Sashe 57
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Khalifa ya jima yana mamaki gami da jajanta al'amarin! hakika abinda wasila ta aikata babban abune wanda ya cancanta da ayi mata ko wane irin hukunci, to amma kuma baiji dadin hukuncin da ya yanke a kanta, da tayi shawara dashi da farko ba zai yarda ya saketa ba, zai fahintar dashi cewar sakin bashi ne sulotion, ya zauna da ita tinda yayi wa kawunta alkawari kuma yayi mata uziri! duba da cewar akwai kuruciya a tattare da ita in yaso yayi mata horon da za tagane abinda ta aikata babban abu ne, shawara ta karshe da zai bashi shine yayi aure yayi rayuwa da matarshi a cikin gidan tana kallo yasan dole za tayi hankali ta shiga taitayinta amma yaji zafin sakin da yay wa yarinyar mutune ya mai da ta karamar bazawara.
Ajiyar zuciya ya sauke yace."A gaskiya banji dadin wannan abu ni da kayi shawara dani ba zan bari ka saketa ba, amma yanzu tinda har haka ta kasance please ka dauki niyya ka kuma 'kudirta a ranka kan cewar ka mayar da ita ni da kaina zanje na dawo maka da ita, sai shawara ta biyu shine kayi gaggawar yin aure domun ta gane kuranta.
Ya kalleshi yana ya mutse fuskarsa yace."Kafi kowa sanin idan na bar abu na barshi har abadah! a yanzu idan da wacce na tsana a duniya to wannan yarinyar ce na natseta wallahi, bani kaunar ganinta, saboda haka maganar ma in da
wo da ita bata taso ba, aure kuma sai na huta zanyi."
Khalifa yace."Kar kayiwa mai allo haka Ahamdu! ka duba daraja da furfurar dattijon! ka duba amanar da ya baka! aure baifi sati hudu ba har anyi an gama! wannan wace irin rayuwa ce."! Kai ya shiga girgizawa yana wani irin mirmishi na takaici yace."Komai abinka ba zan dawo da yarinyar nan ba taje kawai! shi kuma mai allo da kaina zanje nai mishi bayanin komai." Khalifa ya dinga kallonshi yana girgiza kanshi tabbas yasan halin abokin nashi! da zuciya da kuma ramuwar gayya ba tun yau ba! Yasan bai da hakuri ko kad'an! mutukar kayi mishi abu bai rama ba to shine yaga dama.
***
Ta kira wayar Camas! ta kai sau ashirin bata dauka ba, sai abu ya shiga bata mamaki! taje wayar tayi tana fadin"Ko bata kusa da wayar ne bari anjima na sake kiranta......Ita kuwa Camas! a lokacin suna tare da As yana shaida mata abinda ya faru dashi itama tana shaida masa irin hukucin da Wasila ta yanke kan cewa ta bar harkar Siyasa kuma ta tabbatar masa da cewar Ahamdu ya saketa yanzu haka tana gidanta.
As yaji dad'in labarin Camas! sai dai kuma baiji dadin furucin da tayi ba na cewa ta bar harkar siyasa hakika ta zama wani jigo a tafiyar tasu, dole ya shirya yaje gidan domin ya rarrasheta ta dawo kawai su cigaba da fafatawa,
Camas! na fita daga gest house din As kira ya sake shigowa wayarta koda ta duba taga Numbar Rashida ce sai ta kashe tana jan tsaki tasan dai zancen gizo baya wuce na 'koki! Tana kokarin shiga motarta text ya shigo ta bude tana dubawa.
_Camas! kina ina ne? inata kiran wayarki baki dauka ba dan Allah kizo gidana yanzu zamuje banki zan cire kudi yanzu ina jiranki_
Tsaki taja mai tsayi lokacin da tagama karanta text din ta bude mota ta shiga tana fad'in"Shashasha kawai ai kud'in nan sun shiga accont dina kenan! ke kin tsira da gida ni na tsira da kudi a tafiyar nan! babu abinda baki mallaka ba dan'kareran gida iyayen kudi gwala gwalai, ni kuwa fa in banda wannnan fankon motar babu abinda na tsira dashi, saboda haka na cinye kudi wallahi komai za'ayi sai dai ayi." Tuka motarta tayi ta bar gurin hankalinta a kwance.
Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*51*
Wasila tayi ta tsammanin amsar Camas! taji shiru har wajejen karfe goma na dare bata daina kiran Camas! a waya ba, gashi dai tana shiga amma kuma taki dauka......Uwani tace"Wai kiran me kike mata ne? ni nasan da wuya Camas! ta dawo gidanan dan baki ga irin zagin da rashida tayi mata ba." Tace."Uwani ba wannan matsalar bace, kin san na fad'a miki jiya Ahmdu yace zai min bincike cikin accont dina sai na yanke shawarar kwashe kudina dake ciki na mayar accont din camas! kudin suna da yawa fa kusan miliyan biyar ne zuwa shida, a jiya na ciro dubu hamsin to jakar tawa na motarshi, ban dauko ba, wannan dubu dayan ma da nayi kudin mota gurin zuwa nan na siyi kati Allah ne ya taimakeni na tsinta cikin jakar dana zo da ita, kinga yanzu duka sau dari biyar a hannuna gashi ina ta kiran Camas a waya taki dauka."
Uwani ta soma tunani cikin fargaba da faduwar gaba tace"Anya Camas! ba amanarki zata ci ba kuwa irin wannan kira da ake mata ai yaci ace ta dauki wayar idan ba da abinda ta shirya ba.
Rashida tace"Aikuwa wallahi ko tana yawo da ubanta sai ta fito da kudin nan tabd'ijam! miliyan shida za ta cinye lallai bata da hankali.
Wasila tace"Allah nima jikina ya soma sanyi da al'amarin anya kuwa! amma dai bari na sake kiranta mu gani." Nan ta shiga kiran wayar Camas! gashi dai tana shiga amma babu amsa! dukaninsu hankalinsu yay masifar tashi mussaman Wasila da tasan wannan kudin su kadai ne suka rage mata kuma sune zasu taimaka mata ta 'bangarori da dama tunda dai ta 'kudiri aniyar barin harkar jagaliya......Sai kusan karfe daya na dare sannan sukaje suka kwanta dukaninsu babu wanda yay baccin arziki sai juyi sukeyi mussaman wasila da abubuwa suka taru sukai mata yawa, kuka take sosai shashshekar kunanta yasa Uwani mikewa zaune tana kallonta, Tsakanin d'a da mahaifi sai Allah sai taji tausayin 'yar tata itama ta hau share hawaye tace"Wannan kukan bashi ne mafita ba a gurinki, wai shin meye abun damuwa da tashin hankali dan wannan mutumin ya sakeki ke ba abin alfahari bane a gurinki za kici karanki babu babbaka yanzu fa wata dama kika samu da zaki cigaba da neman kudinki gashi Allah ya sanya miki nasibi a cikin harkar kina nema ki 'barar da damarki, ni dai idan zakiji maganata shine gobe idan Allah ya kaimu ki shirya ki tafi gidan gomnati domin cigaba da gudanar da harkokin siyasarki."
Wasila taja majina tana goge fuska tace"Nifa Uwani na fada miki bazan sake yin wannan harkar ba na fada miki ni yanzu babban damuwa ta shine idan Camas! ta salwantar min da kudina ya zanyi da rayuwata da wane kudi zan kama sana'a me zan juya ni ba zanyi karuwanci ba kuma ba zan koma wannan harkar ba."
Uwani tace"Idan ya kasance Camas! ta salwantar miki da kudi ba sai ki maka ta kotu ba, sannan kina maganar sana'a to tunda kince ba zaki koma harkar siyasa ba kuma kince ba zakiyi karuwanci ba to me zai hana ki shiga wasan hausa (film) nasan mutukar kin shiga wannan harkar zakiyi arziki na ban mamaki."
Wasila ta dinga kallon mahaifiyar tata cike da tsananin mamaki! wai me yasa uwani take hakane? kullum bata da buri illa taga ta dorasu turba mara kyau! idan akwai abinda ta tsana a duniya bai wuce wannan harkar ba film! duk lalacewa ta tattare a gurin koda kai mutumin kirki ne kana wannan harkar jama'a ba zasu kalleka da kima ba.
Ba ta sake cewa da ita koma ba ta koma ta kwanta tare da juya mata baya tana addua cikin ranta tana jinta tana sake kwarzanta mata nasarorin harkar film din da yanda 'yan mata ke samun mahaukatan kudi mutukar sun shiga harkar....Uffan bata sake ce mata har dai taji shiru hakan ya tabbatar mata da cewar bacci ya dauke ta, sai ta mike a hankali taje ta dauro alwala ta fito a nutse ta tada sallah nafila tayi raka'a biyu ta dade sujjada karshe tana kuka da addua da fadin"Allah ya kawo mata agaji ya yafe mata kusa kuranta na baya.....Addua ta shafa ta kwanta kan daddumar bacci me nauyi ya dauketa.
Asubah suka tashi sukayi sallah Uwani ta koma tayi kwanciyarta, Wasila da Rashida suka zauna suna shawarwarin ya za suyi, Tunda yanzu ma sun sake kiran Camas! din bata dauka ba, Rashida tace",Anti Wasila bari gari
yay haske sai muje gidansu shegiya macuciya dama ni tuntuni bana kaunar abotarku da ita na tsaneta wallahi." Hannunta rike da wayar tana ta trying tace"Rashida bamu da tabbacin samun Camas! a gidansu shin ko kin manta ne? ko lokacin da muke unguwar sai tafi sati biyu bata kwana a gidansu ba tana can yawon bin maza watarana ma gidanmu take zuwa ta kwanta." Rashida tace"Na tuna yanzu to ya za'ayi a same ta."? Shiru tayi tana nazari itafa ba tasan ya za'ayi a sami Camas! ba dan bata tantance in da take ba......Rashida tace",Anti Wasila ki shirya sai na raka ki government house din nasan za'a iya samunta a can." Girgixa kanta tay tace"Har abada na bar wannan gidan tunda banda ala'ka dashi a halin yanzu, kuma bai zama lallai a samu Camas! a can ba, ban'ki ma idan anje gest house din Alhaji Ma'aruf mybe a iya samunta a can."! Rashida tace"To ki shirya muje can d'in." Shiru tayi tana naxari kafin tace"Rashida ba zanje ba kawai kyaleta don Allah ni na hakura taje kanta tayi wa in ta min maganar kudin shikkenan idan batai min ba na barta da Allah." Rashida tace"Ni dai da zaki min kwatacen gest house din da naje naci ubanta wallahi sai ta baki kudinki." Girgiza kanta tayi tace"Rashida ba zakije wannan gurin ba kawai dai tinda nace na kyaleta da Allah shikkenan."