← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 52

Sashe 47

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Suna saukowa jirgi direct gida aka wuce dasu dan mom bata dawo ba bare suje gaida ita, ana saukesu suka shiga gidan kowa part dinsa ya nufa.
[9/15, 2:45 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/23, 7:29 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣8⃣2⃣ Haka dai zama ya kasance mana da khaleed baya zuwa part dina bana zuwa nashi, idan ma munhadu a hanya kowa zai kama gabansa na rasa dalilin haka, amma nidai na dauki alwashin bazan kara kai kaina gurinsa ba bare ya disga ni, na lura sai rama yake da baki, duk muka hadu zanga alamun yanason gayamin wani abun amma sai ya fasa, nima kuma sai na basar.

Bikin kausar na matsowa dan yau sauran sati daya, shirye-shirye kawai akeyi, ni kuwa duk naje skul nadawo zanje gidan aunty fareedah bana wani tsayawa ayi shirye-shirye dani, kausar tayi masifa har tagaji, nace tayi hakuri baikamata na guji aunty fareedah yanzu ba, dukda ke kanwata ce itama kawatace kuma tanada muhimmanci sosai a gurina, dan nima lokacin da khaleed zai auro salmah ta tsayamin, da yake kausar mai hankali ce ta fahimta haka ma mom ta bani goyon baya, aunty fareedah kuwa taji dadin haka, tasan tanada muhimmanci a wurina ko kausar ta auri saeed bazan juya mata baya ba, duk da tana nunawa bakomai bane amma ni na tabbata tana juriya ne kawai dan ba macen da mijinta zaiyiwa kishiya tace bataji ciwon haka ba koma yane, shiyasa nima na boyemata tawa matsalar.

Ana saura kwana 3 biki, Aliyu da salim suka zo, nida khaleed akace muje mu daukosu airport, na dade banyi farinciki irin na yau ba nayi missing danuwana rabin jiki, maimakon mutafi a mota daya kowa tasa yaja, muka nufi airport ina gaba khaleed na bina baya har muka sauka, ina hangosu na tashi da guduna na tafi inajin khaleed na kirana nayi banza dashi, naje na makalkale Aliyu cikin farinciki, yace sweet sis i missed you alot, nace nima danuwa, naje nayi hugging salim dake tsaye yana dariya khaleed ya shiga tsakani, ya jawoshi ya rungume, kannemin ido yayi, kinyi hugging dan uwanki nima kibari nayi nawa, na harareshi na basar troly aliyu naja, khaleed ya janyo aliyu yayi hugging ya hado dani, radamin yayi a kunne karki sake ki rungumemin danuwa idan hug kikeso i'm all free janye jikina nayi da sauri, a raina nace dan rainin hankali kawai, na basar nace salim ya karatun yace sis karatu ba dadi we missed home alot, nace gaskiya hakane no place like home, yanzu kwana nawa zakuyi mana yace a week, nace 1 week kawai danuwa, ya marairaicemin idan kikace na zauna ni da gudu zan tattaro kayana na dawo coz i missed you guys alot.

Hannunsa naja na rike gam, tareda jawo trolynsa a dayan hannun, nace hakuri dai zakayi duk karatun kwana nawane zaku kammala very soon ku dawo, gida khaleed gyran murya yayi, ya shige tsakiyar mu, ya raba hannun cewa aliyu yayi excuse me broda inlaw this is my place, aliyu yayi dariya tareda jayewa hakanefa, bari na koma gefe nace wai miye haka mutum da danuwansa? Cewa yayi amma ai mutane zasu dauka saurayi da budurwa ne, baki bude na tsaya ina kallonsa, nace masa kanen nawa? Yace eh mana ko bakigan yafiki tsayi bane? Salim yaja aliyu danuwa muje kan sugama dramarsu mu shiga mota suka wuce suna dariya suka barmu a tsaye.

Nace are you jelous? Yace yes ofcouurse i'm, dariya nayi just drop d act now, tin yaushe kafara kishina gira ya dagamin, tin ranar da kika zama tawa mana, murgudamasa baki nayi just stop pretending bayan ka daina kula dani, cewa yayi does dat hurt you? Nace ofcourse not dama indan ka batamin rai kakeyi kayi a banza na kara murgudamai baki.

Jan bakin yayi wallahi idan kika kara murgudamin baki sai na baki hot kiss anan wurin, nace nan wurin with all these people you are not serious, jawoni yayi ya hada goshina da nashi, just dare me and see sai na nunamiki ni banida kunya i'll kiss yo here and right now, ganin nayi dagaske yake fa na tureshi na wuce gaba abina ina sauri, sai yanzu muka lura da su salim har sun wuce, khaleed yayi sauri ya cimmin ya rungumoni muka cigaba da tafiya, nidai na kyaleshi a raina sai mamaki nake shidai khaleed na rasa gane kansa, wani lokacin he'll make me fell like he love me wani lokacin kuma sai naji kamar banida wani muhimmanci a wurinshi
[12/23, 8:13 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣8⃣3⃣ koda muka iso wurin mota duk sun shiga motata, cikin murnata na bude murfin driver na shiga, khaleed ya bude baya ya shiga, yace madam ya haka? Nace da akayi ya? Yace duk kin kwashe passengers din ni motata empty, nace toh ai dai passengers din ne suka zabi inda ya musu, nan ko sabuwar rigima ta kaure, salim yace toh wai wane kaudin ne yasa kuzo da mota biyu? Khaleed yace kasan halin mata so take tayi gasa dani, nace don't mind him salim ni bammasan daga inda yafito ba kowa hanyarsa daban, nidai mom tace nazo na daukeku, ai kuwa rigima muka dingayi har salim da aliyu suka fita motar suna dariya, salim yace danuwa idan muka biye wannan love birds din bazamuje gida da wuri ba, ni na lura basuda lokacin kowa sai kansu, yanzu dai ni bari naje motar broda kai ka zauna a ta sis mutafi, khaleed yayi kutsul yafito mota kai ka zauna anan din, Aliyu zo mu tafi a tawa, shidai yayi murmushi ya bishi, waigowa yayi yayimin gwalo akwai zancen da zamuyi tare ya sakaleshi a kafada suka tafi, naja motata muka wuce, ina gaba yana bina baya, bini-bini na kallesu ta mirror sai naga firarsu suketayi kuwa suna dariya, sabanin nida salim da bamuda abun cewa na lura ma bayason hayaniya da haka har muka isa gidansu khaleed, koda mukashiga duk anfito waje ana jiran isowarsu, sai murna akeyi bayan anzauna da minti goma mom tace su tashi su hau dining ga abincinsu chan.

Mikewa nayi nace aliyu tashi muje gida su mama na jira, mom tace kibari yaci abinci mana, nace mom su mama sunriga sungama shirin zuwansa, idan yaje baici komai ba bazasuji dadi ba, mom tace hakane kuma duk da haka saida tayi packaging wasu abubuwa tace sai mun tafi dasu, naja aliyu zamu tafi khaleed ya taso muje ni zankai danuwana gida, wata harara na masa ya basar waishi dagaske kishin aliyu yake? Haka muka tafi yaja aliyu motarsa suka barni nikadai ins binsu a baya har muka isa gida.

Khaleed dashi aka zauna dakin mama akayita fira da dariya, anan yaci abinci yayi komai, inason fira da danuwana ya hana, sai wuraren karfe goma mama tace mutashi mu tafi dare nayi, kuma taji dadi sosai ganinmu a haka, zargin da take ada duk ta daina yanzu ta yarda muna zaune lafiya. Mikewa nayi nace aliyu sai na shigo gobe akwai magana yace Allah ya kaimu muka fita, kowa ya shiga motarsa, kuma koda muka isa kowa part dinsa yayi kamar ba khaleed din dazu ba nace dan rainin hankali kamar nayi kuka dan haushi.

Da safe kuwa ina shiryawa na kama hanyar gida, mama harda fada na dako uban sammako, anya ko breakfast nayiwa mijina? Nace mata eh kuma shi yace nazo, anan gida nayi breakfast munata fira, sai karfe goma sha daya aliyu ya fito, nace danuwa ansha bacci, sai azo abamu tsaraba ya fito dasu arabian gowns masu kyau da jewelries ya siyowa kowa mukayits murna.

Nace danuwa nima inada gift kazo gida cikin motocina 3 ka zabi wadda tayimaka ya fara ihun murna, mama tayi sauri tace ba yanzu ba, sai ya kammala karatu tukunna zaidai iya zaba yanzu, aliyu yace bakomai ya amince tinda banan ma yake zaune ba yanzu.

Nan nafara yimasa zancen kudina, harda 5 million dinda khaleed ya bani lokacin da zaiyi aure, Aliyu yayita mamaki aure kuma sis? Nace alkawarin da ya daukane ya cika, amma karka damu sun rabu ma yanzu, aliyu yayi hamdala, nan muka fara shawaran meh za'ayi da kudin.
[9/15, 2:46 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [12/23, 2:23 PM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah abdul
1⃣8⃣5⃣ khaleed ne a zaune a office dinsa ya dafe kai hannun akan table, saeed yayi sallamah ya shigo, khaleed baimasan yayi ba, saida yazo ya tabashi firgigit ya motsa, ya bashi hannu suka gaisa da idonsa da sukayi ja, saeed ya zauna yace khaleed meh yake damunka ne wai? Yace bakomai friend bacci kawai na fara, ya shiryeshirye? Saeed yace kada kamaidani wani karamin yaro mana, ko wa ya kalleka yasan kana tattare da damuwa ji yanda kake rama, miye matsalarka ne? Mikewa yayi ya tashi na gayamaka bakomai fa, saeed yace just admit it ka kamu da soyayyar ameerah malam, kadaina tsayawa kana ba kanka wahala.

Khaleed ya dawo ya zauna, ya akayi kasan haka, saeed yace gashinan rubuce a fuskarka, toh ni abunda ban fahimta ba shine ai matarkace yanzu miye matsalar? Khaleed yace ni gani nake kamar bata sona niko bazanso na chusa kaina a gunta ba batareda ta shirya ba, kuma friend duk lokacin da nayi kusa da ita take nake ganin ta fara chanja yanayi, alamun tsorona takeji tin bayan abunda ya faru, kuma ni duk lokacin da nake tare da ita i can't help it wata sha'awarta nakeji so shiyasa nake nisanta kaina da ita, dan kwata-kwata banason na cutar da ita.

Saeed ya gyadakai amma ai kana cutuwa ko? Khaleed yace alot friend, i need my wife seriously saidai inaganin kamar she is not ready for me, but bazan iya boyewa ba na kamu da son ameerah, kuma kullum karuwa sonta yakeyi, saidai banason na cutar da ita ko kadan shiyasa nake nisantarta, but ina shan wahala friend ya share hawayen da suka zubo masa.

Saeed dai kallonsa yake abun gwanin tausayi da dariya, dafa kafadarsa yayi friend ameerah batada matsala, kai yakamata ka nuna mata kana sonta wannan shi zaisa ta saki jiki da kai, kai zaka koya mata sonka, khaleed yace friend baka ganin har yanzu bata manta da tsohon saurayinta ba?
Chapter 47 · 0% Book details