← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 37 OF 108

Sashe 37

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Harara ta watsa masa, "Wallahi Wasila tafi karfin wannan sadakin da kake magana akanshi idan kana so kasan wacece Wasila kaje ka sake sabon daurin aure kuma nice zan fad'i iya adadin kudin da zaka biyani na sadaki."

Ya kalleta da mamaki a tare dashi!! "Ke kina da ilimin addini kuwa."? Dauke kanta tayi....Yace." A'ina kika ta'ba jin mace ta yanke sadakin auranta da kanta? Shiru tayi masa, yace."Na lura kina da masifar son kudi......Me zaki dasu? nan ma ba tace komai ba, yace."Kar ki sake min magana makamaciyar wannan ranki zai 'baci! Sadaki na auranki na baki tuntuni, ke kika san yaya kika da kayanki kuma kin jawo sai na amshi sadakina yau dan haka ma ki shirya." Yana gama maganarshi ya sauka daga bed din yana tattare fuska yace."Malama ki shirya ki fito suna jiranki." Ta mike tana sake damke kirjinta dake daure da towel taje tana nemo kaya.........Super Holland ta dauko cikin kayayyakin da ya siyo mata, yana kallo ta wuce shi ta nufi toilet da kayan a hannunta, wai ba zata shirya a gabanshi ba da sauri ya tare mata hanya yace."In dai ba zaki saka kayan a gabana ba to zanja ki a haka na kai musu ke ." Ranta a bace tace"To wai me yasa kake takura min ne? yanzu sa kayan ma sai nayi a gabanka."? Yace."Kin mata da d'azu na gama ganin abinda kike 'boyewa to meye na damuwa.''?

Takaicinsa ne ya kamata! ta wuce ta barshi tsaye a gurin.....Babu yanda ta iya haka ta dinga kare karen jiki wai kada ya ganta tasa breziyya tana kokarin zura riga ya rike! taji tsoro sosai dan ba tayi tsammanin ya iso gurin ba, wuyan rigar ya shiga kana hannu guda ya shiga daya hannun ne bai shiga sanadiyar rike rigar da yayi!!!! Taga yana mata wani shu'umin kallon da ya kusa sanyawa ta zube a gurun! Ji tayi kafafunta na rawa, kafin ta ankara ya daga hannuwanta sama ya zare rigar! ya jefar manneta yayi a jikinsa ya zagaya hannunsa bayanta ya 'balle breziyyar ya jefar, ajiyar zuciya suka sauke a tare......Fatar bayanta ya shiga shafawa yana hadawa da kwantaccen gashin kanta, ta dinga jin tsigar jikinta na mikewa sanyi na ziyarta ta bata san sanda ta shige cikin jikinsa ba, ya sun jima a haka kafin ya d'ago fuskarta idanunta na rufe ya sumbaci le'bunanta ta bude ido a hankali ta sauke su a kanshi.....Murmushi ya sakar mata wanda ta kasa fahimtar ko na menene! Taji yace."Kiyi hakuri sai dare zanyi miki abin dazu yanzu kinga muna da ba'ki."! Kunya ce ta lullubeta sai tayi 'kas da kanta duk ta rasa ya za tayi, wai me yasa take saurin bada kanta ne gashi har ya gane ta daga ya ta'ba ta sai ta hau network! kamar mara lafiya haka ta zama sukuku! tana ji tana gani ya sanya mata breziyar da kanshi bayan ya gama lugwigwita nonowan sannan ya dauki rigar ya sa mata, mika mata zanin yayi yace."Wannan ne ban iya daurawa ba daura abinki."

Ta karba da mataccen jiki ta daura, tana ji kamar ta fashe da kuka ji take ta tsani kanta da kanta yanzu yanzu tagama cin alwashi kan sadaki amma gari banza ta bari yaga abinda take boyewa, ta dauki dankwalin ta yafa ba ta daura ba, yace."Kisa kwalli a idonki kamar ba amarya ba." Kamar ta gaura masa mari haka taji, zuciyarta sai zafi take, ya dauko mata kwallin ya bata, jefar dashi tayi....Ya daga kafada alamun bai damu ba, "Wuce muje ko."! yafada yana tsareta da ido, Simi simi tayi gaba, ya bi bayanta yana murmushi shi wataran ma idan tayi abu dariya take bashi a kwai kuruciya a tare da ita...........Dan sai-saita fuskarta tayi yayin da ta fito, kafin ta ankara Afnan ta tawo a guje ta ru'kun'kume ta tana fad'in" Aunty amaryata aunty amaryata ce."

*_'Yar Uwa yana da kyau a duk lokacin da ki kigama al'ada ma'ana jinin haila! Ki sanya miski ki goge gabanki kana ki dan goga zuma ki tsuguna a turaran suguno, sannan ki d'an sha kayan marmari, domin ni'imar ki ta dawo, duk lokacin da mace ta zubar da jini ko na haihuwa ko na al'ada ni'imarta na dan raguwa gurin na bushewa yana bukatar gyara sosai domin ki tar'bi mai gidanki da aka kwana biyu ba'a had'u ba🙋🏻‍♀️_*

Littafin na kudi ne......!
Kika futar min da book ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap number
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: 'Yr Bngr Sys
*34*
Rike hannun yarinyar tayi tana dan murmushi tare da fad'in"Oyoyo baby ya sunanki."? Afnan tace."Halimatu amma ana kirana da Afnan." Tace."Ashe ma mamana ce daga yau sunanki momy." Afnan tasa dariya tana fadiin"Laaa! Dadyna wai na zama momyn aunty amarya." hannunsa ta rike tana kyalkyala dariya murna take yi wai Wasila tace ita momynta ce....Yace."Eh mana tunda kikaji ta fadi haka da gaske take." Yarinya ta ruga a guje inda iyayenta ke zaune tana fada musu. 'Karad'in yarinyar ya sanya Wasila dariya, ta 'karasa inda suke a nutse tace"Sannuku." Khalifa yace."Sannu da fitowa gimbiya amarya ." Murmushi tayi kawai ta zauna tana kallon Hafsa dake kallonta tana murmushi, tace."Ina kwananku." Hafsa ta amsa tana dariya tace."Ai kin cancanki a kira ki da wadannan suna, amarya ya gida ya bakunta." Tace."Alhamdullahi, cikin ranta tana jin yanda famliy din Khalifa suka burgeta ta lura matarshi na kirki shima kuma ta lura yana da mutumci ba kamar abokinsa ba......Khalifa yace.''Ga 'kawa nan na kawo miki ku gaisa ku san juna Matata ce ga yarinyata anan Afnan duk naji lokacin da take gabatar miki da kanta."

Murmushi tayi tace"Afnan akwai karad'i Allah ya albarkaci zuria mungode da ziyara." Khalifa ya dinga mamakin hankali da nutsuwar yarinyar ashe duk kallon da suke mata na lalatacciya ba haka abin yake ba........Duk wannan gaise gaishen da sukeyi Ahamdu na can tsaye bakin window yana kallon harabar gidan nashi........Wasila ta kalli teble din gabansu ta taga ko ruwa babu, sai taji nauyi, ta mike a nutse tace"Bari na kawo muku ruwa ko."Hafsa tace "Mungode." kicin din ta nufa, Afnan tabi bayanta, tana fadin"Aunty amarya zan raka ki." Hannunta ts rike tace."To muje." Tana kokarin shiga kicin din ya juyo suka hada ido tayi saurin dauke nata ta shige kicin din da sauri shi kuma ya dawo inda su khalifa suke lokacin Hafsa na gulmar Wasila.....Khalifa yace."Gatanan tana gulma. Ya zauna kusa dashi Yana kallon Hafsan dake murmushi kunya ce ta kamata duk da ba wata mummunar magana ta fada kan wasilan ba.

Khalifa yace."Wai cewa takeyi amaryar yarinya karama kuma akwai karancin ilimi a tare da ita amma kuma tana da hankali." Murmushi ya danyi ya ta'be baki yace."Khalifa bana jin wannan yarinyar ta cika 20yeares fa, duka bata fi 17 ba, karatu kuwa dama ai ba'a maganarshi a gurinta, bana tunanin tana da takardar scondry School." Hafsa ta bude baki! Yace."Yes hakane mana ai babu nutsuwar da zata sanya tayi karatun....Hafsa tace."Allah sarki amma dai yana da kyau ta koma makaranta gaskiya magana matar governor guda ace bata da takaradar kammala karamar makaranta gaskiya akwai babban kalubale.

Yace."Hafsa ke kike tunanin wannan itafa wannan yarinyar a yanzu bata da wannan burin burinta shine ta samu hanyar da zata fita daga gidanan."? Tace"To a kan me."? Dake duk abinda ke faruwa ba tasa ni ba, khalifa na da amana sosai baya futar da sirrin abokinsa.

Share maganar kawai yayi shima saboda ya lura da cewar batasan abinda ke faruwa ba kuma bata san yanda akayi auran nasu ba gaskiya yana mutukar alfahari da abokinsa yana da sirri sosai matarshi ma bai yarda taji labarin ba.

Ta fito hannunta rike da wani madai-daicib tire da goran ruwa da lemo a kai sai kananun cups ta ajiye kan teble din tana fadin ga ruwa sannuku." Khalifa yace."Yawwa sannu amaryamu." Murmushi tayi kawai ta kama hannun Afnan suka nufi dakinta, ba tajin zata zauna in dai yana gurin a zaune..........Khalifa yace."A'a ya zaki gudu kuma." Karaf! yace."Kunya takeji wai ita amarya." Hafsa tasa dariya tace"Ai kunya halal ce! a gurin 'ya mace gaskiya mungode da tar'bar da akayi mana amarya." Ba tace komai ba ta bar suna ta surutu....Tana jin sanda yake fad'in"Ita wannan amarya bata da wata kunya dan ta ganku ne take sunkuyar da kai." Hafsa kuwa sai tare mata takeyi tana fadin "Sam! ba haka bane."

Afnan ta hau kan bed dinta tana tayi mata surutu da labarin skull dinsu ita dai jinta kawai takeyi, ta rasa wane tunani zatayi da ta sa'ka wancan sai ta kwance sam! wannan gidan ba gidan zama ba hankalinta har yanzu na kan harkokin siyarsar ta, taga sai wani gayyato mata mutane yake sai kace wata wacce tazo zama."

Sun jima suna hira dan sai da suka dauki kusan awa biyu tukkuna sannan suka niyar tafiya, har lokacin Afnan na tare da Wasila suna hira dan tun tana biye mata da surutun ta har tayi mata shiru itama ta gaji ta kwanta bacci ya dauketa....Ya shigo dakin ya same su kwance kan bed a tare ita Afnan din baccinta yayi nisa sosai itace dai take ta kokarin gayyato baccin yazo yaki zuwa.

Mikewa tayi zaune tana daura dankwalinta, ya tsaya kusa da ita a nutse yace."Yarinyar nan fa tun bata sanki ba, take zumudin ganinki gashi ta makale miki ya za'ayi ne momynta tace zata kwana biyu a gurinki kina ganin babu matsala ko."?
Yafad'i wannan maganar ne saboda kawai baya son shiga hakkinta idan taga zata iya daukar yarinyar shi bai da matsala,

Jim! tayi itafa bata so ta sha'ku da kowa ballanta hakan yazo ya dameta wane irin zama za tayi a gidan! da har za'a na'nika mata yarinya,

Domin kar ta watsa wa maman yarinyar kasa a ido yasa tace."Ni meye nawa a ciki gidanka ne fa, tayi zamanta." Yace."Eh ai nasan gidana ne ai kece matar gidan dole kina da hakki akai.'

Shiru tayi masa, yace."alamu sun nuna kin amince kenan? Kallonsa tayi ya d'aga mata girarshi guda tayi saurin dauke kanta gabanta na faduwa, yace."Ki fito zasu tafi sai kuyi sallama ko."
Chapter 37 · 0% Book details