Sashe 9
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Wasila tace"Karki damu malama muje tare zamu sanyaki a tsakiya ba zasu gane ki ba." Laraba tace."To ku muje." Kai tsaye suka durfafi kofar shiga gurin jami'an tsaron dake tsaye a gurin sukace su tsaya wani abu suka kara a jikinsu minti biyu sukace su wuce ciki.......Wasila da Camas! suka kama layi kamar gaske! Laraba kuma ta mike hanya dan isa inda yake tsaye..........Tana zuwa ta watsa masa kudinsa a jikinsa da karfi tace." *Bama so bama yi! wa 'yan nan 'yan kud'in naka basu isa su siyi kuri'armu bamu ba!.* Ai sai gurin ya kaure da hayaniya Garba da Hadi sukayo kan laraba Ahamad dake tsaye cikin dumbun mamaki ya hanasu dukanta, su kansu Police din dake tsaye a gurin Sunyi mamakin matar amma ya hana a ta'bata komeye dalili oho."
Ya Kalli Garba a nutse yace."Zo ka tsaya ka cigaba da raba musu." Garba ya tsaya inda yake shi kuma ya kalli Laraba dake tsaye jikinta yayi sanyi kalau yace."Baiwar Allah bance dole ki za'be ni a matsayin d'antakarar ki ba wannan kudin da nake raba muku duk karshen wata inayi ne saboda Allah ba da wata manufa fa ra'ayinki ne ki za'be ni ko ki za'bi abokin gamayya ta ni nasan ba zai iya siyan 'yanci ki ba nafi so duk wanda zai za'beni ya za'beni saboda Allah da kishin kansa da kuma 'kasarsa...."
Laraba ta fashe da kuka tana fad'in"Kagafarce ni yallabai! wallahi bayin kaina bane roman baka akayi min wata yarinya ce yanzu tayi min alkawarin zata bani dubu hamsin idan na aikata maka haka yanzu kuma wad'annan maganganun da kayi sunyi bala'in kashe min jiki don girman Allah ka gafarce ni."
Ahamd ya sauke ajiyar zuciya shi sam baiji zafin matar ta saboda yasan irinsu siyansu ake da 'yan kud'i kad'an! saboda an san shi talaka bukatarshi kudi ko ta halilin kakane zai iya siyar da 'yanci akan sabulu ko omo ko sukari.
Yace."Yanzu zaki iya nuna min inda yarinyar take."? tace"Kwarai kuwa Yallabai ai gatacan ma ta kama layi." Ahamd ya goya hannunsa a baya suka mike dogon layin dake jere da mata har suka inda su Wasila suke....."Gata nan Yallabai."! Laraba ta nuna Wasila dake tsaye fuskarta da ni'kabi.....Zatin ta kawai ya kalla ya gane ta ya d'an tsirawa idanunta kallo dake ni'kab itama ta sama ido suna kallon juna.....Ya d'an juya a nutse ya kira police yana karaso yace."Zura mata ankwa ka kai min ita cikin gida."
Camas! tace"Innallihi wa'ina ilahi raji'un! Jama'a me mukayi baiwar Allah me tayi miki zakice itace haka kawai dan sharri! Yalla'bai wallahi ba ita bace hasali ma mu yanzu muka shigo gurin kuma ai ba ita kadai ce mai niqab ba a gurin." Ahamdu ko sauraranta baiyi ba ya bar gurin.
Camas! ta dinga ihu! tana zagin Laraba Wasila ta dinga turjewa tana fad'in''Me nayi muku wannan sharri tayi min bani bace wallahi Police din yace."Wallahi idan bakiyi shiru ba zan fuxge wannan niqab din dake fuskarki in yaso kowa ya ganki munafuka kawai."
Jin abinda Police din yace ne sai ta daina turjewa saboda bata so ya cire mata niqab jama'a su ganta akwai tozarci sai kawai ta hau fuffukar 'karya da fad'in"Ai gaskiya daya ce kuma wanda ya zalinci wani Allah yana gani haka kawai saboda rashin adalci za'a sanya min ankwa sai kace 'barauniya ko kuma wacce tayi kisan kai!! kuma a haka ake cewa za' a iya mulki wannan ba adalci bane wallahi duk wanda ya shiga hurima na barshi da Allah."!!!
Dan sanda kuwa ya tasa 'keyar ta tana tafiya tana surutai da farfad'ar bakake maganganu masu harshen damo wanda wanda ake dominsa ya sani masu hankali ma a gurin sun gane da wanda takeyi....Angizata yayi cikin gate din yayi ya mayar da 'kofa ya rufe......Ta waiwaya bayanta babu kowa har masu gadi duk suna waje gefen bainci masu gadi ta zauna gabanta na fad'uwa sai yanzu jikinta yayi sanyi da al'amarin, dole ta cire tsoro da shakku a kan abunda zai faru ita dashi tayi al'kawarin ba zai ta'ba samun nasara a kanta ba.......Can ta hango shi ya fito daga wata iriyar kofa ta gilas ya durfafo inda take zaune gabanta ya dinga duka yana daka! mussaman ganin yanda fuskarsa take had'e tamkar hadarin da ya daf da zubar da ruwa.
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
_*Babu mahalu'kin da ya isa yayiwa mutum abunda Allah bai masa ba, bama nema gurin kowa! gurin Allah muke nema Allah ka yi mana ba dan mu ba*👏🏻_
~~~~~~~~~~~~~~
*Page d'in naku ne*
_HAUWA S ZARIA_
*(Mmn Uswan)*🌺
_MAMAN MAMY_
*(Shalele)*🌺
*Free Pege11*
Ganin ya kusa isowa inda takene ya sanya tayi maza ta yi 'kasa da kanta gani tayi ya kara wani kwarjini da kamala adduar neman rinjaye ta soma sai dai duk wacce ta dauka sai ta subce ta kamo waccen ma ta subce duk sakamakon tsayuwarshi a kanta ga masifar kamshinsa ya rikirkita mata lissafi.
"Cire wannan ba'kin abun na fuskarki." Yafad'a cikin wata iriyar murya.....Ta dago kanta tana kallonshi, "Kamar yaya na cir.....Kafin ta 'karasa ya fuzge niqab! din ya jefar, tayi saurin kauda kanta gefe.
Hannu ya mika yayi kamar zai juyo da fuskarta sai ya fasa yace." Juyo ki kalleni ina son muyi magana dake." Sai da ta dai-dai ta nutsuwarta tukkuna ta juyo tana kallonshi........Sun kai kimanin minti uku suna kallon juna kafin ta dauke kanta tana wani ya mutse fuska.
Gyaran mirya yayi a nutse yace."Ina so ki fad'amin nawa aka biya ki kika tsunduma kanki a wannan harka ta jagaliya ki fada mun ko nawa suka baki ni nayi miki al'kawari zan nin ka miki abunda suka baki ko sukayi miki alkawarin mutukar zaki dawo kiyi harkar ta siyasa mai kyau, da tsari!
Ta mike tana karkad'e hijab d'inta ta kalleshi ido da ido tace"Ni! bana jagaliya siyasa nake tsaftacciya kuma kai baka da kudin da zaka iya biya na kan wannan harkar."
Murmushi ya saki yace."Kina bani tausayi yarinya baki san waye Ahamdu ba ko."? Tace"Saninka ba zai amfana min da komai ba tunda nasan anayi siyasa ne da ra'ayi ni bana ra'ayinka kuma baka isa kasa ni na sauka daga a'kida ta ba.''
"God."! yafada yana tafa hannunsa ya kalleta da kwantaccen murmushi a fuskarshi yace." Gaskiya kin burgeni yarinya kuma ana siyance ana son mutum mai a'kida ni kaina idan da zan samu abokin tafiya irinki da naji dadin harkar ammafa ni yanda na dauka kin tsunduma kanki wannan harka ne domin cimma wata manufa taki.
"Kwarai kuwa akwai manufofi da nake dasu akan wannan harkar wanda ni kadai na barwa kaina su ina so kuma Allah ya cika min burika na."
"Masha Allah shin meye sane kuka daura tuntuninku akaina kuka tsawwala min sai kace ni kadai ne dan takarar Governor dake takara da governor ku me yasa duk inda nake kuna bibiyata da al'amurana saboda tsabar bin diddigi irin naki har gida kike biyo ni kina kokarin ci min mutunci shin wai me kuka dauki wannan harkar ne."!?
Wasila tayi shiru yace." Siyasa ba hauka bace! wad'anda suka san abunda sukeyi sunayi ne kan tsari amma ke naga kina so ki wuce gona da iri saboda talauci yayi miki katutu shiyasa kike ganin zaki iya zagin mutum kamar ni wanda yake da shekarun da suka nunka naki sau uku, okey nasan babu abunda ke damunki sai jahilci da rashin mafad'i to wannan shine lest winning na 'karshe kada! na sake ganin wad'annan kafafun naki a gidana duk ranar da kika sake kuskuran shigo min gida to a ranar ki kwana da shirin wad'anann kafafun naki ba naki bane dan sai na sanya an ragargaje su! in yaso sai naga kafafun yawon *Banga* ban hanaki ki zageni ba ko ki jefe ni kije kiyi tayi idan kin cimma burinki nasan zaki bari gidana dai ban lamunce in sake ganin kafafunki a ciki ba."