← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 52

Sashe 38

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Mom tace wannan ai zancen banza ma yake, ama daina zancen yanzu, ameerah share hawayenki, kinfita daraja a wurina, kuma ki kwantar da hankalinki kiyi zaman aure kinji? Karki sake tinanin wai auren plan kukayi, kifara dauka aure kikayi kamar ko wace mace, na gyada mata kai kawai ina share kwalla, daga kai nayi muka hada ido da khaleed wani mugun kallo yayimin na dukadda kai kasa ina murmushi.
[9/15, 2:37 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah abdul
1⃣5⃣5⃣ mom tace zauna saeed muyi magana, ya zauna duk muka tsura mata ido danjin abinda zatace, mom tace wannan zamanin yanada abun mamaki da yawa, rashin tarbiya yayi yawa, idan kaba yaranka freedom da yawa bakasan meh zasuje su kwaso maka ba, saeed wata alfarma nakeson kayimin, domin nidai tin kana yaro nasanka nasan halinka, zan iya bada shaida akanka, alfarma nakeson kayimin ko nace wata kyauta zanmaka, zuciyar kausar tafara bugawa da karfi, saeed yace mom duk abunda kike nema aguna indai inadashi ko ikonsa zanmiki, kifadi bukatarki kawai.

Hayaniya mukaji ta barke a part din kausar sai shewa suke ga alama kawayenta ne sukazo, ihunsu kawai suke sunma hanamu jin komai, nace mom kutashi muje part dina may be zaifi dama, girgiza kai mom tayi Allah ya shirya tafasan duk muna zaune falonnan amma suka ishemu da ihu a gida kamar gidan kalcha, khaleed yace mom bari naje nayimusu magana, mom tace kabarshi kawai, ameerah muje part din naki, muka tashi mukatafi, saida na rurrufe ko'ina sannan muka samu dama-damar hayaniyarsu.
Mom tace ai kunga irin abunda nake gudu, shiyasa nikeso nanemi wannan alfarma gunka saeed, ammafa ba dole, idan akwai abunda baimaka ba ka sanardani kawai kada kaji komai ni zanfahimceka, kausar gatanan nakeso nayi maka kyauta dan banason tayimin zabi irin na yayanta, zuciyar kausar kamar ta fito waje dan tsoron amsar da saeed zai bayar.

Saeed yayi murmushi mom mace irin kausar bai kamata kice zakiyi kyautarta ba kamar wata er tsana, takai matsayin da ko wanne namiji zai iya sonta idan ya samu, amma a ganina mom yakamata muji ra'ayinta kafin mu yake hukunci. Mom tace kausar wai bakyason yayanki saeed? Kausar a kunyace ta tashi da gudu tayi dakina, mom tace ja'ira nidai nasan zabina bayada aibu, mukasa dariya, mom tace da fatar kagane amsar a yanzu? Gyada kai yayi wani farinciki yana ratsashi wa zaiki mace irin kausar, mom idan hakane bakomai na karbi tayinki Allah ya sanya alkhairi, mukace ameen, mom tace toh alhamdulillah nagode sosai duk sanda ka shirya zaka iya turo magabatanka, i'm glad ka amsa tayina, ba kamar abokinka ba muka kalli khaleed ya wani dukar dakai kamar wani mara gaskiya, mom tace na lura kamar ma ba jituwa tsakaninku dan Allah komai ya wuce ku daidaita, rashin aboki irinka agun khaleed ba karamin rashi bane, yana bukatar wanda zai rika saitashi a hanya, saeed yace bakomai mom zamu daidai ta bare yanzu zamu zama inlaws, mukasa dariya khaleed ya kaimasa duka amma kai bakada kunya fa, yanzu sai ka auri kanwata? Saeed yace ai ko yayarka ce zan aureta bare kanwa mukayi dariya mu duka.

Mom tace toh mashaAllah tinda komai ya daidaita ni zantafi, sauran ku manta da abunda na gayamuku, you should give your marriage a chance kunji, kallon juna muka tsayayi har mom ta juya ta tafi, saida saeed yayi gyaran murya muka tina inda muke, mom fa ta tafi yacemin, da gudu nafita nabita har ta shige mota, nace mom har kin shige mota? Tace toh kin tsaya kallon mijinki ba dole na wuce na barku ba, a kunyace na dukar dakai mom tace ameerah just keep on trying, naga wani sirrin so a idon khaleed da yake kallonki dashi, watakila shi bai gano hakan ba, amma idan kika dage shi da kanshi zai gane har ya furta miki, ni zantafi taja motarta ta wuce, nayi wata sassanyar ajiyar zuciya na juya na koma falona.

Koda na koma khaleed da saeed suna fira, khaleed nacewa friend bakasan damuwa da kadaici da na shiga ba da baka tare dani, saeed yace ai nasan baka iyayi saidani, khaleed yace oh yanzu da nayi bakai dinfa? Saeed yace ai shiyasa naga ka yamutse kamar ba ango ba, lokacin na shigo nace lallai yau kara'in abota ake, saeed yace wai ina ciwon kafar ne?

Nace ni banida wani ciwon kafa inaga dai shida kanwarsa keson ganinka shiyasa suka hada plan, saeed yayi dariya oh really nace eh.
[9/15, 2:37 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah abdul
1⃣5⃣6⃣ khaleed baki bude yake kallona, na daga masa gira ina dariya, wato mu zakiyiwa sharri ko? Nace ba wani sharri ba gashi kana fada masa kayi kewarsa ba? Saeed yace toh ni kiramin amaryar tawa ma mu zanta, nace iye lallai maza bakuda kunya? Wato yaya saeed haka zakayiwa antina ko? Dariya yayi toh wa zai ki kari? Kuma antin taki batada matsala zata amince, khaleed yace toh shine ni kake fushi dani din dan na nemi karin? Saeed yace ni ba karin aurenka ya dameni ba, yarinyar da kazama obsessed akantane, it turns out ma batada kunya, khaleed yace toh ya isheka dai, ai laifi akayimata, saeed yace laifin meh? Khaleed yace kishiya mana ai nasan ba macen da takeson kishiya sannan kuma honeymoon dinda mukeso muje mu sake shima cancel , saeed yace ai ita tayi wasa da damarta.

Nace excuse me guy waye kishiyarta anan wurin? Ni ba kishiyarta brace yakamata ta gane, idan kuma ma haka ne ai ni akayiwa kishiyar ba ita ba, dan a bayana tazo, khaleed yace lallai yarinyar nan dama kinada baki ashe? Nace ai kai yakamata na tambaya dan nagan kana kokarin kare matarka, alhalin itace mai laifi, yace kudai kuka sani ni da badan wannan kawayen nata da suka damu mutane ba, da naje na lalla6a ta, nace malam if you are dat romantic ai kawayenta bazasu dameka ba, sai kaje ko a gabansu ka lallasheta, khaleed yace madam are you jelous, nace jealous of who? Dama ka fadi hakan ne just to make me jelous? Yace toh naga kin wani bata fuska dan nace zan lalla6a abata, dariya nayi da ta bayanna fararen hakorana, kaga malam it obvious matarka bata sona, so banga dalilin da zaisa nayi farinciki dan ka ambaci sunanta ba, ni dakai da ita kuje kuyi duk abunda kuka ga dama i really don't care amma dai a daina min zancenta a falona ehe, khaleed yace falonki ko falon gidana? Nace gidanka amma falona dan nikeda hakki a part dinnan as long as ina gidannan, khaleed ya taso yayo kaina wai yaushe kika rainani, ya bini da gudu muna zagayen falo muna dariya, saeed dai ya zama dan kallo dan anmanta dashi a falo, ya kusa chafkoni na afka dakina na datse kofa ina masa gwalo, komawa yayi baya yana dariya ya zauna, muryar saeed na jiyo nidai kifitomin da amaryata idan kungama soyayyar.

Khaleed yace soyayya kuma? Saeed yace toh meh zance kiyayya kuka gama ne? Abokina ka kamu fa Allah blif it or not, you are just obsessed wit salmah but i can see a true love in your eyes for ameerah, khaleed yace kama daina zancennan ba abunda kake tinani bane, saeed yace toh gamu gani dai.

Kausar na sama a daki tayi zugum, tana murmushi rungumeta nayi i'm really happy for you, mafarkinki ya kusa zama gaskia, zaki samu soyayyar wanda kikeso yaya saeed na sonki u are so lucky, how i wish nima zansamu nawa.

Kausar tace may be baki lura bane amma ni na hango soyayyarki a idon broda, kibashi dan lokaci kawai shima zaigano ya kamu da sonki, nace i hope so dear, tashi muje yaya saeed nason magana dake, tace itadai kunya takeji nace kausar ai dole ne dan ku fahimci juns, naja hannunta muka fita, saeed na ganinmu ya Mike tsaye amaryata ki sameni a waje, kar su samana ido su hanamu jin dadin soyayya, ya mike yafita kausar tabi bayanshi, khaleed yace mara kunya binshi zakiyi? Abokina nane fa? Harara kausar ta watso masa ta ficewarta nasa dariya, karfa ka takurawa kanwata.

Yace kanwarki? Ai ta girmeki, nace oho dai ai tinda nike auren yayanta tazama kanwata, khaleed yace dagaske ni mijinki ne? Harara na watso masa sannan nace haka naji ana cewa mukayi dariya, ashe duk abunda ake a idon salmah da kawayenta suna leke, shiru ne ya biyo baya a falon, bini - bini muna satar kallon juna, da muka hada ido na basar nace naji part din amaryar taka shiru ai sai ka tashi ka tafi ka tsaya kana kallon mutane, mikewa yayi tsaye yace hakane fa, yayi kamar zaiwuce sai ji nayi an damko ni, nafara er karar shagwaba ina kokarin zillewa, amma ya rikeni tamau jansa na rikay a haka shiko ya biyoni amma bai sakemin hannu ba.
Chapter 38 · 0% Book details