← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 77 OF 108

Sashe 77

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Littafin na kudi ne....!
Kika futar min da book keda Allah kika karanta baki biya ba kema keda Allah What'spp numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*64*
Da sauri Uwani ta tare bakin 'kofar fita tana kallon Kuluwan cikin mamaki tace"Haba Kuluwa dubi yanayin da kike ciki babu suttura a jikinki kanki babu dankwali sannan kuma kike 'kokarin fita haka gaban siriki karfa ki manta mutumin nan babban mutum ne kamar yanda Kawu ya fada miki idan kin fita haka ai kin zubar mana da kima da mutunci ." Kuluwa ta hau ya'ke tana washe baki tace"Wallahi duk na manta babu riga a jikina Uban kudin dana gani hannun Malam su suka gigitani amma bari inje in sanyo riga ku jirani dan Allah." Da sauri ta koma cikin gidan jikinta sai rawa yake.....Wasila da Rashida suka bita da kallon mamaki matar mayyar kudi ce duk ta fita daga hayyacinta.....Kawu Madu kuwa na tsaye sai dariya yake yana ta dangwalar miyau a hannunshi yana lissafa kudin hannunshi, kamar zautacce ya kalli Uwani yace."Uwani kudin nan dubu hamsin ne wallahi! kai masha Allahu gaskiya naji dad'in zuwan mutumin nan Uwani ashe haka Allah yayi wa 'yar arziki amma saboda baki da hankali kika kashe mata aure, saboda kina mata bakin ciki, waye ya fada miki yanxu ana wasa da auran irin wad'annan mutanan? ai duk abinda ya faru ya fad'a min yanzu kafin na shigo sai ku godewa Allah da Allah yasa ya mai da auran dan da bai mayar da auran ba to da kun cutar damu wallahi dan wannan arzikin sai da mugani a nesa amma yanzu ko banza nasan zamu dinga samun zakka a kai a kai! idan Allah ya nufa ma wataran sai da kawai naji ance na fito an biya min kujerar makkah." Kawu Ya 'kare maganar tashi yana dariya had'e da gyara babbar rigarshi yana sake gyara xaman kudinshi a aljihu........Kuluwa ta karaso cikin wata kod'ad'diyar atamfa da wani ya mushashshen mayafi da duk ya tattare saboda tsabar yaga jiya da yau wai nan sune karshen adakarta, sai wani washe baki take ta kalli Uwani tace"Ai haka yayi ko."? Uwani dai shiru tayi dan bata da abince wa sam ma bata so Kuluwa ta bisu gani take zata iya yin wani abun na rashin hankali ita kuma bata so yanzu mutuncinsu a zube a gurin Ahmadu......Kawu ne yay gaba suka biyo bayanshi

A babban soron gidan suka tsaya Kuluwa sai l'eken kofar gidan take dan Kawu cewa yayi su tsaya anan zai shigo dashi Kuluwa duk ta 'kago sai d'aga kai takeyi tana lekawa.....Wasila taji tamkar ta gaura mata mari shin wai ita wannan matar wace irin mata ce mara kintsi da kamun kai.? 'Kamshin turaranshi ne ya bakuncin hancinsu gabad'aya, Uwani ta gyarq lullubinta hade da sunkuyar da kanta 'kasa kunyar hada ido take dashi sosai, Ita kam kuluwa fad'i take "Sannunku da zuwa Alhaji sannuku." Ahmadu da Khalifa suka samu gefe suka tsuguna a nutse aka fara gaishe gaishe, Ahmadu ya kasa tantance mahaifiyar matar tashi duk da ya ta'ba ganinta sau d'aya amma dai baya tunanin Kuluwa itace saboda yanda ta za'ke da yawa sai banbad'anci takeyi tana musu hirarraki Mikewa sukayi a tare Khalifa ne ya fara yin gaba shi kuma ya tsaya yana gyara rigarshi, kuluwa ta tsura mishi ido Kudi ya fito dasu daure a kyaure ya mi'kawa Wasila dake gefanshi a hankali yace."Ki bawa Momy ko." 'Kin 'karba tayi Kuluwa tayi wuf ta kar'be kudin tana washe baki da fad'in "Ai kunya ba zata bari ta kar'ba Alhaji Mungode kwarai Allah ya tabbatar da alkairi ya baku xaman lafiya." Uwani da Wasila ba suji dadin Abinda Kuluwa take ba, sai basu da yanda za suyi da ita......... Kuluwa da Kawu har bakin mota suka rakosu suna musu godiya da fatan alkairi, jama'ar garin sun taru suna mamakin irin bakin da Kawu Madu yayi, sai bayan motarsu ta 'bace daga gurin ne Kawu ya shiga yi musu bayani cewar Ai sirikin sa ne mutumin dake auran 'yar gidan Uwani 'yar 'kanwarshi.....
Uwani cikin gidan ta koma ta shiga daki ta had'a tagumi hawaye takeyi sosai takejin kewayar 'yayan nata amma ko babu komai zamansu a gidan Ahmadun sai yafi mata kwanciyar hankali fiye da su zauna a wani guri itama ta yarda mutumin nason 'yarta dan da baya sonta da bazai mayar da ita ba duk da tarin laifin da tayi masa.

Bayan azuhur suka sauka gajiya gami da jiri da zaman mota suka taru sukayi mata yawa, dan da kyar ma ta iya fitowa daga motar kafafunta duk sun sage sunyi tsami! Tana dan ya mutse fuska t

a rike hannun Rashida tana kokarin zama gefan shuke shuke! Ya fito daga cikin motar hannunshi rike da babbar rigarshi, Garba ya kar'bi rigar da wayoyinshi, hankalinshi na kansu yaga tana matse fuska cike da kulawa yace."Lafiya menene."? Shiru tayi mishi." Ya kalli Rashida yace."Ku shiga ciki mana karki bari ta zauna anan." Rashida ta kama hannunta suka soma tafiya, 'kafarta ta dama ce ta ri'ke ta kasa takuwa, ta rintse idanunta tana salati, dama tun a cikin mota takejin yanda cikin ke tattare mata yana dunkule mata guri guda, kwallah ta cika mata ido bakinta na rawa tace"Rashida 'kafana d'aya ta ri'ke gefan marata ya daure." Rashida tace"Ki daure anti wasila zaman mota ne yaja mu shiga ciki ka zauna sai in matsa miki kafafun naki." Yana tsaye suna magana da Garba yaga sun tsaya sai ya sallami Garba ya nufi inda suke.......Rashida na ganinshi tace"Wai kafarta ciwo take." Yace"Subahanallahi! to me ya jawo hakan."? Rashida tace "Nima ban sani ba watakila kuma zaman mota ne." Ya kalli Wasilan yaga tana kuka tana kokarin zama kasan gurin......Yace."Kada ki zauna anan mana tashi mu shiga ciki ki samu kiyi wanka sai ki kwanta ki huta."
Shiru tayi ta'ki tanka masa bala'in haushinsa takeji a ganinta ba kowa ne ya jawo mata wannan masifar ciwo ciwon ba sai shi.....Ganin tana had'a zufa a gurin rana na dukanta yasa ya sunkuya ba tare da yayi shawara da ita ba ya dauketa cak daukar jira jirai yayi mata ya nufi cikin gidan da ita......Duk da halin da take ciki sai da taji wani iri kunyar ma'aikatan gidan duk ta rufe ta tasan dai dole idan wasu ba sugani ba wasu zasu gani Uwa uba ga 'Kanwarta Rashida, rufe idanunta kawai tayi ta 'boye fuskarta cikin 'kirjinshi.....Rashida tabi bayansu tana sinne kai fuskarta dauke da murmushi sosai mutumin yake burgeta saboda irin kulawar da yake bawa 'yar uwarta.

Hajja tace"Subahanallahi! me ya faru haka."? Yace"Zaman mota ya sanya kafafunta tsami ta kasa tafiya dasu." Hajja tace"Aifa dama zaman mota ma ga mai lafiya babu dadi ballanta ga mai ciki sannu Wasila ka shiga da ita ciki tayi wanka sai suci abinci su huta.'' Baice komai ba ya shige da ita bedroom dinshi, kai tsaye bad ya kwantar da ita ya nufi toliet.

Mikewa zaune tayi a hankali tana d'an mikar da kafafunta wacce tafi takura mata da ciwo ta dan tasa kad'an! ta rintse idonta tana kiran sunan Allah can taji zillo a cikinta ta bude idanunta da sauri tana sauke ajiyar zuciya, yanzu zai isheta da kusurkusur a ciki idan ba abinci taci ba babu zaman lafiya.....Fitowa yay daga toilet din yana tattare hannun rigar dake cikin shi tayi saurin dauke kanta ya 'karaso inda take ba tayi aune ba taji ya dauketa, da sauri ta kalleshi ya d'aga mata girarshi guda, dauke kanta tayi tana zumbura baki kamar zatayi kuka itafa wannan za'kewar da yake a kanta sam baya burgeta taga sai wani rawar jiki yake mata tasan dai ba komai ya sanya shi yake mata hakan ba sai dan tana dauke da cikinshi.....A hankali ya dure ta tsakiyar bandakin yana mata wani munafikin kallo ya dora hannunshi a wuyanta, tureshi tayi ta jingina da bango (garu) gabanta ne ya soma faduwa, Ya sake matsowa kusa da ita, sai kawai ta saka kuka tana ture kirjinshi, cikin taushin murya yace"Wanka zanyi miki ba wani abu ba, ke kuka baya miki wuya ko."? Cikin nauyin baki da yanayi na gajiya tace"To ka barni mana nayi da kaina da can kaine kake min?" Ya shiga kallonta yana girgiza kanshi, yace." Daga yau nake so duk wata d'awainiya taki ta dawo hannuna ni mutum ne mai tausayin masu lalura irin taki, insha Allah mutukar ina gida zan dinga dauke miki dukanin laluranki har Allah ya saukeki lafiya."
Shiru tayi tana kallonshi anya kuwa zata amince da wannan dad'in bakin nashi? itafa tafi tunanin saboda cikin sa da take dauke dashi ne yasa yake rawar jiki a kanta.......Saukar hannunsa taji a bayanta yana kokarin zuge zuf din rigarta, ta dinga tureshi tana hawaye hakan be dameshi ba sai da ya cire mata kayan jikinta tas, ya kurawa cikinta ido da yayi kurcici a mararta, wata kwallah ce ta ciko a idanunsa, ya tsuguna gwiwa bibbiyu 'kasan toilet din ya dinga sumbatar cikin yana shafashi da hannunshi, Wann
Chapter 77 · 0% Book details