← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 95 OF 108

Sashe 95

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Yana shiga da'kin da ruwan gishirin a hannunsa Hajja ta kar'ba a hankali ta dinga dandala mata a bakinta tana tsotsewa sai da tayi mata sau uku sannan ta mike tana kokarin sata a kafad'a, Rashida tace"Hajja koma ki zauna kawo in dan zagaya da ita."
Hajja ta zauna tana fad'in " A kafad'a zaki sanyata insha Allah yanzu za tayi gyatsa." Rashida ta kar'bi babyn tasa a kafada ta shiga zagaye da ita a dakin.....Cikin ikon Allah kuwa ta daina kukan da takeyi ta shiga sauke ajiyar zuciya tana sakin gyatsa.
Hajja tace"Alhamdullhi yanzu zakaga tayi bacci."
Yace."Ai gwara tayi baccin Hajja yarinya kankanuwa cikinta yay irin wannan kumburin wanda ko a gurin babba ma zaiji jiki ballanta yaro karami irinta."
Hajja tace"Mafi akasari dama 'kananun yara kamarta sunayin irin wannan kumewar cikin, sai hankali suke dainawa wasu kuwa sai suyi kwana da kwanaki ma basuyi bayan gari ba." Yace."Idan hakane kuwa al'amarin akwai ban tausayi wallahi." Hajja tayi murmushi tare da gyara kwanciya tana fad'in " to nidai sai da safe jama'a ina baccina tsohuwa ta tasheni dan dai kawai sunan kishiyata ne da ita shiyasa na saurareta da badan taci darajar sunan Yafindo ba to da sai dai ta nemi wanda zai rarrasheta."
Rashida tace"Kai Hajja ai yanzu ma bake kika rarrasheta ba Momynra ce."
Hajja na hamma tace"Haka kika ce ko."? Rashida na dariya tace"Ai gaskiya na fada Hajja gani ina rarrashinta har tayi bacci kice kece kika rarrasheta."
Hajja tace"Shikkenan dan dai ba'a fatan cuta ne da sai nace gobe ma rana ce."
Rashida tasa dariya tana dan bubbuga bayan baby zahran wacce ke lumshe ido bacci na fuzgarta.....A hankali yace."Kawota nan Rashida kema kije ki kwanta an tasheku kuna bacci ko."
Cike da jin nauyi ta mika masa yarinyar tace"Haba babu komai Wallahi kaga ma bacci zatayi." Ya kar'be ta tare da rungumeta a jikinsa, yace."Ki dinga yiwa yayarki fad'a har yanzu ta'ki hankali." Kanta ta sunkuyar tana d'an murmushi, ya kama hanya ya fita daga dakin rungume da yarinyarsa a jikinsa.
Tana kwance a gado tana tunanin rayuwa ya tura kofar dakin ya shigo, rufe idanunta tayi taki yin kwakkwaran motsi mugun haushinsa takeji dan duk wani girma da 'kimarsa da take gani ada yanzu sun zube a idonta.
A hankali ya kwantar da babyn a gadonta, ya dan tsaya a kan yarinyar minti biyar ya tofe mata jikinta da addua kana ya juya da niyyar fita daga dakin.
Ja yay ya tsaya yana tunani, sai kuma ya bud'e kofar dakin ya fita, tana jin fitarsa ta bude idanunta ta mike zaune tana jan tsaki! Yarinyar ta dauko ta dawo da ita kusa da ita ta kwanta tare da rufe jikinta da bargo, bacci har ya soma daukarta taji an bude dakin an shigo shine dai ya kara shigowa, dake ta kashe fitilar dakin sai ya kunna wayarsa yana duba gadon babyn, wayam babu ita, da sauri ya kalli bed din ya gansu a lullebe! a jiyar zuciya ya sauke, ya kashe wayarsa ya aje saman bedside ya zare jallabiyar jikinsa dake akwai singlet a jikinsa da gajeran wando sai kawai ya shiga cikin bargon nasu yay kwanta rigingine fuskarsa na kallon rufin dakin, ya dora hannuwansa a kirjinsa, yana addua, sai da ya gama tukkuna ya tofe musu jikinsu gabad'aya kana ya rufe idanunsa, Wasila gabanta tun yana fad'uwa har ya daina fad'uwa ganin tunda ya kwanta baiyi kuskuran koda rik'e d'an yatsanta ballanta yay mata wani abun asali ma ya bada tazara mai yawa a tsakaninsa da ita sanda tayi dubarar juyawa ta

fahimci hakan......Al'amarin yay masifar 'bata mata rai! da kyar ta samu bacci ya dauketa, saboda tsabar damuwa da 'bacin ran da take ciki.

Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*'Yr Bngr Sys
*78*

_*Sa'ko na mussaman zuwa gareka Amadu 'kawayen Wasila irin su Mumy Farhan, Bomis Zainab kankara Mrs Aliyu Nafisa Buhari Hauwa Chindo, Sakina Ummee da dai sauransu, sunce kayi hakuri dan Allah karkayiwa Wasila kishiya kayi mata uziri saboda yarinya ce, idan kuma ka kuskura ka 'kara aure to zaka gane baka da wayo dan duk wacce zaka aura ba zata kama 'kafar Wasila ba, zaka dawo inda kake salati kana kiran sunan Allah😅🤭 babu ruwana Sistar Sakina ce tafad'a🕺🕺 sannan Sistar Jamila tace duk wacce zaka aura sunanta salamatu salam dan ba zata iya da jarabarka ba🕺 babu ruwana! Jamila da Ummee ne suka fad'a ni dai 'yar aike ce......Momyna tace kayi auranka dan ba Wasila ce kadai mace ba, takwara Fatima Yakubu ma haka tafad'a Sai sistar Hadiza Shall itama haka tace ka more rayuwarka, Shafa'a S Yari da Bilba sunce kayi aure ka more rayuwarka💃🏼🔥 ni dai na isar da sa'kona Amadu sai ka yanke shawarar da zata fishe ka, nima nace ba Wasila ce kad'ai autar mat.......🙊😌*_

Cikin sanyin jiki suka koma cikin gidan Hajja ta gansu duk babu kuzari a tare dasu tace"Ai kam ni kaina naso su zauna su danyi kwana biyu ku samu sakewa da mahaifiyarku amma ace daga zuwa sai su tafi wallahi banji dadin hakan ba sai kace wad'anda ake kora."
Rashida ta goge hawaye tace"Nima naso su zauna wallahi yanzu anti Wasila yaushe zamuje to." Wasila ta kalleta ranta duk babu dad'i tace."Sai an d'an kwana biyu baby tayi 'kwari zamuje insha Allahu." Hajja tace"Kwarai kuwa hakan yana da kyau, Allah ya kaimu ya bamu lafiya mai amfani." Duk suka amsa da "ameen."

To har dai kusan goma da wajan rabi bai shigo gidan ba Hajja na kokarin shiga daki ta kwanta ya shigo da sallama a bakinsa......Dukaninsu suka amsa suna masa sannu da zuwa.
Ya kalli Hajja yace."Ashe baki kwanta ba hajja ko kema kallon kike."? Tace"Oh!oh kai nake ta jira ka dawo ai." Yace."To Allah yasa lafiya."Ganin yana 'kokarin zama ya sanya ta mi'ke a hankali ta bar gurin, Rashida ma ganin 'yar uwarta ta tashi sai itama tayi yun'kurin mi'kewa yace."Rashida koma kiyi zamanki ya kina kallo zaki tashi kuma."
Cike da kunya da jin nauyi ta koma ta zauna ta maida hankalinta kan tv.....Hajja tace" Dazu munyi ba'ki a gidanan na sanya Wasila tayi kiranka a waya kazo ku gaisa duk da nasan da cewar kasan da zuwan nasu, bai kamata ace suzo har su tafi baka zo kun gaisa da juna ba."
Ya d'an dafe kansa yana girgixa kai ya kai minti uku a haka kafin ya d'ago kansa yana kallon Hajjan yace."Wallahi Hajja na manta shaf! ni da kaina na sanya Garba yaje ya daukosu amma kuma banyi tsammanin yau zasu koma ba shiyasa kwata kwata ban mai da hankalina gurin dawowa gida da wuri ba.''
Hajja tace"Aikuwa ko awanni uku basu cika ba suka tafi dan babu yanda banyi dasu su zauna su kwana biyu ba suka ki."
Yace."Ashsha! nima ban so hakan ba naso mu gaisa dasu wallahi amma babu damuwa Insha Allahu zamu shirya muje idan momy tayi kwari."
Hajja tace"To yawwa yanzu naji kayi magana dan haka naji ita Wasilan ma ta fad'a to dan Allah ka mai da hankali kada ka shiririce ka kai yaran nan su kwana biyu tare da mahaifiyarsu."
Yace."Insha Allah Hajja." Mikewa yay yace."Bari na shiga nayi wanka." Hajja tace"To sai da safe dan nima shiga zanyi na kwanta."
Yace."Hajja Allah ya tashemu lafiya." Hajja ta mike ta nufi daki shima ya nufi dakinsa. suka var Rashida ita kadai tana kallo.
Wanka yay ya fito yana mamakin zuwan bakin da kuma tafiyarsu a gaggauce baiji dad'i ba gaskiya sai kace wad'anda ake kora ai sa bari su kwana tukkuna sai su koma gida, zuciyarsa ta shiga wasi-wasi kan Wasila yana tunanin kamar itace za tace su tafi tunda gashi tana fad'awa Hajja zasuje idan ankwana to kuwa idan hakane nufinta babu inda za taje duk wanda ke son ganinta daga can garin sai da yazo koda kuwa mahaifiyarta ce yana da inda zai sauketa, amma b
Chapter 95 · 0% Book details