← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 84 OF 108

Sashe 84

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Ya fito daure da babban towel ya tsaya gaban mudubi yana goge jikinshi......faffad'an bayanshi ta tsurawa ido tana kallo ta lumshe idanunta tana sauke zazzafar ajiyar zuciya.........Motsin zamansa taji a kusa da ita ta bude idanunta, cike da kulawa yace "Baki bacci ba." ? Dan d'aga masa kanta tayi tana kokarin mikewa zaune Yace."Ki koma ki kwanta mana." ta koma ta kwanta gabanta na dan faduwa tace"Kasha maganinka ko." Kallonta yay sai kuma yayi saurin cewa"Zan dai sha yanzu kafin na kwanta." Ya manta da wani magani dan bashi ne a gabansa ba, ashe ita hankalinta na kansa.

Ya mike ya fita daga dakin, mintina goma ya dawo...... Paracetamol kawai ya 'balla ya watsa a bakinsa ya kora da ruwa, ya aje gorar ruwan saman fridge ya nufi bed din......Tana kallon zuwanshi sai ta rintse idanunta tana takure jikinta.

Bargon ya dan ja a hankali ya shiga ciki idanunta ta rufe dai-dai lokacin da taji hucin numfashinsa a kusa da ita.........Hannunshi ya sanya ya d'an juyo da ita suna fuskantar juna........Ya sanya dan yatsansa kan le'banta na 'kasa yana shafawa a hankali.
Shuru tayi duk kuzarinta yakare, cikin kunnanta ya kira sunanta, taji wani irin yarrrr a jikinta.

A hankali ya cire mata rigar jikinta ya kai kanshi kan cikinta ya sumbata tare da fad'in Allah yay maka albarka yarona." Wasila na jinsa nata magana da dan cikinsa kamar me magana da mutum, mamaki gami da tausayinsa ne ya kamata ta lura yana masifar son abinda ke cikinta tun bai iso duniya ba.

shafa sassan jikinta ya shigayi yana sa harshensa yana lasar sa'ko da luko na jikinta yana aika mata da wasu zafafan kesses masu hargitsa lissafi! wani irin rawa jikinta ya shigayi tsigar jikinta ta soma mikewa kamar dai koda yaushe jikinta ya mutu sosai ta saki jikinta ya dinga jagwalgwala iya son ranshi dan babu inda bai tsotsa ya lashe ba a jikintajagwalgwalata romantinc sukeyi irin wanda basu ta'bayin irinsa ba, cikin jikinta bai hanasu aikata komai ba, Amadu ya aikata komai cikin nutsuwa dan ita ya barwa fagen tayi iya yinta mai gudun kada ciki ya samu matsala sai gashi ta manta dashi, tana biyan bukatar ranta, sai da tayi iya yinta sannan ya shi ya soma nashi cikin nit

suwa tana taimaka masa tare da shashshafa sassan jikinsa, duk sun rikice sun had'a zufa fatar jikinsu sai mannewa takeyi guri guda, kusan tare suka samu gamsuwa suka rungume junansu suna sauke numfashi.

Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah! kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*71*

Can 'bangaran su Uwani kuwa, tun bayan tafiyarsu Wasila sai ta dan samu sassaucin cuzgunawa daga gurin Kuluwa, ta daina kyararta tunda ta gane tana da amfani, shi kansa Kawu Madu din lallabata yake yi wai su shirye suje ga gidan Wasilan tunda basu ta'ba zuwa ba, Uwani ta shiga tunani kan maganarshi tana jin tsoron daukarsu suje garin ganin gida suje su jawo mata abin kunya tasan ba komai ne yake d'awainiya dasu ba sai kwadayin abin duniya, kawu madu kullum cikin naci yake da dai ta gaji sai tace "Shikkenan zasuje amma sai karshen wata, kuluwa tamkar ta zuba ruwa a kasa tasha saboda murna da farin ciki.

***
Sosai *Anti Daba* suka sa'bawa Camas kammani saboda ta kasa kawo musu shaida gamshashshiya wacce zata nuna musu da cewar ita d'in me gaskiya ce, kwanta biyu a hannunsu suka saketa bayan sun mata kashedi mai tsauri kan kada ta kuskura ta kara zuwa filayen nan tace nata ne duk ranar data sake zuwa to sai sun mata dukan mutuwa......A jigace ta fito bakin titi inda tayi parking din motarta ta nufa, wayam! babu ita a gurin, ashe ranar saboda tsabar rud'ewa a jikin motar ta bar key din, kuma akan idanun wasu matasa, aikuwa tana bada baya suka dauke motar, sai yanzu ta tuna abinda ya faru tsugunawa tayi bakin titi rana na dukanta ta dinga kukan bakin ciki, sai da tayi ta gaji ta samu babur ta hau government house ta nufa.

******
Yau dai basu samu damar zaman karatu ba dan basu tashi da wuri ba, Rashida ma gajiya tayi da zaman jiransu ta bar gurin, basu fito palo ba sai takwas saura, lokacin Hajja da Rashida har sun karya suna zaune suna hira...... Kai tsaye inda Hajja ke zaune suka nufa a nutse suka gaisa Wasila sai sinne kai takeyi kunyar hajja takeji sosai, barin gurin tayi ta nufi daning shi kuma ya zauna suna magana da Hajjan.........Suna break fast ta d'an kalleshi sai akaci sa'a shima ita yake kallo, kasa tayi da kanta, ya gane duk sanda take son yi masa magana kunya na hanata, yace."Akwai abinda kike bukata ne."? Ta dago kanta a hankali tace"Ina so ka dan bani waya ta ina so mu gaisa da Kawu duk da dai bani da numbar wayar Kawu Habibu wacce zata sadani dashi nasan baza'a rasa a gurinka ba.'

Murmushi yayi yana goge bakinsa yace."da akwai numbar Kawu Habibu a wayata sai da kwanaki nayi ta kiran wayar baya dagawa nasan fushi yake dani kan abinda ya faru.'' A hankali tace"Kawu Habibu fushi ne dashi nima bama shiri sosai munfi yi da mai allo." Wayarsa ya mika mata yace."Ki duba sunanshi nayi serving da Habibu garko."

Wayar ta amsa tana budawa taga hotonsu ita dashi a fuskar wayar hoton da hafsa ta daukesu lokacin da suka zo hoton yay masifar kyau......... 'Dan kallonshi tayi hankalinsa na kan karamar wayarsa yana dubawa, ta dauke kanta tana sauke ajiyar zuciya bata ta'ba tsammanin haka yake da saukin 'kai ya mai da kansa karamin yaro duk dan saboda farin cikinta.

Tayi ta kiran layin Kawu Habibu gashi dai tana shiga amma bai dauka ba, Ta dan kalleshi sai taga yayi murmushi, a nutse yace."Mutukar fa zai ga numbarta ce ba zai dauka ba har yanzu nima kunyar hada ido nake dashi nasan abinda nayi ban kyauta ba amma ai na bada hakuri kuma ya cancanta a yafe miki ko." Cikin wani irin yanayi yake maganar.......Sai taji tana jin zafin Kawu Habibun meye abin ri'ko da daukar gaba, ai itace mai laifi tunda duk abinda ya faru itace ta jawowa kanta itama yanzu ta daina ganin laifinsa bisa ga sakin da yay mata ta wani gefan ma farin ciki take da hakan ta faru tunda gashi tayi hankali tasan inda yake mata ciwo.

Rau-rau tayi kamar zatayi kuka tace"Kawu Habibu haka halinshi yake kayi hakuri." Yace."Nine zan bashi hakuri ai kada ki damu duk sanda Allah ya saukeki lafiya zan daukeki muje har gidanshi na bashi hakuri ai tunda ina sonki babu abinda ba zanyi ba." Hawaye suka zubo mata ta tsira masa ido tana kallonshi ta rasa wane irin so yake mata! Yace"Ke kam bakya gajiya da koke koke goge hawayenki." Ya mika mata tissue kin kar'ba tayi tana shashsheka, hannunta ya rike ya mikar da ita suka nufi dakinshi.
Rungumeta yay ya rarrasheta tayi shuru kana ya bud'e wata drowar dake gefan gadonshi ya dauko mata wayoyinta da

jakarta, cinyarta ya aje mata yace."Ki duba kiga abinda baki gani ba sai ki fada min."

A hankali ta bude jakar tana dubawa komai nata data sani na ciki ga sabbin kudinta nan na sadakin auranta da sauran tarkacenta a ciki ta aje jakar tana kokarin kunna wayar, ya kar'ba ya kunna mata.
Numbar Kawu Habibu ta dauka a wayar tata ta soma kiranshi, aikuwa ya dauka duk suka cika da mamaki.

Muryarta na rawa tace"Kawu Ina kwana" Ya amsa yana tambayar wacece.''?

Tace."Kawu nice Wasila." Tana ji ya sauke ajiyar zuciya yace."Wasila ya kuke ina fatan kunanan lafiya ko? ina mijin naki."?

Ta dan kalleshi yana zaune yana jinsu, tace"Kawu gashinan kusa dani yana jinka." yace."Masha Allah." Tace"Kawu dan Allah kayi hakuri ka daina fushi nice fa mai laifi dan Allah ka yafe masa kamar yanda mai allo ya yafe masa."
Kawu Habibu yace."Wasila ni tuntuni na yafe masa abinda ya faru kawai duk sanda na tuna sanda yazo gabanmu yace ya sakeki raina yake 'baci sosai, amma ni bana rikon mijinki." Tace"To Kawu me yasa idan ya kira wayarka baka dauka."
Shuru yayi tace"Kawu kayi hakuri magana ta wuce nima nayi alkawari insha Allahu bazan sake baku kunya ba." Yace."Masha Allahu dama haka nake so naji."

Amadu ya kar'bi wayar daga hannunta, a nutse yay sallama Kawu Habibu ya amsa cikin mutumci suka gaisa da juna, Kawu Habibu kunyar abinda yayi masa taso ta hanashi magana, inda shi kuma Amadu ya nuna masa komai ba komai bane ya kuma tabbatar masa da cewar abinda ya faru a baya insha Allahu ba zai sake faruwa ba a gaba..........Kawu Habibu yaji dadin maganarshi sosai da sosai dan yanzu babban burunsu shi da dan uwansa shine yarinyar ta zauna a dakin mijinta.

Mika mata wayar yay bayan sun gama ta karba tana fad'in "Kawu dan Allah idan ka koma gida ka bawa mai allo wayar ina so mu gaisa dashi." Kawu Habibu yace."Insha Allahu idan na koma gida zan bashi yanzu haka nayi tafiya wani gari zan kuma kwana biyu acan sai dai na koma din." Tace."To Kawu Allah ya dawo da kai lafiya." Ya amsa da "ameeen." Sukayi sallama cike da kaunar junansu..........Ajiyar zuciya ta dan sauke kanta a kasa, yanzu tana masifar kaunar kawunanta saboda ta gane yanxu sune gatanka........Hannunsa taji cikin nata yana saka mata wani abu, ta dago kanta tana kallonshi, tana kuma kallon hannunta, wasu takardune guda biyu ya saka mata cikin hannunta........Kallonshi tayi tana neman karin bayani.
Chapter 84 · 0% Book details