Sashe 105
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Gari na waye wa ta tashi da walwala da farin ciki sai shiri takeyi shi kam yana kwance yana kallonta kwata kwata baya son tayi nesa dashi dan dai bashi da yanda zaiyi ne kawai, ya shirya cikin manya kaya kamar dai yanda ya saba, duk ranshi babu dadi kawai dai yana kokarin daurewa ne amma duk da haka sai da fahimta to itama nata bangaran tasan tilas tayi kewarsa amma haka zata hakura dan gaskiya tana so taje ta gaisa da iyayenta sosai.....Kafin su tafi sai da ya fara kaisu gidan Hajja suka gaisa sosai Hajja tayi mamakin girman baby zahra yarinyar tayi wayo sosai sai kace wata 'yar wata biyar.
Hajja ta ke'be da Wasila tace"Dama inata so inzo gidan naku Allah be nufa ba to tinda Allah ya kawoki sai ki tafi da ajiyar da nayi miki."
Wani garin magani ne a cikin wani madaidaicin bokiti tace"Kullum ki dinga sha da madara ko nono daga can sakwatto nasa aka hada miki, ita kuma wannan zuma ce kada kiyi wasa da ita kullum kina shan murfi biyu safe da dare, idan kikaji dad'insu nasan da kanki idan sun kare zaki bukaci ayi miki wani." Wasila ta sunkuyar da kanta kunyar Hajja takeji sosai godiya tayi mata cike da kunya tana kara jin kaunar matar a cikin ranta.
Hajja har mota ta rakosu tana fad'in "Su gaishe da mahaifiyar tasu insha Allah ranar daurin aure tare da ita za'azo."........Garba ne ke driving Rashida na kusa dashi da baby a hannunta....Ita dashi kuma suna bayan mota sai kalamai take mishi wai ya kwantar da hankalinsa insha Allahu sati guda kamar yau ce."
Ya kalleta sosai yace."Ni nace miki sati guda zakiyi."? Ta kalleshi tana marairace fuska a langwabe tace"Hakafa kace dani shekaran jiya."
Yace."Takura min kikayi shiyasa na fada miki haka, yau laraba ko."? Ta daga kanta tana kokarin mai da hawaye, yace."Zan iya daurewa kuyi kwana biyu shima dan dai babu yanda zanyi ne! Ranar juma'a idan na shigo daurin aure sai mu tafi."
Murya na rawa tace"To baza muje pataskum din ba." Yace."Wane pataskum kuma Itama Momyn ai nan za'a kawo ta sai ku had'u kawai ku gaisa."
Tace."Ai sai dare za'a kawota kuma lokacin nasan mun tafi." Yace."Ni zanyi magana da Malam d'in kancewa ana daura aure a tura mota a daukota ke Ni da kaina ma zan tura Garba ya daukota da sauran 'yan uwa sai ku gaisa da juna.'
Shuru tayi masa domun ta fahimci duk dubarar da zatayi masa ba zai amince ba.
Haka suka isa Garko kowa na jin damuwa cikin ranshi mussaman shi Uban gayyar da yake fargarbar dare yay yasan kuma shi da bacci sai dai yaga anayi.
Amadu kafin ya tafi babu inda bai je sun gaisa ba cikin dangin Wasila yau kowa yaga mijin da take aure suka zama abun kallo a garin ba'yan uwansu kadai ba harda jama'ar gari fitowa suke suna kallonsu mussaman da wani matashin saurayi dake shiga kano sarin kaya ya gane fuskarshi sosai ya dinga watsawa mutane ai shine *Amadu Musa Ba.Iya.ka d'an takarar governor Kano* Aikuwa Jama'ar garin Garko tamkar an musu albishiri da gidan aljanna! suka fito kwantsinsu da kwarkwartasu suna ihu da fad'in "Allah ya baka mulki jahar kano fari mai farar anyi maliya mai ruwan 'kare kukanka." Ganin yanda Jama'a suka nuna masa 'kauna sukayi dafifi a jikin motarsa ya sanya ya koma cikin motar tashi ya bude wata ma'ajiya da yake aje kudi ya daukosu dami guda, ya wakilta mutane biyar yace."kowa a bashi abinda ya samu." Aikwa Jama'a sukayi layi suna ihu da 'kara yi masa kirari.....Wannan damar da ya samu ce ya sanya ya Umarci Garba da yayi maza maza yaja motar su bar gurin dan idan ba haka ba jama'a baza su bari ya tafi ba.
Su Wasila na cikin gidan Malam mata dam'kam tamkar suyi mata sujjada ita abun ma mamaki yake bata sai wani bata girma ake kowa so yake yayi tozali da ita, wato tun mijin nata bai zama governor ba har sun soma kiranta da matar governor dariya kawai take musu itama ta fito da kudi daga jakarta ta shiga raba musu......Deluwa sarkin kanzagi tace"Hajiya Wasila ina fatan idan kun samu mulki a Hannuku baza ki manta da Kauyen Garko ba domin dai nan ne tushenki asalinki Karamar hukumar garko na bukatar hanyoyi masu kyau, na bukatar wuta da ruwa da kuma makarantu gami da asibitoci sannan muna bukatar tallafi domin mu inganta harkokin noma da sauransu."
Wasila dukanin abinda Deluwa ta fad'a sai da ta rubuta a wayarta tace"Insha Allahu duk su kwantar da hankalinsu idan mijinta ya samu mulki a hannunsu Wannan karamar hukuma zata zama city za'a gyara sosai yanda kowa zaiyi sha'awarta.
Sai bayan magariba suka samu sassaucin mutane a gidan, Bitan ta shigo dakin bayanta goye da zahra tace"Oh! ai shikkenan kuma gidan nan zai zama sansani na jama'a duba dai mutane sun kasa bari ki huta abincin ma sun hana kici cikin nutsuwa."
Wasila tayi dariya tace"Bitan ai haka siyasa take dama zakiga mutum kwata kwata baida nutsuwa daga zarar na bar garin inace shikkenan kuma." Bitan tace"Aikuwa dai kuna kokari wallahi ga baiwar Allah nan itama an shiga hakkinta." Tafada tana kokarin kwance zahra daga bayanta.
Tace"Ki bata nono tasha Rashida zata shigo muku da abinci."Yarinyar na ganin mamanta ta soma cilla kafafu tana b'angala dariya.
Bitan tace"Ji ja'aira wai ta san uwarta."
Wasila na dariya tace"Bitan wannan yarinyar wayo ne da ita ai."
Bitan tay dariya tana kokarin fita daga dakin tace"Ai yaran yanzu dama da wayonsu ake haifarsu.
Tana fita Inna Hajara ta shigo gidan tare da dan autanta da yake dauke da kwanukan abinci."
Bitan tace"Yanzu Hajara sai da kika yi girki bayan komarwar ki gida."
Hajara tace"Murhu biyu nayi shiyasa nayi sauri."
Bitan tace"A gaskiya dai mana." Kicin ta nufa ita kuma Inna Hajara ta shige masaukin su Wasila.
Wasila tace"Inna Hajara sannu bakya gajiya da zurga zurga koda yake babu nisa sosai ai.....Hajara ta zauna tana fad'in"Ke ni zurga zurgar da nakeyi kullum ai koda kudi aka hadaki ba zaki iya ba." Wasila tayi dariya tace"Ai kam wallahi bazan iya ba, tace"Inna hajara shine tun bayan tafiyarki baki sake zuwa ba ko."
Inna hajara tace"Ke rabani da zuwa wannan gidan da ba'a bukatata a ciki."
Wasila kamar tayi dariya sai dai ta daure tace"Haba Inna waye baya bukatarki." Tace"Rufe min baki kina so ki kare mijinki ko? bayan kin san shine ya koreni daga gidansa to me zai kaini ni ba kwad'ayayya bace."
Wasila tasa dariya tace"Haba Inna yaushe zai koreki a gidansa Wallahi bakiji yanda yaji rashin dadi ba da ya dawo yaga bakya nan yayi ta fada wai nice nayi miki laifi shiyasa kika tafi."
Tace"Oho! dai ni duk abinda nakeyi dominsa nakeyi da har zai dinga jin haushina dan nace ki gyara kanki ai shine zai mora shiyasa ai koda ki kayi ar'bain banyi gigin zuwa ba dan nasan dole zaki zo da kafafunki, in yaso sai nayi miki abinda nayi niyya ba don halinsa ba kome za'ayi ai shi za'ayi wa amma saboda tsabar rashin hakuri irin nasa yake ganin aibun mutune."
Wasila tace"Dan Allah Inna kiyi hakuri magana ta wuce Yace a baki hakuri." Ta'be baki tayi tace."Uhmm! ni dama ai ba bakuwar zafi bace, Wannan kwanon da kike gani roman 'yan shilla ne mai had'e da maganin gyaran matantaka da kuma ni'ima ki cinye tas ki shanye roman duk wani abu da kika rasa gurin haihuwa idan kinsha wannan roman zai maye gurbinsa.
Wasila tace"To shikkenan Innata nagode sosai babu shakka duk wanda ya rasa iyaye a duniya dole yayi kuka." murya na rawa ta 'kare maganar.
Inna hajara tace"To meye abin kuka kuma mu dai kullum fatanmu ki zauna dakin mijinki lafiya kiyi masa biyyaya domin ki samu rabauta duniya da lahira, itama Rashida addua muke kan Allah ya kawo mata miji nagari kamar naki."
Wasila tace"Ameen Inna insha Allah Rashida zatayi aure komai nada lokaci dama.
Tace"Inna gaskiya bazan boye miki ba naji dadi sosai da faruwar wannan abu Kawuna Malam zai auri Uwani wallahi ji nake tamkar babu wanda ya kaini farin ciki da faruwar al'amarin.
Inna Hajara tace" Shi al'amarin Ubangiji dama haka yake ai Allah ya kaddara akwai aure tsakanin Mahaifiyarki da Malam babu abunda zamuce sai dai muyi fatan alkairi shi kuma Yahuzu Allah ya jikansa ya gafarta masa."
Tana goge hawaye ta karashe maganar, itama Wasila taji zuciyarta na kokarin karyewa tuno mahaifinta da tayi sai dai kawai ta daure ta cigaba da yi masa adduar samun rahamar Allah a cikin zuciyarta.
Inna Hajara bata bar gidan Malam ba sai da ta tabbatar da Wasila ta shanye roman 'yan shillan nan sannan tayiwa Bitan Sallama ta tafi gidanta.
Koda malam ma ya dawo suka ke'be suna sake gaisawa da tambayar bayan rabuwa Wasila tace"Malam ji nake kamar nafi kowa murna da farin cikin da kasantuwar wannan abu kai da Uwani Allah Ubangiji ya sanya alkairi a ciki."
Mai allo ya dinga amsa cike da walwala da farin ciki, Yace."Hakan shine suttura da kuma mutumcin mahaifiyar taku."
****
Sai bayan goma da rabi ya shiga gida a gajiye sosai dan bayan sun bar garin Garko can 'karamar hukumar *Gaya* suka Wuce shi da Khalifa da jama'arsu, sai yamma lis suka dawo saboda yasan masu gidan basa nan yasa ya yada zango guest house dinshi Khalifa ya zauna yana d'eba masa kewa Sai da Hafsa taga dare yayi mijinta bai dawo ba ta kirashi a waya, sannan ne suka rabu kowanne ya tafi gidanshi