Sashe 13
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Malam mai allo ya kalli Hajara yana girgiza kansa yace."Hakika naji dadi da kukayi gaggawa zuwa ku sanar dani wannan al'amari dake faruwa, wannan rashin tarbiyar ne yasa tuntuni na hana Yahuza tafiya maraya da zama saboda nasan tilas a haifi da mara ido a lokacin ya rufe ido yaki sauraran kowa shi dai kawai ya tafi burni ya nemi kudi karin abun kuma ya hadu da mata mara kamun kai ya aure ai asalin lalacewar yaran daga mahaifiyarsu ne da ta basu tarbiya da duk haka bata faruwa ba mu kanmu Uwani bata ganin girmanmu ballanta tana nuna musu muhimancimu a gurinmu, amma babu komai insha Allahu gobe tare zamu tafi kome za'ayi kafata kafar yaran nan dan bazan bari su lalace ba ace muna kallo nan zan kawo su duk in aurar dasu kowa ya huta."
Hajara tace"Wannan shawara taka itace abun dubawa Allah ya tabbatar mana da alkairi." suka amsa da "ameen" gaba d'ayansu.
To kamar dai yanda malam mai allo ya fad'a hakane ya kasance da wurwuri yayi sallama da 'yan uwa ya fad'a musu abunda ke faruwa suma suka bada goyon bayan kan hukumcin da ya yanke, kana suka hadawa Haraja sha tara ta arziki suka bita da godiya da fatan sauka gida lafiya.
Uwani da Rashida kadai ne a gidan sunci kwalliya har sun gaji kamar wanda zasuje gidan buki ga cefane nan kayan miya da nama cikin takarda za'ayi miya gida sai kamshi yake yi....Amina na kwance a tabarma tana danna katuwar waya Uwani na kicin tana aiki Malam mai allo yayi sallama a kofar gidan.....Gaba d'ayansu sai da gabansu ya fadi! Uwani ta fito daga kicin da ludayi a hannunta tana fad'in"Ke Rashida muryar wa nakeji kamar ta wannan masifaffan tsohon."! Rashida tace"Wallahi nima irib muryarshi naj......Kafin ta karasa muryarsa ta sake karad'e gidan "Salamu alaikum."!! Uwani ta amsa da karfi tana fad'in" Waye wai yake rangwada mana sallama kamar munci bashi."
Malam mai allo ya girgiza kansa jin muryar Uwani radau! yasan zata aika tunda dama ba kunya gareta ba......"Nine malam mai allo na Garko."!
Yafada yana dafe kyauran kofar gidan.
"Ayyo koda naji wannan sallama haka to ana zuwa." Uwani tafada tana jan karamin tsaki." Ta kalli Hajara "Ai sai ki tashi kije kece tilas dinsa ni kuwa yace zai min wannan wa'azin sai dai mu kwashi 'yan kallo ni dashi a unguwar nan."
Jiki a sanyaye Rashida ta mike ta dauki yalolon mayafinta dake kan igiya ta yafa, duk rashin kunyarsu suna shakkar malam mai allo dan baya musu da sauki.........Tana fitowa ta durkusa tana gaisheshi bai amsa ba sai kare mata kallo yake ganin irin dinki dake jikinta atamfa ce duk an kacalcalata saman nonowanta duk a waje......Girgiza kansa yayi yace"Rashida kece kika dawo kamar ba d'iyan musulmai ba wannan shigar ta jikinki ta sabawa sharia meye abun burgewa anan.? to babu komai duk magana ta kare kiyi maza ki kirawo min daya marakunyar yanzu yanzu zan tasa ku a gaba mu wuce garko saboda na samu labarin ashararanci da kukeyi a gari mahaifiyarku na daure muku gindi kuna yiwa manya mutane rashin kunya wai Wasila ce take siyasa tana gogayya da maza saboda kasa ta rufe idon ubanku shiyasa annabi yace ka zabawa 'yayanka mace tagari duk dan gudun faruwar irin wannan, mu ba'a son ranmu dan uwanmu ya auri mahaifiyarku ba saboda sam bata da tarbiya gashi kuma kun dauko irin nata halin to kome zakuyi sai da kuyi amma tilas ku koma can Garko da zama idan Allah ya kawo muku miji kuyi aur......"Babu wanda ya isa ya rabani da 'yayana wallahi akan wannan sai in maka mutum a kotu."!!!!Uwani ce ke fadar wannan maganar ashe tana la'be tana jinsu......"Haka kawai zaka zo har gida kana zagina malam ka rike mutuncinka da girman ka ada can ma ban yarda ba ballanta yanzu da nasan ina da 'kumbar susa a hannuna dan haka ni banga wanda ya isa ya rabani da 'yayana ba."
Malam mai allo yace."Uwani rashin kunya za kiyi min."? Wannan ba rashin kunya bace gaskiya ce, sai da yarana suka girma suka zama mutane inacin ganiyarsu sannan za'a lalla'bo kawai saboda an samu labarin mun faso gari ace ga zance ga magana kafad'i idan kana bukatae wani abu yanzu yanzu sai na kira Wasila tayi maka hasafi ba wai kace zaka tafar min da 'yaya kauye ba."
Malam mai allo 'kwalla ta taru a kwarmin idonsa yace."Baku da kudin da zaku bani Uwani kuma kinyi min abunda yafi haka dan kin zageni a yanzu ba wani abun bane ni dai na gama yanke hukunci ke Rashida idan na isa daku maza jeki had'o kayanku muka kama hanya mu tafi.".
Rashida ta mike ta shiga cikin gidan tana kuka wayarta ta dauka ta kira Wasila ta fada mata abunda ke faruwa.....Wasila tace''Kome zaiyi kar ku sake ku bishi ku kyaleshi a soro idan ya gaji da tsayuwa ya gaji ya tafi masifaffan tsoho kawai." Uwani kuwa taja tunga ta tare bakin kofa ta rantse babu inda zai tafar mata da 'yaya......Suka dinga tafka rigima da Malam mai allo Uwani ta dinga yi masa rashin kunya kamar ba wan mijinta ba har hankulan mutane ya fara dawowa kansu mutane suka fara taruwa a'lamarin yayi wa malam ciwo a ranshi sai ya fito waje ya tsaya yana tsumayin fitowar Rashida ganin ya fita daga gidan sau kawai Uwani ta rufe kofar gidan ta zura sakata ta koma ciki tana surutai "Idan ka kaji da tsayuwa ka tafi tsoho mai nacin tsiya kawai..........Garba dake can gefe suna magana da wani mutumi ya nuna masa malam mai allo dake bin kofar gidan da kallo yana mamakin rashin kirkin Uwani wato shi suka rufewa kofa, sai ya sanya gefan babbar rigarsa yana goge gumin saman goshinsa.....Garba ya karaso inda yake hannu ya mika masa suka gaisa yace." Aramma idan ba zaka damu ba ina so mu tattauna wata magana da kai." Malam mai allo dake neman wanda zai rarrashe shi kan abunda su Uwani sukayi masa yace."Babu komai yaro ina sauraranka." Garba yace."Muje mota arrama." Malam mai allo baiyi shakkun bin Garba ba saboda lokaci guda yaji ya aminta dashi suka nufi inda yayi parking din motar a tare.
_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/18, 2:01 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*PEGE 'DIN YAU NAKI NE*
*Real Eshaa🌺*
Marubuciyar book d'in.
*NAGA RAYUWA*
Fatan alkairi har karshen rayuwa aysha Allah ya kawo miji nagari wanda zai rike min ke tsakani da Allah👏🏻
~~~~~~~
*Free Pege15*
Cikin nutsuwa Garba yace."Aramma alamu sun nuna kamar kana da ala'ka da masu wancan gidan, dan Allah idan babu damuwa ina so in san wani abu dangane da wata yarinya a gidan mai suna Wasila." Malam mai allo yace."Ni a matsayin mahaifi nake a gurin Wasila da kanwarta Rashida Yahuza mahaifin yaran kanina ne ciki daya muka fito kuma mu 'yan asalin garin garko ne Yahuza yazo kano neman kudi tun yana saurayi sai ya sai gida yayi aure tare da wannan matar wacce ta kasance a matsayin mahaifiyar su Wasila da Rashida......Garba ya katse shi ta hanyar fadin"Alhamdullhi dama abunda nake so naji kenan ashe faduwa tazo dai-dai da zama malam idan babu damuwa zamuje can gidan ubangidana wanda shine ya sanya ni nayi masa bunkice akan asalin iyayen yarinyar to kuma sai nayi katarin had'uwa da kai, kar kadamu arrama idan mun isa sai kayi masa cikakken bayani akan yarinyar." Malam yace."Yaro ina fata dai ba laifi yarinyar tayi ba domin nima abunda ya taso ni kenan saboda na samu labarin cewar tana cin mutuncin manyan mutane a gari tana fakaicewa da siyasa wannan shine dalilin zuwa na garin." Garba yace."Kar ka damu arrama alheri ne insha Allahu muje koma meye zakaji daga bakin mai gidana." Malam yayi shiru yana nazari yana tsoro kar daga zuwan sa ya shiga masifar yarinyar nan tasa a daure shi baiji ba bai gani ba....Girgiza kai yayi yace."Babu damuwa samari muje kawai Allah yasa alheri ne." Garba ya kunna motar yaja suka futa daga cikin unguwar.
Suna tare da Khalifa a harbar gidanshi suna hutawa motar su Garba ta shigo cikin gidan.....Can parking spece ya nufa yayi parking din motar ya fito ya budewa malam mota yana fitowa Idanun Ahamdu suka sauka a kanshi A fuzge yaga suna kama da yarinyar babu tamtama wani nata ne amma babu shakka Garba ya iya aiki bai dauka futa ta farko za'a samu nasara ba to amma yanda yaga kamilin mutum sai yasha jinin jikinsa anya wannan kudi zasu rud'ashi ko dai ya sauya wata hanyar ne dan baiga alamar zalama ta kudi a idon dattijon ba......A nutse ya mike yana masa barka da zuwa dake suna zaune a wata rumfa wacce aka kewaye ta da wasu kujeru masu kyau tsakiyar kujerun katon teble ne da lemuka akai kana ganin gurin kasan na hutawa ne....Malam mai allo ya zauna nutse suka gaisa cikin girmama juna......Garba yace."Yallabai Allah ya takaita mana wahala ina zuwa unguwar nayi katari da wannan bawan Allahn shine yake shaida min shi din shine mahaifin Wasila shima zuwanshi kenan garin to anan na nemi alfarma a gurinshi kan yazo kana son magana dashi."