bak 2u soon, ni zantafi miqewa yayi kamar jela ya bita yana mata kalaman soyayyah ni Deejah tsabar haushi kasa rubutawa nayi, motar ta taja ta tafi ya bita da ido kamar maye saida ta 6acemasa.
[9/14, 4:37 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah Abdul
8⃣9⃣ Ajiyar zuciya khaleed yayi, Allah na godema da kasa ameerah ta sauraren, sai a lokacin ya duba tima 20 minutes to 2 cikin hanzari ya tari cab, ya koma hotel dinda ya sauka shiga kawai yayi ya dauki jakarsa ya wuce airport, koda ya isa jirgi kadan ya tashi, anyita qwalla kiran sunansa baya kusa, daqyar ya samu aka barshi ya shiga, suka daga sai india.
🍒🍒🍒INDIA🍇🍇🍇

ameerah da kausar sai around ten suka farka, kausar ta taimaka mata tayi brush sannan ta barta tayi wanka, ta dawo ta kwanta itama kausar ta shiga, koda ta fito nurse ta kawo breakfast dansu asibitin su kebawa patient abunda zasuci amma duk a kudinka, kausar ta taimaka mata tayi breakfast itadai ameerah taste din abincin india yayi mata, taci tasha magani, kausar kuwa snacks dinta ta diba taci da drinks.
Kausar ta lura ameerah tayi wani zugum tace bari na kira su mom, tasa call dinsu take mom ta dauka, tanajin muryar kausar tace hope good news zaki bamu, kausar tace yes mom ta farka tin jiya ma now she is alright, murna suka fara, mom tace toh meh yasa baki gayamana tin jiyan ba? Kausar tace mom bansamu simcard da wuri ba sai cikin dare, nasan kunyi bacci, sis ameerah tace nabari har da safe, mom tace toh kibamu ita mana, ta miqomin wayar, waya mukayitayi dasu, mom, mama, suhaila, fatima, siyama da khairi kowa saida akaba mukayi magana, mom tace su suna airport ma yanzu zasu taso, nace mum ku duka? Tace a'ah itada mama dai su suhaila a gida zasu zauna har adawo, tace ina khaleed? Na daburce nace mata ya fita siyo magani kausar ta dago kai da sauri ta kallonj, nayi mata alama da hannu tayi shiru, daga bisani mukayi sallamah, akan sai sun iso.
Bayan mungama sai ga kiran su salim da aliyu haka mukasha fira suma saida kausar ta kar6e wayan ta kashe, nace ya haka sis? Tace magana zamuyi kafin su mom su iso.

Kallon tuhuma tayimin, meyasa kika hana na fadi gaskia akan yaya khaleed? Nace toh meh zakice? Tinda aka sauka india ya gudu? Kinsan meh yajeyi ne? Ta6e baki tayi, amma koma mene ae baikamata ya kwana achan ba, sister inlaw ki gayamin gaskia tsakani da Allah, wai miye tsakaninki da yaya khaleed? Qirjina ya buga nace mata kamar ya? Ni bangane ba, tace ni Allah na lura banga wani chemistry a tsakaninku ba, kwata-kwata wanda ya zauna tareda ku baxaiga alamun soyayya a tareda ku ba, duk da nasan yayana daban ne, amma ni nasan sanda yayi soyayya da wata er abokin dad ba haka yakeyi ba, take zuciyata ta buga nace mata kinsan salmah ne? Tace farin sani kuwa? Amma ke ya akayi kika santa? Take qwalla ta cikon ido na share, zuwa tayi ta dafani, dama ni nasan da wata a qasa, titsiyeni kausar tayi saida na kwashe komai na gayamata.

Ajiyar zuciya tayi, gaskia kinyi wauta sister inlaw, amma kuma banga laifinki ba so ne yaja miki, kuma da kingayawa broda gaskia bazai kalleki ba, amma yanzu kinada hope kuma ni zan taimaka miki to fulfill your DREAMS, hugging dinta nayi ina kukana inamata godiya ita kuma tana bubbugamin bayana alamun rarrashi.

Sakinta nayi nace mata salmah fa? Tace diyar abokin dady ce, senior ta ce a secondry skul, tin alokacin nasan tana soyayya da broda, har lokacin da ta gama aka turata germany karatu, amma daga time din banqara jin zancenta ba ko a gida broda bai fadi ba, so mundauka ma sun dade da rabuwa, i was suprised ma da kika gayamin har yanzu ita yake so, toh ko meyasa sukaqi fada a gida oho, amma ni sis inaganin Allah shi yasan abunda ya tsara shiyasa haka ta faru, ni yarinyar tuntuni batayimun, tafiye jinkai da yiwa mutane kallon banza, itama bata qaunar talaka ya ra6eta shiyasa bama jituwa tin a skul, kuma mudai yanzu kece choice dinmu, zan tayaki fighting till d end, hugging dinta nayi cikin farinciki, araina nace samu dafa, Allah ya nunamin cikar burina. Kausar tace now dat i think may b bro germany yaje, nayi rau da ido, tace jelous ko sis nayi murmushi tace karki damu, my broda iz not dat bad bazaiwuce limit ba, doctor ne yashigo yana tambayar meh nikeji now nacemasa jst a weakness yace it normal zandaina ji, allura yamin zaifita, nacemasa zanfita nagaji da zama wuri daya, dariya yayi yace lallai sauqi yazo, kausar ta taimakamin muje garden gatachan ya nuna mana, tashi tayi ta kamani muka nufi gun.
[9/14, 4:41 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah Abdul
9⃣0⃣ Garden din muka shiga muka zauna ko'ina luf-luf gwanin sha'awa sai kukan tsuntsaye kakeji, shiru mukayi 4 sometime kausar tace sis amma kinsan ya kamata mom tasani ko? Da sauri na dago na kalleta, nace dan Allah sis karki fada, inajin kunyar mom da wanne idon zan kalleta, idan tasan plan dinda muka shirya, zataga kaman mun renamusu da hankali ne, kinga mom ta yarda dani sosai, kausar tace nima dalilin da yasa nace na gayamata kenan, dan nasan tana sonki sosai kuma ta yarda dake, so zata fahimce dalilin qaryarki kuma m sure mom zata taimakeki. Nidai na girgiza kai sister inlaw just promised me bazaki gayawa mom ba, dis is my battle i need to fight it alone, tinda ni nasaka kaina, a ranta tace zanyi shiru 4 now, amma duk naga abund zai baki wahala dole mom ta shigo ciki dan broda baya tsallake maganarta, a zahiri kuma tacemin shikenan sis bazan fada ba, and remember this is our fight, not yours alone, hugging dinta nayi ina qara godewa Allah ashe dama za'a samu dangin miji haka? Nidai nayi dacen dangin miji, saura mijin shima Allah ya dorani akansa.

Su mom an iso birnin mumbai india, direct mota suka shiga sai FOUR SEASONS HOTEL MUMBAI, suka kama kowa daki, suka sauke kayansu sannan suka nufi adibiti.
Chapter 25 · 0% Book details