← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 52

Sashe 34

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ita kuma hotuna ta hango a tsakiyar gadonshi ta juya taja jikinta ta jawo hotunan, shikuma ya waigo ya dawo inda take, kici6is sai akan bayan ameerah da yake bude, take numfashinsa ya dauke, yabi surar jikinta da ido, fatar ameerah sumul ba tabo sai sheki take, matsawa yayi wurinta yasa hannu ya shafi bayan nata, ya runtse idonsa wasu abubuwa namasa yawo aka, ita kuma a razane ta waigo taga khaleed a durkushe bayanta, ido ta kuramasa da mamaki, shi kuma ya bude idonsa da suka fara chanja kala, suka fara kallon junansu, ameerah taji bazata iya jure kallonsa cikin ido ba, ta sauke idonta, hannu khaleed ya daga ya fara zagaye fuskarta, tace zuciyar ameerah ta fara bugawa da karfi kamar ta ballo kirjinta ta fito, ta runtse idonta gam, bakinta ya fara zagayewa da dan yatsansa, hakan yasa ameerah ta bude idonta tana kallonsa bata ankara ba sai bakin khaleed taji a nata ya fara kissing dinta, chak nufashinta ya tsaya, shiko tsutsar lips dinta yake kamar ya samu sweet, rurar karar da wayarsa take tafara dawo dashi hayyacinsa, dakyar ya janye bakinsa daga na ameerah ya duba wayar, salmah ya gani, ya dauka hello my love, jin haka yasa ameerah ta motsa daga sandarewar da tayi, ta yunkura ta tashi jikinta duk ya mutu, haka ta daure ta mike tsaye, tana taka kafar ta saka wata uwar qara ta koma ta zauna.

Arazane khaleed yayo kanta lafiya? Yama manta da waya yake, ta nuna masa kafarta tana kukan shagwa6a, yace ina zataje? Tace dakinta, chak ya dauketa kamar wata baby, yayi hanyar dakinta da ita, bai direta ko'ina ba sai kan gado, yaja bargo ya rufeta har ya juya ya tafi ya waigo kuma, yayi wani kicin-kicin da fuska meh ya kaiki dakina? Check ta nuna masa da duk ta wani dukunkuneshi a hannunta, tsaki yaja nakine mom tace sai namiki kayan fadar kishiya, kisiye abunda kikeso idan kuma bakiso ki yadda, ya juya ya ficewarsa
[12/12, 7:57 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣3⃣9⃣ Ameerah tabi khaleed da kallon mamaki shi wannan wai meh yake damunsa ne? Ko har ya manta abunda ya mata ne yanzun? Juyawa tayi ta rufe idonta dan tayi bacci, amma ina baccin yaki zuwa sai abunda ya faru tsakaninta da khaleed take tariyowa tana faman murmushi abun kamar a mafarki, sai wuraren karfe 3 tasamu bacci yayi gaba da ita.
A wurin khaleed ma haka ne tinda yaje daki ya kwanta, sai tinani yake ya akayi har yayi kissing ameerah yau? Harda marin kansa yayi, dole na nisanci yarinyar nan kafin ta wargazamin duk wani shiri nawa, ga alkawarin da nayiwa salmah, sai lokacin ya tinada salmah ta kirashi fa, kafin ameerah ta kwalla kara, da sauri yajawo wayarsa yasa kiranta missed call 3 taki dauka, nan wai ita fushi tayi tinda taji karar ameerah a kusa dashi dats means suna tare, namiji fa munafuki ne yana nuna mata ba abunda ke tsakaninsa da ameerah amma meh yakeyi a tareda ita? Harda ajiye call dinta yana kula matarsa, wallahi tinda khaleed yayi mata haka akan ameerah ranar da tashigo gidan gobe kenan zata sanya yayi waje da ita.

Shiko baisan meyasa rashin daukar wayar da salmah batayiba, bai wani damuwarshi ba, ajiye wayar yayi, yayi kwanciyarsa, amma sai ya nemi bacci ya rasa abunda ya faru dashi da ameerah kawai yake tinani, duk iya kokarinsa na ganin ya hana kansa tinanin ya kasa, daga bisani ya tashi yafara salloli anan kan sallaya bacci yayi gaba dashi.

Washe gari ta kama ranar daurin auren khaleed da salmah, karfe goma na safe za'a dauran, amma ango na kan sallaya yana kwasar bacci dakyar ma ya iya tashi yayi sallar asubah.
Ameerah kuwa da ta tashi tayi wankanta ta koma ta kwanta, sai karfe goma ta farka, ta tashi taje kitchen ta hada dan breakfast, sai sallamar aunty fareedah taji tazo da gudunta ta rungomota, tace yau dai munzo tausar kirji inanan har dare, dan kar en kawo amarya suzo sumiki rashin mutunci cikin murnata nace nagode antina, dan basket ta mikomin tace ga kayan breakfast nazomiki dashi, nace ohh antina you are the best, kaman kinsan yunwa nakeji yanzu ma haka da kitchen zanje, najata muka wuce dakina.
[12/12, 8:25 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣4⃣0⃣ Munje daki na zuba breakfast dina inaci, muna dan taba fira da aunty fareedah, sai ga kausar ta shigo a dan hargitse, nace ya akayi kika fado haka kamar watchche aka koro? Tazo ta wani turbune fuska, tace ina yaya khaleed? Da mamaki na kalleta kamarya ba yau ake daurin aurensa ba may be yana chan, tace kinga ina baccina mai dadi fa dad ya tasoni, wai antaru wurin daura aure amma ba ango ba alamarsa, dad da friends dinsa sai kiran wayarshi suke yaki dauka, shine akace nazo na duba ko lafiya, a razane na mike nace bari naje na duba dakinsa ko kalau yake, aunty fareedah ta jawoni ki kyaleshi kawai kar a daura auren ma, ke miye naki a ciki? Murmushi nayi anti fareedah kishi ba hauka bane fa, bazan iya yimishi haka ba bayan ya tara jama'a, after all banmasani ba ko bayada lafiya ne, kausar ta tabe baki ai sai kije ki taimaka mishi ya auromiki kishiya, nidai nafita na barsu ina dan Murmushi.

Dakinsa na tura nayi sa'a a bude, chan na hangoshi akan sallaya kwance, da sauri naje wurinshi na taba jikinsa, naji ba zafi sai baccinsa yake kwasa, na rasa ya zanyi na tadashi, naje ina bubbugashi, jawoni yayi ya rungume ya cigaba da baccinsa hankali kwance, wayarsa ce ta dinga ruri, dakyar na janye hannunshi naje na jawota, dad nagani na daga dad yq fara zabgq masifa idan yasan bayason auren ubanwa yasa Ya tara jama'a wannan ai wulaqanci ne, minti goma ya bashi ya iso wurin daurin auren ya kashe wayarsa.

Na rasa ya zanyi, naje na bubbuga khaleed amma sai ya bude ido ya rufe kamar dan maye, sai jawoni da ya karayi a jikinshi ya rungume, takarkarewa nayi na gantsara masa cizo a hannu, a razane ya mike zaune ke mahaukaciyar inace ne? Ar you a vampire? Are u thirsty of my blood? Yama ki bari nayi magana meh ya kawoki dakina yanzu? Mikewa nayi na dauko agogo na miko masa, koda ya duba 10.40, a razane ya mike tsaye ya dora hannu aka what have i done?

Kallona yayi yafara nunani it all your fault, da mamaki na kalloshi my fault kuma? Ashe dana sani na barka ka cigaba da baccinka nazo na tadaka shine laifina? Naja tsaki na juyawata kuma dad yace 10 minutes ya baka, ka isa wurin daurin aure dan mutane sunfara gajiya da jiran ango, na kama hanyar barin dakin.
[9/15, 2:34 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/13, 8:25 AM] Deejah Abdul: Dream girl na deejah abdul
1⃣4⃣5⃣ Munanan zaune a daki duk ihunsu ya damemu, aunty fareedah tasa na tsala kwalliya da wani dakakken lesi orange sai zuba kamshi nike, niko sai magiya nike musu kar sutafi su barni dan Allah, aunty fareedah tace itadai mijinta na jiranta amma zata kara jira har suzo sidw dina dan a ka'idah dole akawo amarya gun uwargida indai iyayen nata datijai ne, haka kuwa akayi muna zaune mukaji alamar shigowa part dina. En kawo amarya sai santin part dina suke duk da cewa itace amarya amma ba abunda zata nunamin, muna haka mukaji anafadin ina uwargidan take ne? Aunty fareedah tace ku tashi mu samesu parlour kadda su shigo miki daki, mukatashi mukayi parlour aunty fareedah tace gafa uwar gida ran gida nan, idan bata ba gida suka tabe baki, aka zazzauna kan kujeru, wasu tsofaffi sai nasiha suke wai ga kanwata nan na riketa Amana mu zauna lafiya, duk abunda tayi ba daidai ba na luradda ita, ni sai waige-waige nake dan kwata-kwata bangane amaryar ba, tinda a al'adance za'a samu amarya rufe a mayafi tana dan kukan rabuwa da gidansu, amma nan din kam ni banga ko waccensu a lullu6e ba, aunty fareedah na dan taba ina mata rada wai wacece amaryar ne? Tace itama batasaniba, khadijah nasir tace wai ina amaryar ne mudai bamu ganta ba sai cewa kuke a riketa amana toh wa za'a rike din tinda mudai bamu ganta ba.

Chan mukaji murya daga gefe gani nice amaryar ko da matsala ne? Na dubeta dakyau naga wata fara gajera mai kwala-kwalan ido ta zubo mana su, take na tunafa kaman hotunanta ne nagani a dakin khaleed ranar.

Aunty fareedah tace taya za'ayi ki zama amarya? Mudai munsan amaryar hausawa da kunya suke, ko wacce a mayafi ake kawota koda kuwa batayi kuka ba dole ne ta rufe fuska ko ango sai ya biya yake gani.

Tsaki mukaji tayi ai zamani ya chanja, meh zaisani kuka kamar wadda za'a kawo gidan makiyinta? Kuma na rufe fuska abun kunya nayi ne? Aure aka dauramin ba wani mugun abu ba, mudai sai kallon juna muke cikeda mamaki, sai chan wata tsohuwa ta fara yimata masifa, wato ke salamatu rashin kunya kadai kika koyo turai, ta katseta niga gwaggo ki daina yimin masifa, sai chan wata figaggiya daga cikin kawayenta tace toh wacece kishiyar tata a cikinku? Aunty fareedah tace ai batada kishiya anan wurin nan da zaman aure takeyi ba zaman kishi ba.
Chapter 34 · 0% Book details