← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 74 OF 108

Sashe 74

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rashida kam na daki na rarrashin Wasila suci abinci ta'ki hawaye kawai take! tarasa abinda yake damunta, mai allo ya d'aga labulen dakin yana fad'in "Ina Wasila."? Da sauri ta goge hawayen ta tace" Gani Kawu, Yace."Kiyi hakuri kinji ko kiyi hakuri ki kyautata hakuri a karo na biyu na umarce ki da kiyi biyayya kibi abinda nace miki insha Allah zaki samu alkairi a gaba, bani na fad'a ba Allah ne ya hukunta hakan! duk macen da mijinta ya saketa saki d'aya kafin ta 'kare iddah mijinta ya dawo yace ya janye sakin ma'ana ya mayar da ita ko bata so dole ta koma ta cigaba da zama dashi a matsayin mijinta, dan haka nake sake baki hakuri nake kuma ro'konki da kibi mijinki ki koma d'akin ki insha Allahu za kiji dad'i kuma kiyi alfahari anan gaba." Mai allo ya gama kashe mata jikinta da maganganunsa shiru tayi tana tsiyayar da hawaye mai allo ya saki labulen dakin zai tafi tace"Kawu ina da magana." Ya dawo da baya yana kallonta......Tace"Kafin na koma to ina so muje can pataskum gurin Uwani kaga tunda muka zo ba muje saboda yanayin rashin lafiyana ba kuma musan halin da take ciki ba."

Mai allo yayi shiru yana nazarin maganarta ta Yace.''To babu laifi sai kuje domun ki shaida mata abinda yake faruwa, yana da kyau a fita hakkinta a matsayinta na mahaifiyarki tasan halin da ake ciki, bari na sanar da Alhajin abinda ke faruwa." Labulen dakin ya saki ya nufi inda suke zaune Sun gama cin abinc

i suna hira mutumin ya saki jikinsa sosai dan har ya kira Khalifa a waya ya shaida masa abinda ke faruwa.....Mai allo ya dan jingina jikin bango a nutse yace."Anya Alhaji tafiyar nan zata yiwu yau kuwa."? Yayi saurin kallonshi yana so yaji dalilin da zai hana yiwuwar tafiyar......Mai allo yace."Yarinyar nan na bukatar ganawa da mahaifiyarta hakan nada kyau sosai mahaifiyarta tasan halin da ake ciki ta kuma sanya mata albarka, a zamantakewar auranta, dan haka nace ko zamu bari rana ita yau! insha Allah sai kadawo ka d'aukesu kafin sannan sunje sun dawo ta sake nutsuwa tukkuna.

'Dan 'bata fuska yayi yace."A'a malam ina ganin rana d'aya ma zamu iya zuwa mu dawo
Ba tare da anja dogon lokaci ba, ni da kaina zan kai su su dubata insha Allah gobe zamu dawo tare da khalifa sai su shirya muje daga can sai mu wuce kawai.'' Mai allo yace."Babu laifi hakan Allah ya kaimu lafiya." Hajjah tace "Amin amin ya rabbi mungode malam Ubangiji Allah ya kara girma da dattako." Mai allo yace."Babu komai hajiya mudai fatan anan shine Allah yasa anyi kenan Allah ya d'orar da zaman lafiya."

Ya d'an gyara zamanshi as'usel kamar ko da yaushe dai ya ciro kudi masu yawa a jikinshi ya dora saman buzun mai allo yace."Malam zamu koma Allah ya saka da alkairi." mai allo yace."Alhaji Ahmadu baka gajiya kullum cikin hidima kudin nan sunyi yawa." Yace."Babu komai malam Allah ya bamu mu bayar meye amfaninsu in ba'a badasu ba." Mai allo yace." To maddalah mungode kwarai Allah ya kara arziki da wadata." Ya amsa da "ameen." yana gyara babbar rigarshi.

Hajja ta le'ka d'akin su Wasila tana gyara lullu'binta tace"To Ina kuke zamu tafi Wasila kina ina.''? Wasila dake kwance kan kafita ta fara kokarin mikewa zaune Hajja ta shiga dakin tana fad'in "A'a yi kwanciyarki kinji ko sannu! Dan Allah kiyi hakuri karki sa damuwa cikin ranki insha Allahu abinda ya faru a baya bazai faru ba yanzu ki kwantar da hankalinki ki daina damuwa kuma ki daina kuka." Kanta a kasa tace"Insha Allah Hajja nagode ki gaida gida." Tace"Gida zaiji insha Allahu gobe inanan ina jiran zuwanku." Shiru tayi tana mayar da 'kwallar dake kokarin zubo mata......Hajja ta fito daga d'akin kawai sai ta ganshi ya 'kurawa kofar dakin ido kamar zai shiga, kai kana kallonsa kasan a dame yake daurewa kawai yake yana kokarin dauke abin daga ranshi duk dan kar girmanshi ya zube a idon yarinyar da mutanan gida.....Hajja tace"To ko zakuyi sallama ne naga kanata kallon dakin....Girgiza kanshi yace "Tunda kunyi sallama babu damuwa ai gobe zamu had'u insha Allah." Tace"To babu lefi." Bitan ce ta fito daga daki hannunta rike da wata roba mai murfi mai kamar kwanon sha robar da fulani ke zuba nono a ciki, daya hannun nata kuma ledar fura ce a cure tace"Hajjah ga wannan babu yawa, tun zuwanku naso in dama muku ayyuka sunyi yawa." Hajja ta kar'ba da walwala a tare da ita tace"To godiya muke Bitan Ubangiji Allah ya saka da alkairi kwarai naji dadin yanda kika kar'bemu hannun biyu mungode sosai." Bitan tayi murmushi kawai tana fad'in "Babu komai hajiya mune da godiya ai ku gaishe da gida Allah sauke ku lafiya." Hajja ta amsa da ameen kana tabi bayan Ahmadu da ya riga yayi gaba." Suna tsaye da mai allo suna sallama, Garba dake zaune cikin mota ya fito suka gaisa da mai allon kana ya koma ya jingina jikin motar yana ganin tawowarshi ya hude mishi mota ya shiga Hajja ma shiga ta zauna da sauri ya zauna a maxauninshi , Ahmadu ya shiga dagawa mai allo shima yana daga mishi hannu gami da yi musu fatan sauka lafiya.

Bitan ta le'ka dakin nasu sai ta tarda rashida ita kadai a zaune Wasila tayi bacci Tace"Au bacci tayi kenan."? Rashida tace"Eh tun dazu nayi nayi taci abinci ta'ki ci." Bitan tace"Kyaleta na fad'a miki tana tashi daga wannan bacci xata nemi abinci da kanta." Rashida tayi dariya tana fad'in "Aikuwa yanzu ma kawai dan tana cikin 'bacin rai ne amma anti Wasila da abinci ba dama." Bitan tasa dariya tare da fitowa daga dakin.

Aikuwa hakane ya kasance da wata masifaffiyar yunwa ta tashi da kyar taje ta wanke bakinta ta nufi kicin Bitan tace"A'a kar ki fara da abinci d'azu malam yace." Kafin kici komai kisha wann

an rubutun." Dakin bitan din ta nufa ta kar'bi rubutun ta tsuguna da bisimillah a bakinta tasha ragowar ta shafe cikinta dashi kamar yanda ta saba.....Bitan ta mike da kanta taje ta dauko mata abincin ta gyara zama sosai zauna kana tayi bisimillah ta fara cin abincin........ Sai bayan da ta kammala cin abincin ne tace "Bitan ina Rashida."? Tace" Bata jima da tafiya gidan Innar ku ba, malam yace taje ta fad'a mata abinda ke faruwa.

Ta sunkuyar da kanta kasa a hankali tace"Yanzu Bitan sai na koma gidan mutumin nan."? Bitan tace"To ya zakiyi Wasila shine alkairi don Allah kiyi hakuri ki daina wasiwasi insha Allahu babu wani abunda zai sake biyowa baya kuma insha Allahu zaki haihu lafiya." Shiru tayi tana tunanin shin idan ta koma gidan ko wane irin zama zasuyi dashi, ita yanzu ta daina jin sonsa a ranta, kawai zata koma ne ta zauna tare dashi saboda an rinjayeta.

Bayan magariba da mai allo ya shigo ya sake tabbatar mata da maganar ya kuma umarcesu da su had'a kayansu su kuma shirya da wuri don kar yazo yana jiransu.........mai allo kwana yayi yana karatun al'kurani mai girma sai da ya had'a izifi sittin kana ya tofa cikin tsabtattaccen ruwan sama, ya samu jarka mai kyau ya zuba ya rufe da murfinta ya aje a guri guda, kana ya mike a nutse ya fito ya d'aura alwala ya wuce massalaci.
Karfe tara shaura na safe sun shirya duk suna zaune a tsakar gidan har da Inna Hajara data dako sammako tazo gidan, ita da mai allo sun tasa Wasila a gaba sai fada suke mata mai tafe da nasiha irin fadan da iyaye kan yiwa 'yayansu a lokacin da za'a kaisu dakin mazajensu, Gatan da bata samu ba a farko, sosai take share hawaye tana jin wani iri a jikinta tabbas duk wanda yayi rashi iyaye nagari yayi babbar asara, Ada babu mai nuna mata ga yanda za tayi itace ke zartar da hukunci kan mahaifiyarta da 'yar uwarta dan sai abinda tace sannan Uwani da Rashida keyi, shiyasa takejin wani irin a jikinta, gaskiya babu abinda za tacewa mai allo da Hajara da ita kanta Bitan din dan sun nuna mata kauna da so da kulawa, duk mutumin zai fad'a gaskiya yayi maka fad'a kan wani kuskure naka to babu shakka masoyinka, dan haka sai ta dauki aniyar zama lafiya gidan Ahamdu kamar yanda suke bukata ta kuma yi musu alkawari kan insha Allah za tayi mishi biyayya iya iyawarta."albarka suka shiga sanya mata suna cike da farin ciki mara misaltuwa

Wannan karon cikin babbar mota (Sieana) sukaje garin wacce ke dauke da kayan abinci dana masarufi, Ahmadu yayi niyar farantawa mai allo kamar yanda shima ya faranta mishi saboda ya fahimci tsayuwar shi kan Wasilan da abinda ke cikinta yasan bashi da abinda zai biyashi a bisa abinda yayi mishi, sai dai hausawa nacewa yaba kyauta tukwici.....Almajirin malam ne ya hangi zuwansu lokacin da yake kokarin shiga gidan malam din, dan haka koda ya shiga gidan sai yake shaidawa malam din zuwansu, Wasila taji gabanta ya fadi har sai da ta rasa miyau a bakinta, tayi shiru tana kokarin maida kwalla ita har ta gaji da zubda hawaye..........Mai allo ya shigo dasu, cikin gidan yana musu barka da zuwa, Garba da Hadi sune suka shiga shigo da kayan abincin cikin gidan malam ya cika da mamaki yana so yayi magana Khalifa yayi saurin tareshi da fadin malam kada kace komai don Allah ba wai munyi hakan bane domin mu biyaka mun san bamu da abinda zamu biya dashi wannan ihisani ne kawai mukayi maka saboda karamcinka." Mai allo ya girgixa kanshi yana fadin anya abun baiyi yawa ba kuwa? Khalifa yace."Beyi yawa ba malam ka sanya albarka kawai." Yace."To nagode kwarai Allah ya sanya alkairi ya kara arziki da wadata." Khalifa ya amsa da ameen ya rabbi."
Inna Hajara kuwa mamaki take sosai ita bata ta'ba 'karewa mijin Wasilan kallo ba sai yau! sai take ganin kamar ma yafi karfin wasilan dama haka Allah ke tsara lamarinshi Addua ta shigayi kan Allah ya xaunar da ita lafiya a dakinta.
Chapter 74 · 0% Book details