← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 36 OF 52

Sashe 36

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Khaleed yace salmah sallah zakiyi sai ki dawo ki kwanta, kaga ni ka kyaleni ai har yanzu da sauran lokaci dan gari baiyi haske ba, kara jan bargo tayi ta rufa, ya fisge bargon ya ciccebeta bai sauketa ko'ina ba sai toilet, ya shafa mata ruwa a fuska ya fito ya barota sai kiyi alwalan duk sallar da zakiyi ai baza ta dauki ko minti goma ba, ita duk haushi ya isheta, shiyasa bata son bakin auren nan da rayuwar 9ja duk sai abi a takuraka ita wlh dole ta koma germany ta cigaba da rayuwarta inda ba mai takurata sai abunda taga dama takeyi.

Koda tayo alwalar tafito yana zaune yana karatun alqur'an, taje tana duba kayanta batada hijabi ma ko daya, yana kalle da ita sai wata abaya ta dauko tasaka tayi rolling dankwali tazo zata kabbara sallah, yace salmah ina hijabanki? Da har bazata kar6a ba tace ko a saudi arabia dai naga ana sallah a haka, ta kabbara sallah shidai ya bita da ido.

Ya lura sallameh salar kawai tayi ta dane gado, ya lura ko addu'a batayi ba bare ayi wani zancen azkar, girgiza kai yayi wannan kamar ba salmarsa ba da yasani ada tanada rikon addininta kuma batada tsiwa, amma may be gajiyar biki ce bari yayi mata uzuri, ya gama karatunshi saida gari yayi haske yaje ya raba bayanta ya kwanta harda wani rungumota, ya sauke ajiyar zuciya sannan bacci ya daukeshi.

Ameerah ma haka take a wurinta, bacci gagararta yayi sam, dukda bawai saba kwanciya tayi tareda khaleed ba amma tinanin yana tareda wata macen ya hanata sukuni, tin suna fira itada kausar, har kausar ta gaji tayi baccinta ta barta, itama saida akayi kiran subh ta tashi, ta tada kausar sukayi sallah, sukayi azkar dinsu da karatun alqur'an da gari yayi haske sannan sukaje suka kwanta, sai lokacin bacci ya dauki ameerah.
[12/14, 8:49 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣5⃣0⃣ Sai wuraren 9.30 kausar ta farka, ameerah kuwa bacci take kausar ta lura jiya ba bacci tayi ba dan idonta sun nuna hakan, shiyasa bata tasheta ba kitchen taje ta fara hadamusu breakfast.

Kamshin girkin da ake ya tada salmah itafa yunwa takeji Allah, jiya tsabar masifa ko kazar da amare keci bataci ba, khaleed ta lura dashi da ya manne mata a jiki ta fara bubbugashi, sai bude ido yake yana rufewa akan tsabar baccin da ke idonsa, sauka tayi ta fara zagaye dakin ta lura da ledar da aka ajiye gefen gado, cikin sauri ta jawo gasassun kajine manya-manya guda biyu da yourghurt, ta jawo sai kuma taji sunyi sanyi qalau, itafa idan ba abu bai zafi taci ba bazata gamsu ba, zuwa tayi ta dinga bubbuga khaleed shikam bacci ya masa nauyi, haushi ya isheta, ta sauko ta fito parlounta tabi hanya ta shigo main parlour, sai kausar da tagani tafara jera kayan breakfast din a dining, kamshi duk ya isheta gashi ba dama tayiwa kausar magana sai hararta da kausar keyi, taja jikinta takoma dakinta, ruwa ta debo ta zubawa khaleed firgigit ya tashi zaune, kansa ya fara juya masa kamar ya tsage tsaban ciwo, dakyar ya bude ido yace ya akayi salmah zaki tadani da ruwan sanyi, duk sanyinnan da ake.
Ta zumbure baki yunwa nikeji Allah kasan tin jiya bakabani komai naci ba, yace toh laifinwa kin bari anyi maganar kirki ne jiyan bare har na ciyar dake? Ga kazarki nan ki dauka kici let me sleep please jiya kinsa nakasa bacci, kibarni yanzu kaina ciwo yakeyi sosai.

Cikin masifa tace toh nabarka kayi bacci ni yunwa ta illatani? Ni bazan iya cin kazar chan ba duk tayi sanyi, ni abu mai zafi nikeso, yace toh ki dauka kije ki dumama a micro wave ko a oven mana, nifa ban iya shiga kitchen ba ko ruwan zafi bana daurawa a gida, da mamaki ya kallota, kina nufin kenan komai baki iya girkawa ba, toh wa zai yimana girkin kenan? Kaga ni ba girki nazo nayi ba, kuma ai hakkinka ne ka ciyar dani, dan haka ka tashi ka nemomin abun breakfast kawai yunwa nikeji.

Khaleed haka ya sauko yafito kansa kamar ya tsage, yaji kamshi main parlour ya biyo, kausar yagani tanata faman jera abinci, ya tsaya yana kallonta koda ta waigo ta ganshi duk yayi wani iri dashi, tace good morning bro ya kar6amata, yace kausar zamu iya samun breakfast dinnan kuwa? A yatsine tace masa kaida wa?

Yace nida salmah mana, kausar tace ai itama macece tafito ta girka, ni abincin mutum 2 nayi, haka yayi daidai da fitowar ameerah sanye da sleeping dress dinta, tace kausar ki sammusu mana, kinsan baidace amarya ta shiga kitchen ba, khaleed ya waigota ya kura mata ido, saima ya nemi ciwon kansa ya rasa.

Matsowa tayi tana masa murmushi good morning ango, ya amaryar taka? Shidai yama kasa magana baisan meh yasa yakejin wani abu gameda ameerah ba, idan yana kallonta take kwakwalwarsa ke daina aiki.

Taje tana bude flask din abincin, tace haba kausar karki zama mai rowa please wannan girkin yayi mana yawa fa, kausar ta tabe baki toh uwar taimako ai sai ki dauri aniyar yiwa kishiya girki ni wlh bazan iya ba.

Murmushi nayi toh ai kema sister inlawnki ce, ta waigo gurin khaleed zata iya zuwa muyi breakfast din gabadaya, ko kuma ka dibarmata girkin kai kawai ya gyada mata, ta juya nidai bari naje nayi wanka, kausar tace nima haka bari nashiga dayan dakin, yau kayanki zan saka fa dan bazan iya maida wannan ba, nace toh ki biya kudin haya, mukayi dariya muka juya, mukabar khaleed anan yana murmushi ya bi ameerah da ido.
[9/15, 2:36 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/14, 7:35 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣5⃣1⃣ koda muka yo wanka kausar tazo tafito mana da wasu hadaddun kaya indian design iri dayane amma different colors, ni nawa red nata kuma lemon green, nace waike kausar meyasa kikeso koda yaushe na saka kayan India ne? Tace ai sister inlaw kayan india da English wears kyau suke maki sosai kamar danke akayi, kwalliya muka tsaya muka tsara, kamar masu zuwa beuty contest mukanmu munsan munyi kyau.

Kallon kausar nayi cikin tsokana nace waini bangane ba idan ni mijina nake yiwa kwalliya ke kuma fa? Tace ina kikasani i may get lucky yaya saeed yayi spoting dina, may be he'll fall in love, dariya mukayi nace muje muyi breakfast nidai yunwa nikeji, tace itama lets go.

Koda muka fito khaleed da salmah na kan dining, ita uwar kanzagin har tafara kwasar girki, kausar ta yunkura tafara masifa na tareta, na lura tinda muka fito daga ita salmah har khaleed din kallona suke, zama mukayi akan dining nace amarya kin tashi lafiya? Itadai tinda ta kalle ameerah tayi mata wani kwarjini wai dama itace matar khaleed din? Tasan tanada kyau a fuska amma ameerah tafita diri kyau dinma saidai ta nunamata hasken fata, har wannan khaleed zaice bayaso?

Maganar da ameerah tayiwa khaleed ta katse mata tunani, ango kai naga baka debi abincin ba, ko sai amaryar ta koshi ne? Shidai murmushi yayi kawai ya jawo plate zai fara diba, nace amarya yakamata tayi serving dinka ai salmah ya kalla, ta takarkare tana kwasar girki ko kallonsa batayi ba.
Mikewa nayi let me help you then kausar ta takemin kafa nasa kara, tsaye khaleed ya mike da hanzari yayo kaina, kafar har yanzu bata daina ciwo bane? Yazo ya duka yana dubawa, wani kamshi da ke fitowa daga jikin ameerah ya shaka wanda yasa numfashinsa ya kusa daukewa, take yaji yanayinsa ya fara sauyawa, mikewa yayi bari na kira saeed ya dubaki zanyi magana kausar ta karbe gaskiya broda ka kirashi dakyar take taka kafar, kallonta nayi da mamaki ta kannemin ido.

Khaleed yace ko na kirasa ba lalle bane ya dauka dan fushi yake dani let me txt him, salmah dai mamakin duniya ya isheta, itace amarya yakamata ita yake tarairaya amma kamar yama manta da ita agun yana kula matarsa, munafuki, tsaki taja tawuce daki khaleed yabita da ido shifa shaf ya manta tana wurin Allah, lallai yau ya jawowa kansa sabuwar rigima.

Juyawa yayi yabita ameerah ta riko hannunshi, ya waigo ya kallota naga bakayi breakfast dinba, kazauna kayi kafin abincin yayi sanyi, samun kansa yayi da kasa yimata gardama ya zauna tasowa tayi tayi serving dinsa yana shakar kamshita da ya fara zautashi, ya fara cin abincin bini-bini yana dagowa yana kallonta, idan sun hada ido sai suyiwa juna murmushi.

Kausar sai kallonsu take tana murmushi, lallai broda yafara kamuwa, watakila baigane hakan bane amma ita ta hango son ameerah da sha'awarta a idonshi, ana cikin haka mom tayi sallamah ta shigo.
[12/14, 8:26 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣5⃣2⃣ yunkura nayi intashi in tarota kausar ta rikeni idan kika fama kafar fa, wata harara na watsa mata na koma na zauna, mom da sauri ta karaso wurina meh ya sameki a kafa? Nace mom bakomai fa kawai nadan fadine naji ciwo kadan kuma ma na warke, mom tace faduwa garin ya? Toh kinje kinga doctor? Khaleed yace mom nayiwa saeed text nasan yana hanya tace toh shikenan, kirika kulawa ameerah yanzu sanyine ba wuya mutum yaji ciwo, nace relax mom mikewa nayi tsayi na dan taka naje na rungomota bafa wani ciwo naji ba, dazun ma bugewa nayi a kujera da naje tashi shine nayi kara sun dauka kafar kemin zafi, murmushi mom tayi toh shikenan Allah ya kiyaye gaba, zama tayi meh kukeci nima banyi breakfast ba, zama tayi nayi serving dinta tafara cin abincin.

Kausar ta kalla tace wato jiya sai naji shiru ko kausar? Kausar ta sadda kai kasa tana murmushi alamun kunya, mom tace wato nazama sirikarki yanzu ko? Khaleed yace mom meh ya faru take jin kunyarki? Mom tace don't worry zaku sani yanzu, kausar ta dago kai haba mom please karki fada mana, mom tayi dariya naji dadi da na ganku a haka, ina amaryar taka? Yace mom yanzu ta tashi, tace toh kaje ka kirata inaso zanyi magana daku.
Chapter 36 · 0% Book details