← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 92 OF 108

Sashe 92

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Wasila kuwa jin zuciyarta take wasai tunda ta samu ta fad'i abinda ke cikin ranta shikkenan itama ta dauki al'kwarin akan ba zata sake zama ya dinga raina ta ba ballanta har ya dinga d'aga wayar 'yan matansa a gabanta sai ta nuna masa itama macace wacce tasan abinda takeyi.

A shirye ya fito da shirin fita, ya tsaya suna magana da Hajja, Hajja tace"Nima fa na kusa tafiya tunda dai Allah yasa ta haihu lafiya shikkenan zan koma gida." Yace."Kiyi hakuri kiyi zamanki tare damu." Tace"A'a dai gwara na kuma gidana bana dinga zama cikin yara ba." Yace."Hajja ai zaman naki cikin Yara gyara kike ba 'barna ba." Wasila da kanta yake sunkuye tayi saurin dago kanta tana kallonsa, sai taga kamar magana yake fad'a mata kan Inna Hajara oh! wannan mutum baya barin takwana! wato Yana nufin Inna Hajara itake aikata 'barna kenan......Mi'kewa tayi ta bar musu gurin ba tare da tayi kuskuran kallonshi ba, Hajja ce ta bita da kallo sosai ta fuskanci akwai matsala a tsakaninsu amma kuma ba za tayi masu magana ba sai ranar da zata tafi tukkuna idan kuma sun dai-daita kansu shikkenan.

Yana fita Garba ya daukeshi a mota kafin ya ajeshi cikin ma'aikatarshi yake Umartarshi da cewar idan ya saukeshi ya nufi can garin su Uwani Patskum yaje ya sanar musu da cewar Wasilan ta haihu idan da me ra'ayi zuwa yaga abinda ta haifa sai ya dauko shi yazo dashi.....Hakan ce ta kasance Garba na saukeshi sai ya dauki hanya kamar yanda ya umarceshi.

Suna zaune a palo bayan azahar dan uku ma ta kusa Rashida ma ta dawo daga makaranta, kawai sai sukaji sallamarsu su Uwani da Kuluwa dasu Inna Tabawa........Rashida ta mi'ke a guje taje ta bude musu kofar falon suka shigo ciki....Wasila ta mi'ke tsaye fuskarta cike da! walwala da farin ciki mara misaltuwa, Tabawa Iya mai waina da Uwani suka nemi guri suka zazzauna a nutse ita kuwa Kuluwa sai kalle kalle take tana ya'ke dafaffun ha'koranta da kyar ta zauna kan kujerar tana wani irin abu irin na marasa gaskiya......Hajja ta dinga fadin "Sannuku da zuwa kai masha Allah sannuku Wallahi ko jiya sai da mukayi zancenku ashe kuna tafe." Inna Tabawa tace"Aikuwa dai munata sa rana sai yau Allah ya nufa yau din ma Ai maigidan nan ne ya tura a ka dauko mu.....Kuluwa tayi saurin kar'be maganar tace"Wallahi kuwa ai rashin kud'in mota duk shine yayi mana cikas da tuni munzo anyi hidimar suna damu ace yarinya ta haihu babu danginta ai da kunya gashi duk muna raye a duniyar."
Wasila taji kamar ta kwada mata mari jin abinda take fad'a shashashar mace kawai daga zuwanta har ta soma sakin layi....Ita kuwa Hajja murmushi tayi kawai ta mi'ke tana kallon Rashida tace"Kije ki kawo musu abinci tunda Rabe ya fita.'' Rashida ta mi'ke ta nufi kicin cike da takaicin Kuluwa da haukanta.

Kuluwa sai washe baki take tana kallon baby zahra dake hannunta tace"Yarinyar tubarakallah kyakykyawa gata da jikin girma kamar tayi wata uku kai masha Allah." Uwani ta kalleta tana dan jan tsaki cikin ranta, shiyasa fa taki amincewa da zuwansu tuntuni saboda hauka da rashin kamun kai irin na kuluwan

Inna Tabawa ta kar'bi yar tana sanya mata albarka kana ta mi'kawa 'Yar uwarta iya mai wani itama ta sanya mata albarka ta mi'kawa Uwani, kunya ta hana ta 'karbar yarinyar sai dai tace"Allah ya rayata tafarkin addinin musulunci." Ganin ta kasa kar'bar yarinyar yasa Kuluwa dashare baki tace"Uwani kunya ki keji ne ai dole jikar 'yar fari hahahahaha." ta karashe maganar tana dariya kamar sabuwa

r mahaukaciya sai wani mutsu mutsu takeyi......Uwani girgiza kanta tayi tayi mata banza ba tace mata komai ba haka su Inna Tabawa dama suma haushinta sukeji.........Koda Rashida ta jere musu abinci kan daining Kuluwa kasa zama tayi kan kujerar sai kauyanci takeyi duk ta hargitsa musu guri.....Wasila tace"Rashida ki kwashe abincin daga dainnig din ki shirya musu shi kan daddumar can ta gefe sai sunfi jin dadin hakan."
Da sauri Kuluwa tace"Aikam dan gaskiya zama kan wannan abun ba zaiyi dadin cin abinci ba gwara mutum ya zauna a 'kas yanda abincin zaifi tsirga masa.

Cike da takaicinta tace"Dan Allah Kuluwa ki nutsu mana bafa a aljanna kike ba da kike ta wannan rawar jikin haba! ki daina haka dan Allah idan ba haka ba to ni kada ki sake zuwar min gida dan ba zaki zo ki bani kunya ba.'' Kuluwa ta hau ya'ke cike da kunya tace"Yi hakuri 'yar nan al'amarin ya rud'ar dani wallahi ban ta'ba shiga irin wannan daular ba sai yau gaskiya ke d'in 'yar baiwa ce Allah ya samu a danshin ku."
Tsaki kawai Wasila tayi ta bar gurin, Uwani tace"Kuluwa kafin muzo gidan nan fa sai da mukayi magana dake wai me yasa kike hakane kada da mai gidan nan ya shigo ki bamu kunya a gabansa."
Kuluwa tace"Kai jama'a wai ya kuke so nayi ne? to shikkenan bari nayi gum! da bakina na daina sanya albarka tunda dai itace bakwa so nasa." Rashida tace''Hakan shine yafi alkairi dake." Kuluwa taja bakinta tayi shuru sai dai muzurai kawai takeyi tana gyara zamanta, haka suka ci abinci mai cike da nama da lemuka masu sanyi

Bayan sun gama cin abincin Hajja ta fito daga daki tana kallon Wasila tace"Yana da kyau ki kira mai gidan a waya yazo su gaisa tunda naji kamar suna cewa yau zasu koma." Ai kafi ma Wasilan tace wani abu Kuluwa tace"A'a ba yau zamu koma ba sai mun kwana biyu tukkuna dan haka malam yace mu zauna mu yauta tukkuna." Hajja tace"A'a to masha Allah hakan ma yayi kyau ai babu damuwa." Ita kanta Hajja ta fahimci matar kamar bata da hankali.
Wasila jikinta yay sanyi ganin abin na Kuluwa naso ya wuce gona da iri babu shakka baza ta so zamansu a cikin gidan ba ba dan komai ba sai dan kada su zauna Kuluwa ta zubar musu da d'an sauran mutuncinsu da suke dashi a idon maigidan dama hakan ma ya aka kaya yana musu wani irin kallo to ballanta kuma yazo yaga irin haukan da Kuluwa takeyi ai raini ne zai sake shiga tsakaninsu......Ke'bewa sukayi da mahaifiyarta Tace"Uwani gaskiya gwara ku tafi ni bana so ku zauna a gidannan saboda waccan matar mara hankali kawai idan Kunyi sallah sai ku tafi."

Uwani tace"Rabu da shashasha, ai dama mu ba zama zamuyi ba sai kace wasu marasa hankali yau din nan zamu koma tunda Allah yasa mun ganki lafiya da yarinyarki ai anyi barka ita idan zata zauna sai ta nemi guri kwad'ayayyar banza kawai."
Wasila tace"Ai naga alama so takeyi ta zauna min a gida kuma baza ta zauna ba wallahi." Uwani tace"To yaushe ma ai 'kafarmu 'kafarta." Wasila ta shiga bata labarin irin zaman da sukeyi dashi da kuma dalilin da ya sanya Inna hajara barin gidan.
Uwani tace"To in banda abinshi shikkenan daga an haihu babu wani gyara sai a koma masa ai ba zakiyi daraja a idonsa ba kada ki yarda ya kusance ki sai kin gyara kanki sannan kin tabbatar wannan d'inkin da akayi miki yayi dai-dai sannan idan kin koma masa a haka yazo yaji wani sauyi ai wulakanci ne zai biyo baya."
Wasila tace"Nima abinda nake so ya fahinta kenan ya kasa fahinta." Uwani tace"Aikuwa ba zai ta'ba fahimta ba tunda idanunsa sun rufe kiyi kokari kawai ki san yanda zakiyi ki biya masa bukatarsa idan ta taso kuma kada ki dinga yi masa rashin kunya tunda kinga ba sa'anki bane ni da nake mahaifiyarki watakila ma ya girme ni." Hawaye ta share tace"Uwani nifa bana mishi rashin kunya sai jiya da yau da safe kuma duk shine ya jawo kin san dama can ni bana shiri da wanda ba zai ga darajar iyayena ba Uwani banta'ba jin kaunarki da tausayinki cikin raina ba sai da na haihu sannan na tabbatar da cewar Uwa uwace kuma dolene kayi kishinta koda mahaukaciya ce." Uwani tayi murmushi a hankali tace"Ai dama baka ta'bata sanin me duniya take ciki sai ka haihu tukkuna zakayi hankali Allah yay miki albarka, dake da d

uk zuriar da zaki samu." Wasila ta amsa da ameen tana goge hawaye ta mike a nutse ta shiga janyo manya manyan akwatinan dake gefe a jere
Manya manya atamfofi ta shiga fitowa dasu da mayafai masu kyau da tsada, ta zubesu gaban Uwani tace"Ki za'bi wad'anda sukayi miki sauran kuma sai ki bawa su Inna mai waina." Uwani ta shiga d'aga atamfofin tana dubawa tace"Masha Allahu mungode sosai Allah yayi miki albarka." ta amsa da ameen tana zuba mata kayan cikin sabuwar akwati.....Wani dan karamin akwati ta dauko ta bude kudi masu yawa ne a ciki ta tura gaban Uwanin tace"Ki d'ibi iya yanda kike so wannan kud'in da tarin atamfofin nan na samesu ne a haihuwar da nayi....Uwani ta tsorata da ganin Uban kudin dake cikin akwatin tace" Ki dai bani abinda kikayi niyya Wasila duk wannan kudin naki ne."? Girgiza kanta tayi tace"Uwani basu kadai bane ma kinga wad'annan takardun shaidar mallakar rumfuna ne cikin babbar kasuwar dake cikin gari (sabon gari) wanda maigidan ya mallaka min duk saboda ya sameni cikkakiyar budurwa yanzu haka ban san iya adadin kudin da ake samu ba cikin ko wace rana, yace dai zamuje a bude accont ya dinga sanya min kudin a ciki." Uwani ta fashe da kuka tana kallon 'yar tata tace"Nagode Allah da mazon Allah da Allah be sanya kun d'auki hud'ubata ba kun zubar da mutuncinku a titi nasan da mutumin nan be sameki cikkakiyar mace ba da ba zai miki wannan halaccin ba, kuma da tuni zamanku Baiyi nisa irin haka ba ('kalube gare ku 'yan mata kuyi tattalin budurcinku domun ku mi'ka shi ga wanda ya dace shine mijin auranku, koda namiji bai maka kyauta ba to abin alfahari ne ya sameki cikakkiyar mace)
Chapter 92 · 0% Book details