Sashe 85
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Yace." Kada kice komai ni nayi niyya kuma idan nayi kyauta ba'a cewa dani dan me? na jima da mallaka miki wasu kadarori nawa tun ranar da na amshi budurcinki na mallaka miki rumfunana biyu dake cikin kasuwar sabon gari, naki ne a halin yanzu halak malak, tun daga ranar dana mallaka miki kawowa yau din nan duk wani abun da aka samu na cinikayya suna cikin asusuna, insha Allah zamuje a bude miki account zan sa miki kudinki a ciki, bayan wannan kuma akwai sabuwar motar dana siya miki tana can gareji a ajiye, yanzu ki rike key d'in a hannuki." Ya mi'ka mata key din motar yana murmushi.
Hannunta ne ya shiga rawa, ta rasa ma abinda zatace masa sai kawai hawaye ya 'balle mata, rungumeta yay tsam a jikinsa yana shafa bayanta, cikin shashshekar kuka tace"Nagode mijina Ubangiji Allah ya kara maka lafiya da nisan kwana Allah ya rabaka da sharrin masu sharri Allah ya bamu zaman lafiya da zuria masu albarka." Ya dinga amsawa yana dan bubbuga bayanta a hankali.
****
Cikin ikon Allah da hukuncinsa komai na tafiya dai-dai a zamantakewar auransu, ta samu nutsuwa dashi ya samu nutsuwa da ita, yayin da karatunsu na al'kur'ani yayi nisa sosai yanzu sun wuce izifi ashirin tunda kullum sau biyu yake musu kari, bangaran littafan addini kuwa sun wuce matakin su ahlari da fikhu yanzu manyan littafai yake musu irin su Minhajil musulum zaduzjaujen Ismawi balaga......bangaran ilimin addini Wasila da Rashida ba'a cewa komai sai godiyar Allah.
Cikinta ya shiga wata na tara, lokacin kuma ciwuka suka tsananta yau ciwo gobe ciwo haka dai take daurewa duk sanda bala'in ya isheta sai ta shiga daki taci kukana ta koshi.............Gashi baya xama a gida sosai kusan kullum sai sun fita da jama'arshi yawon campain, wani sa'in ma
kwana sukeyi ko kuma su dawo cikin dare lokacin ta dade da yin bacci, ga Rashida ta soma zuwa makaranta abun dai duk babu sauki ta kowanne bangare wani lokacin hajja itake zama tana debe mata kewa idan kafafunta sunyi tsami ta matsa mata a gaskiya babu abinda zata ce da matar sai dai addua.
Akwai ranar da Anti Kubura ita da yaranta suka zo gidan suka tarar da Hajja na matsawa Wasila kafafunta duk sai suka shiga mamaki mai tsanani yanzu kamar hajja ke aikin matsar kafa.....Anti Kubura ta kufula ranta yayi masifar 'baci ta kalli Wasilan shekeke tace"Wato asiri da surkullen naku na fulani ya dawo kan baiwar Allah wacce bataji ba bata gani ba, kawai saboda tsabar rashin arziki ki mike kafafu ki sanyata matsar kafafu shin itace tayi miki cikin da zaki dinga sata aikin wahala? ke ko kunya bakiji ba." ! Hajja tace"A'a kubura nice nasa kaina ba itace ta sani ba, to idan ma itace ta sani laifine dan na matsa mata kafafunta ai lalura ce! bana son irin abinda kikeyi kubura." Hajja ta karashe maganarta cikin jin rashin dadin abinda tayi.....Suhairat da takeji kamar taje ta turmushe Wasilan ita da cikin jikinta tace"A'a Hajja wallahi da sake! baxai yiwu ba idan suna cin 'kasa to su kiyayi ta shuri! asirinsu da surkullansu ba zaiyi tasiri a kanki ba, shi da Yaya Amadu da yaga zai iya sai yaje yayi, amma kamar wannan mara gata da galihu ta saki a gaba kina mata matsar kafa! ai bata isa ba idan ita bata san darajarki ba to mu mun sani."
Wasila ta soma kokarin mi'kewa ta bar musu gurin......Hajja ta dan rike hannunta tana mata sannu, hawayen dake kokarin zubo mata ta mayar ba tace komai ba tabar gurin, tana jin Suhairat na zaginta da kiranta 'Yar iska jahila mai bin maza." Wannan kalmomi sunyi mata ciwo sosai, kawai ta kwanta kan gado ta shiga kukan bakin ciki da takaici! Illar ka aikata mummunan abu kenan bata ta'ba zina ba amma gashi anzo har cikin gidanta ana kiranta da karuwa me bin maza...
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*alliya:
'Yr Bngr Sys
*72*
Bayan shigar Wasila d'aki Hajja ta shiga yiwa anti kubura da Suhairat fad'a kan abinda sukayi bai dace ba suzo har gida s suna zagin matar gida......... aikin matsar kafafu itace tasa kanta ba wai Wasilan ce ta sanyata ba, tace mutukar idan kun san tashin hankaline zai kawo ku to ku daina zuwa dan kun san idan Amadu yaji ba zaiji dadi ba bana kaunar abinda zai 'bata masa rai kamar yanda baya kaunar abinda zai 'bata min rai! Ke suhairat ki iya bakinki wallahi naji kina kiranta karuwa a gidan ubanki tayi karuwancin? to wallahi kika sake Amadu yaji wannan maganar zai iya daureki kuma wallahi ba zance masa dan me ba tunda bakinki ne ya jawo miki." Da jin abinda Hajja take fada sai kawai anti kubura ta fashe da kuka tana fyace majina tace"Haba Hajja ashe kudi yafi zumunci kada fa ki manta ni dake uwarmu daya ubanmu daya, Amadu kuwa bake ce kika haifeshi ba dan mijinki ne amma kike kokarin za'barsa akaina shikkenan nagode."Anti kubura ta karasa maganar tana mikewa, tsaye suma Suka mike ransu a 'bace! Hajja tace"Yanda kika dauki al'amarin ni ba haka na daukeshi ba Kubura nagode kwarai yau ni kikewa gurin haihuwa ko babu komai." Anti kubura ta kad'a kan 'yayanta suka fita daga gidan ransu a tsananin 'bace! Hajja kuwa sai da ta matse hawaye kafin ta mike ta shiga cikin daki.
Rashida da ta dawo gidan duk sai ta gansu wani iri babu cikakkiyar walwala alhalin ba haka ta tafi ta barsu ba, sai da suka ke'be da 'yar uwarta take tambayarta abinda yake faruwa, Wasila na hawaye take fada mata irin zagi da cin mutuncin dasu Suhairat da mahaifiyarta suka zo sukayi mata.
Rashida ta fusata sosai tace"Wallahi anti Wasila da ina gidan sai na rama mi ki wannan ai rashin mutuncine da iskanci su shigo har cikin gidanki suna zaginki na rantse da girman Allah duk ranar da Suhairat ta sake zuwa gidanan ta zage ki sai na nuna mata wacece ni sai ta futa da fashashshan baki." Wasila tace"Ki kyaleta rashida tayi na farko tayi na karshe nima na dauki al'kawarin kan duk ranar da ta sake zuwa taci min fuska cikin gidana sai ta gane bata da wayo...........
To Yau ma bai shigo gidan da wuri ba sai kusan sha biyu da rabi na dare lokacin tayi bacci har ta gaji dan wajejan takwas ta kwanta yanzu kwanciyar ma wuya take mata sai tayi ta juye juye da zarar bacci ya dauketa bata minti talatin sai ta farka, jin shigowarsa dakin ya sanya ta mike zaune......Yace."Baki bacci ko jikin ne.'? Girgiza masa kai tayi, yace."Okey bari nayi wanka ko." ba tace masa komai ba ya nufi toilet, tana zaune ya fito ya kimtsa jikinsa ya fita daga dakin
Minti biyar ya dawo hannunsa rike da ledoji guda biyu ya aje kasan kafet ya bude fridge ya dauki lemo da ruwa........Lokacin da yake kokarin zama kasan kafet ne ya fahimci damuwa a fuskarta, ya kalleta cike da kulawa yace." Menene? Hawayen da take 'boyewa suka su'bce ta soma kuka da shashsheka
Yaji duk wani annushuwa da farin cikin da ya shigo dashi ya dauke, jikinsa na kyarma ya zauna kusa da ita yana me rungume kafadunta da hannunsa....."Kiyi shuru ki fada min abinda ke damunki bana son wannan kukan naki." Abinda yake fada kenan yana goge mata fuska da hannunshi.
Kwanciya tayi a jikinsa tana cigaba da kukanta. Hankalinsa yay masifar tashi ya dinga rarrashinta da kalamai masu sanyi,da kyar tayi shuru yace."Kukan da kikeyi bai da amfani saboda yana sa hankalina tashi ki fada min abinda ke damunki."
A hankali tace"Meye tsakaninku da Suhairat."? Sai ya shiga tunanin wacece ma Suhairat? can ya tuna yarinyar anti kubura ce kanwar Hajja. Yace."Kanwata ce me ya faru.''?
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Ai kai baka da wa ko 'kanwa." Yace."Eh hakane ita suhairat din yarinyar kanwar Hajja ce anti kubura."
Tace."Kace mata kada ta sake zuwar min gida tunda ba alkairi ne yake kawota ba."
Ya danyi shuru yana mamakin maganarta, cikin nutsuwa yace "Kince ba alkairi ke kawota ba sai ki fada min abinda ya faru dan na fahimci dama keda ita tuntuni kunsan juna."
Tace."Idan na fada maka abinda ya faru ranka zai 'baci watakila ma ka dauki tsatstsauran mataki akansu har ita anti kuburan, fad'ar maganar bata da amfani tunda ba alkairi ba
ne, dalili kenan da ya sanya nace ka hanasu shigowa inda nake dan mutukar suka sake zuwa suka zagi iyayena sai na rama.".....Ranshi yaji ya 'baci jin abinda tace Yace."A gaban hajja kukayi wannan shashancin."? Mikewa tayi daga jikinsa tace"Nifa kar kaga laifina nasu ne dan bar musu gurin ma nayi saboda abinda ya dameni shi ya dameni."
Yace."Shikkenan tunda bakya so su shigo miki gida zasu daina shikkenan ko?" Babu kunya tace"Eh." Yace."Sauko kici abinci." Tabi ledojin dake gabansa da kallo, a hankali ta sauka ta dan mike kafafunta shi kuma ya shiga bude ledojin manya manyan kaji ne gassasu wanda sukaji hadi sosai sai kamshi sukeyi.
A nutse suke ci suna dan hira yana bata labarin irin nasarorin da yake samu ta 'bangaran siyasar shi, yanzu babu local goment din da basu kai ziyara ba kuma ko ina sukaje cike da nasara suke dawowa, al'amarin siyasar dai ya dauki zafi sosai da sosai ta inda ko ina ka zaga a fad'in jahar kano zance Amadu Musa ake da fatan Allah ya bashi mulkin jahar kano a hannunsa, pastes dinshi sai yawo suke a titi kasuwanni gami da jikin gidajen mutane, gabakidaya al'ummar jahar kano sun gaji da mulki Lawal rabo sauyi kawai suke bukata a jahar tasu.