← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 46 OF 52

Sashe 46

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Aunty fareedah tace nasan har ranka kakejin kukan ta amma daurewa zakayi ka gasata idan dai kanaso ta samu releif, bakason taji zafi kayi mata abunda yafi ruwan zafi? Gumi ya share ya koma ya dauketa suka koma toilet din, tanaganin zai sakata ruwan ta makaleshi tana kuka zafi Allah zafi, khaleed harda hawaye yace khadijah i'm sorry but i must do this, sakata yayi tayi kara ya kauda kansa ya barta a ciki, sai chan yaji tayi shiru kuma, ya dubota kindaina jin zafin ta gyadamasa kai, ta kwanta a ruwan tace kafita zanyi wanka, yayi murmushi ya fita, aunty fareedah ta miko masa wasu kayan gashi ka bata ta saka, ya koma toilet din ta sa masa kukan shagwaba tareda rufe ido, nidai kafita nace, zuwa yayi ya dibi ruwan ya watsa mata, ni kuma? Miye bangani ba? Dukewa tayi a ruwan nidai kafita, ya mike ok ga kayanki nan, idan kin gama ki kirani ya fita ya nufi wurinsu saeed.
[12/20, 7:53 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣7⃣6⃣ saeed yace ta gama? Khaleed yace a'ah saeed yace toh zauna, ya zauna yace khaleed nasan baka harkar mata amma banyi zaton bakasan komai ba akan abunda ke faruwa a daren farko gun wace mace cikakkiyar budurwa ba, Wannan wahalar da kaga ameerah tasha har ka rikice ko wacce mace indai cikakkiyar budurwa ce dole hakan ya faru da ita, wasu matan ma zaka samu bleeding sukeyi sosai su zubar da jini, amma ba kowace macece take zubar da wannan jinin ba, budurci wata fatace marar karfi da ake samu gun kowace mace budurwa, saidai wannan fatar takan yage ne ba ta hanyar saduwa kadai ba, wasu mata sukan rasa wannan fatar budurcin ba tareda sunsan miye da namiji ba, sukan iya rasata ta hanyar tsalle-tsalle, tsalake-tsallaken rami, hawan itace, hawan gina, hawan keke, daukar abu mai nauyi, da dai makamantansu, wasu matan kuma yawan ciwon mara ko tsananin ciwon mara kansa ayimusu wankin mara ta wannan hanyar zasu rasa budurcinsu, kuma mace ta rika yawan saka hannu ko yatsa a farjinta wannan yakan buda mace, yawan tsarki da ruwan sanyi a wurin mace shima yakan iya budasu, shiyasa ba lallai bane dan ka auri mace a daren farko bakaga ta fitarda jini ba kafara zargin er iskace ya kamata maza susan haka.
Amma wasu matan wannan fatar budurcin zata zauna a jikinsu bata yageba har sai sunyi haihuwan fari, mata kala-kalane saidai duk macen da ta saba biyar maza, bazata taba zama daya da budurwa ba koda kuwa wannan fatar tata ta budurci ta yage, kadda wasu mata suyi amfani da wannan dama su rika yawon iskancinsu ba suyi tinanin mazansu bazasu gane ba.

Salmah kuwa da kake cewa bakaga tayi hakan ba, dukda ba maza takebi ba mata takebi, wannan bazai hana kawar da budurcinta ba, kar mata suyi tinanin wai dan kina lesbianism ba maza kike bi ba, ki dauka kinanan cikakkiyar budurwarki, tsaf mace 'yar uwarki zata iya kawarda budurcinki ta hanyar amfank da hannu ko wasu abubuwan. Allah ya shiryarda masu aikata wannan aikin dan suna tareda fushin ubangijinsu.

Abunda ya faru da ameerah is normal dan cikakkiyar budurwa ka aura saidai sanin a bukace kake bazakayi mata da sauki ba tinda tsohuwar matarka ta garaka, zaka iya jimata ciwo, dan haka kadubo idan ta fito wankan nayimata allura, ga kuma prescription na maganin da zaka siyo, sannan zan dubata idan ta yarda, khaleed yace ta yarda ko na yarda? Ai wallahi baka isa ka dubamin mata ba, zakayimata allura dai amma dubawar saidai muje asibiti doctor feenat ja'afar ta dubata badai kaiba, sukayi dariya yatashi ya shiga dakin.
[9/15, 2:45 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/22, 6:04 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣8⃣0⃣ koda muka shiga hotel room dinmu sauke kayana kawai nayi na watsa ruwa, mukayi sallah nace ni yunwa nakeji, muka sauka kasa mukaje restaurant dinda ke tare da hotel din mukachi abinci, sannan muka shiga yawon gari muka fara siyayyah, bamu muka koma hotel room ba sai dare nashiga toilet na watsa ruwa na fito khaleed ma ya shiga, koda ya fito nasa night gown ya kalleni ya kauda kansa, na kwanta a gado ina jiran naga khaleed shima yazo ya kwanta sai naga ya dauki pillow da bargo ya fita, da yake dakin kamar room and parlour ne, komawa yayi falon ya kwanta a kujera, gajiya nayi da jiransa na taso na biyoshi, bargon da yake rufe dashi na yaye, na kwanta kan jikinsa na rufemu da bargon, take naji bugun zuciyarsa ya fara chanjawa, mikewa yayi zaune tare dani akan jikinsa ke miye haka? Gadon baya isarki ne? Nace ni tsoro nikeji ka barni ni kadai, tsaki yaja chan da kike bacci ke kadai fa? Dan Allah malama ki tashi ki koma ki kwanta idan na din kikeso na barmiki, ya koma ya kwanta ya barta tsaye, wasu zazzafan hawaye suka zubomin toh ni meh namasa na juya na wuce a fusace dakin, ya yaye bargon ya bita da ido, idonsa cike da kwalla, ranar dai duk bacci gagararsu yayi ido bude suka kwana, ameerah na tunanim meh ta masa shiko shikadai yasan abunda ke damunsa.

Haka rayuwarmu dai ta kasance a dubai da safe idan munfita, khaleed na makale dani duk wani motsi nawa a idonsa, da dare kuma zai koma falo yayi kwanciyarsa, ganin nayi abun nashi rainin hankali ne ma, nima na daina kulashi dukda idan munfita da safe kausar kawai nakebi, da naga ya matso kusa dani na janye, idan ya riko hannuna na janye, ina ganin damuwa karara a fuskarsa amma na rasa gane meh yasa yakemin haka.

Da yaga hakan saima ya daina biyarmu idan kausar tace muje sai yace shi ya gaji dama duk harkar matace muje kawai, nuna masa nake ban damu ba, nan ko kasan zuciyata kamar na kurma ihu, haka muke fita mu dawo mu sameshi a hotel room ya zama kamar wani mara lafiya.

Haka muka kare kwananmu shida a dubai har ga gobe zamu dawo nigeria, bayan mundawo daga shopping nida kaisar, har mun bayarda kayan ta cargo zasu zo, wasu kananan kaya kawai zamu dauka a cikin kayan, na dawo nayi sallamah na shigo as usuall yana zaune yana kallonsa, na wuceshi na shiga daki nashiga toilet wanka, na fito daure da towel naganshi a bakin gado zaune, nayi kamar banganshi ba na cigaba da goge jikina, cewa yayi khadijah na waigo na kallesa ya kuramin ido kawai baice komai ba, nace malam lafiya dai? Ba amsa naje na juyawa ta dan towel dinda nake daure ya kwance ya fadi, na duka da sauri na dauko na daura idonsa kur a kaina, zumbur naga ya mike yayi fitarsa na bishi da kallon mamaki, zuciyata na suya, nayi sauri na saka night gown dina na nufi wurinshi dan naji meh ke damunsa.
[12/22, 6:36 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣8⃣1⃣ Fita nayi na sameshi ya dafe kansa, na zauna kusa dashi, da wata murya mai kashe jiki nakemasa magana, khaleed meh ke damunka? Girgizamun kai yayi ba komai, nace ni bakamin kama da wanda ba abunda ke damunsa ba, ni namaka laifi? Ya girgizamin kai? Nace wani ya maka laifi? Shima dai ya girgizamin kan, nace ka gaji da zama dubai ne? Shima dai a'ah, nace toh menene ka gayamin dan Allah, yace ba komai nace ok salmah ka tina da ita ne? Wani mugun kallo yayimin nace yi hakuri toh kaki gayamin meh ke damunka, ok ni kagaji da zama dani ne? Wata uwar tsawa ya dakamin saida na firgita, ke dan Allah ki tashi ki bani wuri, kinzo kin isheni da tambayoyi bayan nacemiki bakomai, cikin kuka nayi hanyar daki, saida na kusa shiga na waigo naga ni yake kallo, nace indai nice inshaAllah bazan kara zuwa kusa dakai ba, kayi hakuri na shigewata na barshi nan tsaye.

Daki na koma nasa kuka ni na matsu gari ya waye mu koma nigeria, dakyar bacci ya daukeni ranar, wurin khaleed ma haka take, gari na wayewa ameerah ta hada kayanta ta sauko ta wuce khaleed a daki, taje dakin kausar, kausar na ganinta tace ke sai jirgin sha biyu zamu tafi fa, nace haba na dauka na tara ne, tace har honeymoon din ya isheki? Na kalleta nayi murmushin yake, wannan ai ba honeymoon bane yawon siyayya dai mukazomiki kuma mungama, tace lafiyanki kuwa naganki wani iri, nace bakomai bacci kawai nikeji na kwanta abuna, tayi dariya broda ya hanaki bacci jiya kenan? Nace dan Allah malama kibarni nayi bacci, tace breakfast dinfa? Nace na yafe karki tadani kuma. Na juya nayi baccina.

Karfe goma kausar ta sauko breakfast, khaleed sai wara ido yake yaga ameerah bai ganta ba, kausar na zuwa tayi dariya, miye kake wani ware ido tana dakina tana bacci tace kada na tada ita, yace lafiya? Tace oho ai kai za'a tambaya may be kai ka hana mata bacci jiya, tashi yayi, ya nufi dakin kausar ya tura ya shiga, gabanta yaje ya duka tanata baccinta ya shafa fuskarta, duk tausayinta ya kamashi i'm sorry khadijah i don't want to hurt you, ya tashi shima yaje bayanta ya kwanta, ya rungomota ya sauke ajiyar zuciya shima take bacci ya daukeshi.

Kausar tagama breakfast ta dawo daki, koda ta duba taga sai baccinsu suke, murmushi kawai tayi soyayya ruwan zuma, wato tinda ba tayi breakfast ba shima ya fasa, gwanda susha baccin tare, nima Allah ya nunamin ina kwance a kirjin saeed dina, ta fito falo ta zauna ta barsu a dakin.

Sai 11.20 taje tafara tadasu, ameerah na buda ido taganta a cikin jikin khaleed, itadai abun ya dauremata kai shi ke cewa ta kyaleshi kuma meh ya kawoshi gunta yanzu? Janye hannuwansa tayi ya bude ido, ta tashi tashiga toilet ta wanko fuskar ta, shiko ya koma dakinsu ya kwaso nashi kayan, suka kama hanyar airport.

Ko a jirgi sai wani shan kamshi suke ba maiyiwa wani magana, sai ita da tafara bacci ya dora kanta a kafadarsa, itadai kausar bata dauka komai ba tinaninta duk cikin siyayyar ne.
Chapter 46 · 0% Book details