← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 39 OF 52

Sashe 39

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ban ankara ba naje na buga kaina a gina, kara na saki wayyo mamata, nafara kuka shagwaba, rumfa yayimin da hannuwansa ba ta inda zanwuce? Wa kike gayawa magana tin dazu? Yaushe nafara wasa dake? Nafara hawaye kayi hakuri bazan kar ba, hannu naga ya daga kamar zai dokeni na runtse idona gam jikina ya fara bari, sai ji nayi ya fara gogemin hawayen da nike, kuramin ido yayi jin shiru yasa na bude idona, kallon juna mukeyi for quite sometimes, naji bazan iya jure hakan ba na sauke idona kasa, cemasa nayi khaleed please i'm sorry bazan ka.......... Ban kammala maganata ba naji bakinsa a nawa, tin ina kokarin kwace kaina har nagaji na kyaleshi jikina duk yayi sanyi nakasa komai, shiko baidaina abunda yakeyi ba, abun naji ya fara wuce gona da iri, na tureshi da karfi idonsa sun rikedi sunyi ja ya budesu dakyar ya kalleni, sai kuma ya juya da karfi ya nufi part dinshi, ni kuma nakoma kan seater na kwanta ina mayarda numfashi.
[9/15, 2:38 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah abdul
1⃣5⃣7⃣ khaleed ya koma dakinsa ya fada kan gado yayi rub da ciki yana mayarda numfashi, wai dagaske na fara son yarinyar nan ne? A'ah inaga dai sha'awa ce kawai, idan haka ne kuwa dole na nisanceta dan idan nayi amfani da ita dan biyan bukatata kawai ban mata adalci ba, i have to be sure of my feelings first.

Salmah kuwa tanan tana daukar shawarar abokai, a yanda sukaga khaleed da ameerah yau sun tabbata akwai so a tsakaninsu ita kadai dai yake fooling, wata tace a'ah ni a tunanina ma shi yake sonta dan kunga dai yadda ta tureshi daga jikinta, sukace kuma hakane fa.

Salmah tace ai namiji munafuki ne wlh, shiyasa kwata-kwata i'm not into men, wannan auren ma tsautsayi ne, kuma ai duk laifinkune ku kuka rika zugani wai ankasani, wata macen ta ture sarautata, kunaga fa har marina yayi dazu a gabanta, ai tariga ta rainani dole na dauki mataki dan Allah ko zanbar gidannan sai na fitar da ita, dannifa bazama nazoyi ba bazan iya wannan rayuwar auren ba.

Wata daga cikinsu tace ai salmah duk abunda zakiyi tinda mahaifiyarshi ke sonta bazaki iya sa ya saketa ba, dan gudun zuciyarta da yakeyi, hanya daya ta ragemiki ki aje duk wani jin kai ki nuna masa soyayya, ki janye hankalinshi daga kanta, idan ta lura batada wani muhimmanci a rayuwarsa dakanta zata nemi saki tayi gaba, tinda ita ba icce bace dole ta buqaci mijinta saidai kuma in duk mune, ta daga mata gira suka tafe.

Salmah tace shikenan zangwada hakan naga idan zan iya, suka mike zasu tafi itako ta shiga dakinta tayi wanka, bayan tafito ta gyara kanta ta feshe jikinta, tasa wasu tsirarrun kaya ta nufi sashen khaleed.

Yananan kwance rub da ciki taje ta hau kan gadon, ta dafashi sweetheart ya waigo ya bude ido dakyar ya kalleta, a yanda ya ganta yayi saurin kawar da kanshi idan banda mugunta yasan rigima kawai ta kawota mezaisa tayi wannan shigar? Kallonta ya sakeyi ta gefen ido sai yaga tayimai murmushi sabanin tunaninsa, janyo hannuwanta yayi ameerah please kiyi hakuri, ameerah ta maimaita a ranta lallai ma wannan, amma sai ta basar it ok aini yakamata na baka hakuri nice nayi laifi, kuma inaso kaba mom hakuri please on my behalf, shidai yakasa gasgata kunnuwansa sai kallonta yake, hannuwanta tasa ta tallabo fuskarsa, ya kayi shiru my baby ko bakayi hakuri bane? Girgiza mata kai kawai yayi bai ankara ba salmah ta fara kissing dinshi, ba bata lokaci ya fara maida mata da martani, cikin kankanen lokaci khaleed ya rikecewa salmah, nidai deejah nafita na basu wuri dan abun yafi karfin idona bari naje na leko ameerah yau khaleed ya angwance.

Ameerah na kwance inda na barta idonta a rufe, abun duniya ya isheta shin dagaske khaleed dinta ya fara sonta ne? Wata zuciyar tace karki yaudare kanki wata kila sha'awa ce kawai kibari harki kara tabbatarwa, tana cikin haka sai ga kausar ta shigo da gudunta, ta fado mata ta Mike zaune a dan firgice, kausar tayi hugging dinta cike da farinciki i'm so happy today yaya saeed yana sona, nace congratulations dagoni tayi ya najiki haka ba kuzari, nace bakomai kausar bacci na fara kika tadani inaga shiyasa, tace ina broda ne ba nan na barshi ba? Nace mata ya tafi ai tindazu, ta tabe baki karki damu very soon kema zaki samu taki soyayyar, bari intashi intafi nace haba kausar yanzu tafiya zakiyi ki barni? Ki dawo nan gidan mana ki zauna, dariya tayi kamar dai wata karamar yarinya? Kiyi hakuri ai anan zamu rika zance da yaya saeed it possible ma kullum sai kin ganni, ta tashi tashiga daki ta hado kayanta, na mata rakiya ta fita.

Khaleed kuwa yau ansamu nutsuwa ba laifi, salmah ma ta jinjina masa yakai jarumi dan ya wahalar da ita sosai toh abunka da sabon shiga, kwance suke a gado suna kallon ceiling, khaleed ya jawo salmah ta tureshi ni nagaji ka kyaleni bacci zanyi, kuma kaje ka nemo mana lunch kan natashi, bargo taja kawai tayi rufarta.

Murmushi kawai yayi yatashi ya fada toilet yayi wanka, anyi kiran azahar yayo alwala yafito, salmah tayi bacci bai tasheta ba dan yasan ta gaji, yayi massalaci daga chan yayo mata takeaway a mr bigs shi kuma snacks da lemo kawai ya siyowa kansa, koda ya dawo stil tana bacci kuma gashi anyi la'asar tada ita yayi sannan ta tashi, wanka tayi a dakinsa kawai ta dauki ledar takeaway dinta tayi part dinta.
[9/15, 2:40 PM] ‪+234 706 332 8523‬: Dream girl na deejah abdul
1⃣5⃣8⃣ A haka dai rayuwa ta kasance a gidan khaleed, ameerah tin ranarda khaleed ya fita part dinta bai dawo ba, har ta fara zargin kanta maybe abunda ta masa ranar ne yasa yayi fushi amma ita bazata iya zuwa tabashi hakuri ba gaskiya ko main parlour da take zama yadaina shigowa duk inda ya ganta tashi yakeyi, abun duniya ya isheta.

Abunda bata sani ba shima din a wahale yake, salmah sai taga dama take bashi kanta ba, kuma ko ta yarda dinma bazata bari yayi wani gamsuwa ba ta tureshi itafa ta gaji, kullum part dinta cike da kawayenta bayada sakewa da matarsa, abokanta sunfishi muhimmanci, fita take kuma son ranta duk inda taga dama, kuma sai taga dama zata dawo, shikansa ya rasa dalilin da yasa yakasa rabuwa da ita, ameerah kuwa ya kasa yadda da cewa sonta ne yake, dan duk dare sai yaje ya lekata tana bashi tausayi, amma abunda ya yarda dashi shine, rashin kulawar matarsa yasa yakejin kamar yana bukatar ameerah, da zaisamu kulawarta shi bazai ji hakan ba, kuma indai ba ya tabbatar da cewa yana sonta ba bazai amince da ya kusanceta ba.

Kwanaki sai dada tafiya suke, anyi baikon kausar da saeed munyi exams na first semester har mungama, amma ba zancen zuwa honeymoon dan sarauniyarsa tace indai ba Germany za'aje ba ita ba inda zataje ya kyaleta, shiko yasan idan har ya amince da zuwa Germany ba tsira zaiyi ba dan ko chan tanada friends ba kulashi zatayi ba, da mom tamasa maganar honeymoon cewa yayi abar zancen kawai dan duk yayi magana damu munce munfasa zuwa, idan lokacin zuwa aikin hajji yayi sai abiya mana, da mom ta tambiyeni banmata gardama ba shiyasa ta kyalemu.

Wasa-wasa har auren khaleed da salmah yayi wata 3, gashi har anfara shirye-shiryen auren kausar ansaka date nan da wata biyu, na zama nikadai sai rama nike, aunty fareedah kuwa banida damar zuwa wurinta dan kunyarta nike, tayita kiran wayata naki dagawa dan avoiding dinta nike, ga saudah na bauchi, khadijah nasir taje hutu minna, mama kuwa ko naje gida ba wani sakemin take ba, su suhaila ma na dan zuwa amma sai weekend, na roki mama ta bani ko khairi ko fatima su dawo wurina taki.

Ranar ina zaune a falona na buga uban tagumi, sai sallamar anti fareedah naji, na karba mata amma duk na dabirce sai kame-kame nake, ta kuramin ido tana watsomin harara, tace yanzu Ameerah abunda kikayi kin kyauta kenan? Nace cikin sarkewar murya aunty fareedah dan Allah kiyi hakuri wlh ba laifina bane, wani mugun kallo ta wurgomin na dukar dakai, zuwa tayi taja hannuna muka zauna, ameerah mai kika daukeni ne? Kin dauka kawai dan saeed zai auri kausar nayi fushi dake? Shiyasa kike guduna bakya daukar call dina? Wlh ni kinban mamaki a lokacinda nike bukatar aboki kika gujeni, take kwalla ta cikomin ido kiyi hakuri wlh Allah kunyarki nikeji, gani nake duk ban kyauta miki ba, inaji ina gani zanbari ayimiki kishiya kuma kinsan yanda nike da kausar zaki doka ko ni na hadasu, murmushi tayi ni wlh banyi fushi dake ba, dan saeed zai auri kausar miye a ciki? Ni namayi farinciki da Allah yasa er gidan mutunci zai aura, kuma sanin yanda kuke da ita yasa hankalina ya kara kwanciya, dan nasan bazaki bari ta cutar dani ba.

Kuka na fashe dashi na rungumeta Allah sarki antina u are d best, kiyi hakuri gudunki da nayi, tace bakomai ya wuce, har muna hada baki tare kowa yace ya naga duk kinyi rama? Mukayi dariya tacemin batada lfy ne yanzu bata cika lfy ba, amma banzo dubata ba, nace kiyi hakuri nauyinki nakeji, nakasa zuwa dubaki, tace ke kigayamin meyake damuwarki, na kwashe nagayamata, tayimin fada sosai, wai duk ni nayi sake abubuwan da duk ta koyamin na watsar, kuma ko sha'awar tawa yake miye a ciki ai mijina ne, ta haka zan janyoshi a jikina kulawar da zanbashi ita zatasa ya fara sona, nayimata godiya tare da alkawarin zan janyo mijina, na rakata ta tafi.
[9/15, 2:41 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/16, 7:01 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣5⃣9⃣ bayan tafiyar aunty fareedah nida kaina, nayiwa kaina fada, wannan bazata fishsheni ba, na zauna ina jiran miracle, ko Allah ma yace tashi in taimakeka, tinda shi guduna yake ni zanbi duk wata hanya da zata sadani dashi batareda ya fahimci ra'ayinsa nike ja.
Chapter 39 · 0% Book details