← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 47 OF 108

Sashe 47

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Wasila da Camas! suka fita ransu idan yayi dubu ya 'baci! Camas! tace"Wallahi nima nabar makarantar har abada shege dan iska kawai dama ya tsanemu." Wasila tace"Camas! zuciyata kamar ta fashe haka nakeji tsinanniyar nan tayi min asara ta kusan dari hudu gashi tasa an koreni.'' Hawaye ta share tana jin wata irin tsanar Suhairat cikin ranta.....Uwani najin labarin abinda ya faru tayi ta kutuntumawa! Suhairat ashar! tana tsine mata har da cewa sai taje gidansu ta ci mata mutunci." Wasila ce ta tausheta tace kawai ta bari ai taci ubanta tunda har sumar da ita tayi, to jin haka yasa zuciyar Uwani tayi sanyi.......To ashe tsugune bata 'kare ba, suna zaune da daddare sunyi tagumi babu abinci yunwa duk ta ishesu, sai ga sallamar dan sanda a bakin kofa......Itace ta le'ka sai kawai taga Suhairat a tsaye ita da wani saurayi da alama Yayan tane. Suhairat tayi saurin nuna ta tana fad'in "Itace yallabai." Kafin tayi aune! ya fito da ankwa ya kama hannunta ya daure! kallonsu tayi bakinta na motsi ta rasa me za tace! Yayan Suhairat yace."Sir me ake jira da itane." Dan sandan yace."Maza muje division sai kiyi bayani." Uwani da rashida suka fito suna ihu! da tambayar abinda ya faru, cikin rashin kunya Suhairat tace"Ki tambayi 'yarki." Wasila ta kalli Uwani tace"Ku daina kuka! Babu matsala kuzo muje." Uwani da rashida suka bi bayansu sai share hawaye sukeyi jama'ar unguwa na binsu da kallo.

Lokacin da suka shiga stion din D.P.O nan yana dube dube! ganin kyakyawan mata Uwani da yaranta sai ya dauki hankalinsa, yace."Maza kwanci mata wannan abun me yake faruwa ne." ? Dan sandan ya kwancewa Wasila Hannunta, sai kawai ta fashe da kuka tana fadin"Shikkenan D.P.0 daga anga mutum bai da gata a duniya sai ay ta tozartashi, Wallahi duk wanda ya cutar damu Allah zai saka mana." D.P.0 yace."Daina kuka kiyi min bayani." Zama tayi kan banci tace"Ai bani ce zanyi bayani ba gatanan a tsaye ita da yayanta." D.P 0 ya kalli suhairat da ita da yayanta yace."Kuyi min bayanin abinda ke faruwa, Suharait ta soma inda inda! D.P.0 yace."Daka gani kece baki da gaskiya ina ruwanki dan tana zuwa da kayan tallah ko kuma kece shugabar makarantar."? Suhairat tayi fiki fiki da ido! yace."Idan da hali ma sai nace ki bata tara tunda kin tozarta kin zubar mata da kayan sana'arta kuma kin sa an koreta daga makaranta, to amma a bayanin da kikayi min kince ta sumar dake to ai kece kikaja haka ina ruwanki da ita? Kije babu wani hukunci da za'ayi mata ke ya kamata ayiwa hukunci." Suhairat da yayanta jikinsu yayi sanyi simi-simi suka fita daga gurin....D.P.O ya kalli Wasila yana murmushi yace."Yan mata meye sunanki ne? saboda mutuncin da yayi musu yasa tace sunana Wasila nan ta bashi takaitaccen tarihinsu, ya tausaya musu sosai yace."Kada ki damu kinji ko, ni da kaina zan mayar daku makarantar ku zana jarrabawa tunda lokaci ya kusa, komai zai wuce." Ya dauki dari biyar ya basu suyi kudin mota.....Sai murmushi yake mata nan Uwani da ita kanta Wasilan su gane akwai alamun tambaya gurin D.P.O Yace."Gobe da wuruwri ku shiryo keda kawar taku kuzo nan ku sameni zan mai daku makarantar." Tace"To yallabai mungode." Sallama sukayi masa kana suka fito daga gurin hankalinsu ya kwanta su zuwa division din ma yayi musu dadi tunda sun samu kudin da zasu siyi garin kwaki suci dama yunwa suke ji.

A daran Wasila taje gidansu Camas! ta fada mata abinda ke faruwa, Camas ta dinga she'kawa Suhairat da wanta dariya tana fad'in"Wallahi Wasila ni na dade da sanin cewar kina tattare sa sirrika a tare dake ke d'in 'yar baiwa ce shiyasa nake so ki zage ki mori 'kuruciyarki kinga wallahi sana'ar karuwanci zata kar'beki tunda kina da duk wani abu da d'a namiji yake bukata a jikin 'ya mace, namiji mutukar lafiyayye ne shi ya kalleki sai yaji sha'awarki." Da jin irin maganganun da Camas! take masa ya sanya ta had'e rai! sosai tace"Kada ki sake min irin wannan maganar banzar idan ba haka ba kuwa wallahi zamuyi fada dake fadan da bamu ta'bayin irinshi ba , a duniya akwai abunda na tsana sama da karuwanci da har zaki dangatani dashi bana so kada ki sake, wannan budurcin nawa insha Allahu sai na kaishi dakin mijina."

To ganin yanda ranta ya'baci ne yasa ta dinga bata hakuri Wasila tayi tafiyarta ranta idan yayi dubu ya baci hakika taji bala'in haushin camas da irin maganar da take mata,

Tundaga ranar Camas bata sake yi mata maganar ba amma dai ita in ta samu wanda zasu sha minti ya latseta ya bata kudi tana yarda tun Wasila bata gane har dai tazo ta gane, ta dinga hanata amma taki dainawa kawai sai ta zuba mata ido.

Tun bayan komawarsu makarantar al'amura sukayi sauki dalili sun hakura da siye da siyarwa da sukeyi a makarantar sai suka dukufa gurin wanki da guga na mutanan dake unguwar tasu, idan kuma ta samu aikin wanke wanke gidajan amare taje tayi su biyata........Gaba mai tsanani ta shiga tsakanin Wasila da Suhairat tsakaninsu kallon banza ne da tsartar da yawu, amma basu ta'ba caccaar baki ba a tsakaninsu, har lokacin da Suhairat suka fita daga makarantar ta shiga scondry lokacin ita kuma Wasila da Camas Da salimat suka shiga aji shida, tsakanin Salimat da Wasila gaisuwa ce dan ita Salimat halin ta ba irin na 'yar uwarta bane Suhairat ita bata shiga abinda bai shafeta ba shiyasa ma dik gabar dake tsakanin wasila da Suhairat din bata shiga ba duk inda taga Wasila tana mata magana......Shigar su Wasila aji shida sai idanunsu ya sake budewa, sosai sunanta ya 'bace! daga Wasila mutane suka koma kiranta da 'Yar gaske.......Saboda yanayin da'kikancin su yasa suka fad'i a jarrabawa, su biyu ne kawai basu ci ba, Wasila ta nufi ofis tana kuka wai wallahi tayi kokari amma za'ace ba zataje scondry ba, Malam Isa shine suke dan shiri da ita, shine ya shiga ya fita ya sama musu makaranta 'yan mata ta *Sani mainage* Wasila da Camas! aka shiga socondry sai rawar kai ya 'karu, da 'yan matanci, lokacin kuma dama ana tashan balaga suka dinga tsula tsiya da rashin mutunci a makarantar, Lokacin jarrabawa nayi suka fad'i ! sunaji sunaji suna gani 'Yan ajinsu suka shiga Ss1 su suna js3 haka aka kawo 'yan 'kananun yara aka gwamutsasu! ba'kin cikin wannan yasa suka sallama makarantar suka hakura akan su tsaya wata shekarar ta zagayo, su ka daina zuwa makarantar gabadaya, Rashida na ganin sun daina zuwa itama sai ta nemi guri ta zauna alhalin ita tayi gaba sune a baya taga gwara ta hakura da karatun tunda babu su a makarantar......
*Wannan shine abinda ya faru a tarihin Wasila da ya shud'e!*

*Mun dawo labari*

Hajjah Babba tace"Da alama kun shaida junanku akwai alamun sannaya a tare daku." Salimat tace"Sosai kuwa Hajjah Tare mukayi pramiry da ita Sunanta Wasila Yahuza." Suhairat kusa wani irin mamaki takeyi da al'amarin ya akayi wannan 'kazamar yarinyar jahila 'yar tallah kuma 'yar bangar siyasa ra jagaliya ta samu nasarar auran Masoyinta??? Bata da me bata amsa dole sai ita wasilar sai kawai ta shiga watsa mata mugun kallo tana ji kamar taje ta sha'ke mata wuya dan takaici.

A nutse ta gaisa Hajja ta amsa tana tambayar ta jiki tace"Naji sauki tana wasa da hannunta, Ta gaishe da Aunty Kubra itama ta amsa babu yabo babu fallasa, itama ta shaida fuskar yarinyar, a cikin 'yan watannin da suka gabata ta ta'ba ganinta a tv tare da governor da mukarrabansa a lokacin da sukeje duba aikin titin Wuju wuju! shine tashar stv suka nuna su, tayi ta mamakin yanda akayi wannan al'amari ya faru to amma dai zata bugi cikin 'yar uwarta Hajjah taji ko tana da masaniyar akan yarinyar dan gaskiya duniya da mutanan dake cikinta basuyi mata shaidar arziki ba mybe ma domin su cimma wata manufa tasu a siyasance ya sanya suka shiryo wannan auran kuma suka yadauri Ahamdu din ya aureta dan su kasheshi ko su shirya masa wata ma'karkashiyar........... hira sukeyi wanda ita jinsu kawai takeyi so take ma taje ta kwanta dan har yanzu jikinta bai gama kwari ba, sai kawai taji muryar Suhairat na fad'in"Yaya Ahamduo ya akayi ka auri abokiyar adawarka ina ce itace Yarinyar data shiga gidan redio taci maka mutunci ta ta'ba martabar iyayenka kana kuma tayi maka 'kazafi na zinaaaa."! Dukaninsu suka mai da hankali kanta a lokacin da take wannan maganar..........
Chapter 47 · 0% Book details