← Book details Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 12 OF 52

Sashe 12

Dream Girl Part 2 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Gabana na faduwa na daure na isa wurin motar khaleed, qwanqwasa masa nayi ya bude qofa, nace ga ruwa, har da zaiqi kar6a ya tuna yunwa yakeji mum bata barshi ko breakfast yayi ba ta sakoshi gaba lemon ya dauka da ruwa ya barni da tray da cup dina, kwalin lemon naga ya bude ya kafa kai, na juya zan shigewata a gida, kirana yayi saida naji qirjina ya buga, na juyo na dawo, so nike ki dauko wayarki ki kiramin saeed, tindazu nike kiranshi yaqi dagawa, cewa nayi ni bansaka wayar a charge ba, tsaki yayi toh wa yacemiki wayar batada charge a jikinta, anaso ne kawai ayi charge b4 use dan ayi saving battery life, anyway dauko wayar na saka battery na, na kirashi, juyawa nayi naje daki na dakko balackberry na fito na miqamishi, tsaki yayi i phone zaki dauko malama, kuma ina simcard din ko dameh zankira? Komawa na qarayi cikin gida na dauko i phone din da simcard, na fitoh again, na miqamishi, sai yanzu ya fiddota cikin kwali na lura iri dayane da tashi har color, simcard naga ya 6alle ya saka sannan ya cire battery Yasa nashi, number saeed naga ya danna yasa call, sai ya tuna ba kudi a layin tsaki ya sakeyi, ba masu saida kati a kusa ne? Nace akwai a chan layin yace toh shigo mutafi ki nunamin, nashiga motar mukaje wurin siyen katin amma kuma maj katin bai fito ba, hanya kawai naga ya miqe bai tsaya ko'ina ba sai near by bank, fita yayi yaje wurin atm, naga ya fitoda sim pack dina yana dubawa yana latsa atm machine, yagama ya dawo mota call naga yasa, tafara ringing ya miqomin wayar, muryar saeed naji yana hello, nace ranka ya dade yace da wa nike magana? Sabuwar budurwarka ce da kaba number a jiya, dariya yayi haba Gimbiya ameerah ai ko a bacci na tashi zanganen muryar nan taki mai sanyi, dariya nayi nace ya aunty fareedah yace gatanan kan jikina, murmushi nayi nace toh ka gaida ita, khaleed ne yace malama toh bafa kiransa nayi ba dan kuyi fira, kar6e wayar yayi, saeed ina gidansu ameerah kazo ka sameni zamu gaida mama, kan ya bashi amsa ya miqomin wayar, nace hello saeed yace ameerah kice masa ba inda zani, nace haba yaya saeed ai wannan ni zakayiwa wulaqanci, shiru yayi sannan yace toh shikenan gani zuwa, amma wlh dan ke kawai zanzo nace na gode yaya saeed na kashe wayar.
[9/14, 1:09 PM] ‪+234 706 332 8523‬: [11/19, 7:03 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
5⃣5⃣ nace mama zanje gidansu saudah tace adawo lfy, nace mama ba kince ba zani ba? Tace yanzu kuma nace kitafi ba, ai dama rashin fahimta ne ko kinga laifina? Nace a'ah wlh mama dama duk uwa ta gari dole tayi binceki akan duk abunda taga yaranta suna shigowa dashi a gida, a ina yafito? Wa ya basu da kuma dalilin da yasa aka basun, kar son abun duniya ya rufe mata ido ko dan tanaganin basudashi, har tayi silar lalacewar tarbiyar 'ya' yanta, kuma mama ni nasan wannan zamani samari en qarya masu amfani da kudi su lalata yaran mutane su sukafi yawa, amma ni mama Allah ki yarda dani ba wani abun duniya da zaisa na zubarmiki da mutunci, tace ai shikenan na yarda dake ameerah dama tsoro ne naji kuma duk uwa ta gari dole taji tsoron faruwar wani abu gun 'ya' yanta, kuma na lura ma yaron yanada nutsuwa ba maison hayaniya bane, Allah dai yasa shine za6i mafi alkhairi a wurinki, ya daidaita tsakaninku yasa kuma alkhairi a aurenku, yasanya aure ne za'ayi na har abada, da qarfi nace Amin mama Allah ya barmin ke na rungumeta, tureni tayi ni sakeni marar kunya karki kadani, a raina nace mama bakisan yanda wannan addu'ar taki takeda muhimmanci a wurina ba dole na kar6a da qarfi.
Nace mama ki bawa suhaila kudi ta siyo extension wire da kika fasa jiya ayi chargen wayoyin chan, tayi dariya hakafa kinsan innayi fushi ba sauqi nace ai kuwa yanzu biya ya biyo gyartai mama, dariya mukayi ta qwallawa suhaila kira ta fito ta bata kudin haka yayi daidai da shigowar saudah nace er halak yanzu zanje gidanku sai gaki kinshigo, tace ba wani nan ai bakida kirki kekan nace tambayi mama kiji Allah da gaske nake, mama tace ba ruwana tsakaninku ta shigewarta daki, nima naja saudah muka wuce dakina.
[11/19, 7:26 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
5⃣6⃣ saudah tayi tsaye tana qarewa dakina kallo yau kuma sabon gyara akayi ameerah? Nace eh tace wannan kwalayen fa ko biki za'ayi a gidan shine baki gayamin ba? Daga mata kai nayi alamar eh, zama tayi a katifa ta jawoni na fado qasa, na kaimata duka so kike kimin illah ayi biki amarya a nakashe? Kallona take da alamar tambaya qarara a fuskarta, ke nifa bangane meh kike nufi ba, bikinwa za'ayi ne nace na qawarki mana, wace qawar kike nufi? Nace wace qawar kikeda a gidannan? Tace ke nifa kin dagulamin lissafi, nace aurena za'ayi nan da wata daya inshaAllah, tace da waye kuma? Nace da khaleed dina mana, khaleed kuma? Wani khaleed din kika samu ne? Nace khaleed dina dai da kika sani my dream man, tace qawas kinsakani a duhu a iya sanina khaleed kince da wadda yakeso, toh taya akayi zakuyi aure yanzu? Ko kuma kina gayamasa kina sonsa ya haqura da salmar zai aureki? Dariya nayi nace relax mana qawata abunnan fa ba na tashin sense bane, aure nacemiki zamuyi ba wani mugun abu ba, toh dan Allah malama kiyimin bayani i'm curious naji yanda haka ta faru, dariya nayi mai isata, sannan na kwashe duk plan dinda na shirya na gayamata, sake baki da ido tayi tana kallona saida na girgizata, tace ashe ameerah bakida hankali? A ina kika ta6ajin anyi haka? Ni ko a films ma banta6a jin anyi haka ba, yanzu kawai sai ki aure mutum dan kawai ki cika burin shi na auren wadda yakeso, nan da shekara daya sai ya sakoki shikenan ke burinki ya cika kenan? Nace saudah ba abunda zai faru inshaAllah, ai Allah yaga zuciyata shi zai taimakeni, saudah tace ameerah dis is total madness meh kika shirya yi nan gaba? Kinga ni badani za'ayi wannan haukar ba, yanzu zan samu mama nayimata bayani ta miqe ta nufi dakin mama.
[11/19, 10:23 AM] Deejah Abdul💗💖: Dream girl na deejah Abdul
5⃣7⃣ da saurina na fita na jawota wlh saudah idan har kika gayawa mama abunda ke faruwa, we are done, karki sake ki qara kirana qawarki, na koma daki, biyoni tayi jiki a sa6ule, ameerah yanzu inaji ina gani zanbarki ki lalata rayuwarki a banza a wofi sanadin soyayya? Nace indai ke qawata ce da gaske ki tayani addu'a kawai, now its too late to cry saboda munriga munsaka iyayenmu a ciki there is no going back, haka yayi daidai da shigowar suhaila ta bani extension wire din da wayoyi naje na sakasu charge, itadai saudah kallona kawai take, wannan kuma fa? Nace maman khaleed ce ta siyomin su jiya, wannan ne nawa wannan ta mama, wannan ta aliyu, kayannan ma da kike gani duk ita ta kawosu dazu da tazo, jinjina kai saudah tayi ashe abun ya girmah kuwa, Allah ya kyauta, nidai fatana kar kiyi danasanin abunda kika shirya nan gaba, nace inshaAllah bazanyi ba indai har kuna tayani addu'a, katina ta fiddo a jaka ta jefomin sai ki tashi muje rabon katinan tin shekaranjiya aka kawo, dubawa nayi nace toh tashi muje, na saka hijabina mukayi dakin mama, nace mama zamuje rabon katin saudah tace adawo lfy, nace mama ki riqa lura nasaka chargen wayoyi a daki kar khairi ya shiga ya lalata tace shikenan adawo lfy.
Khaleed kuwa direct office ya wuce amma still yakasa yin komai, wayarsa ya dauko ya kira salmah, saida ya kira kusan sau uku a na hudun sannan ta dauka, hello babyna yace haba baby haba tin yaushe niketa kiranki amma kikaqi dagawa har txt messages dina ba wanda kikayi reply, i'm really sorry my baby aikine ya mini yawa kasan aski idan yazo gaban goshi yafi zafi, daz y kwata-kwata banida sukuni, amma nima kewarka tana damuna, yace to atleast baby ki riqa replying msgs dina mana, tace ok zanyi qoqari duk ma meh ya rage nadawo gabadaya na zama taka wani farinciki ya ziyarci zuciyar khaleed sai wani washe baki yake, kai ba kace khaleed din ameerah bane da baya ko smile, cemasa tayi ok i have to go baby inada lectures now talk to u later batama jira abunda zaice ba ta kashe wayar, tabar khaleed riqe da waya yana kallo yanata murmushi.

Abunda khaleed bai saniba shine salmah ta qare karatu tin last year tayi zamanta tana aiki, iyayenta sunyi-sunyi ta dawo taqi, dan ita salmah kwata-kwata aure baya gabanta, rayuwar duniya ta sawa gaba kawai.
Chapter 12 · 0% Book details