← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 38 OF 108

Sashe 38

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Mikewa tayi, ya juya baya yana tafiya kallonshi kawai takeyi sai wani magana yake mata yana dage mata gira kamar wani dan saurayi mutum da girmanshi da komai sai iyayin tsiya,

Su Khalifa na tsaye suna jiran fitowarsu, dukaninsu basuyi tsammanin Afnan zata zauna ba sai suka gansu sun fito babu ita, cike da mamaki! Hafsa tace"Ina Afnan din."? Ahamdu yace."Ina ruwanki da ita kuma yanzu." Rike baki tayi tace"Nifa duk wannan abin da nakeyi wallahi cikin wasa nakeyi ko kayanta daka gani saboda kar tayi min kuka ne yasa na had'o mata muzo dasu, amma ni nasan rigimar Afnan ba zata barku kusha ruwa ba a gidanan."

Khalifa yace."To nima dai haka nake gani amma dai shikkenan." Wasila tace"Kai don Allah ku kyaleta mana ai babu wata matsala bacci ma takeyi ai ni nasan ba zatayi kuka ba."

Khalifa yace."Shikkenan ai dama bamu ce komai ba." Murmushi kawai tayi tace"To ku gaida gida mungode.' Hafsa tace"amarya yaushe zaki kawo min ziyara ne."? Dan murmushi tayi takasa magana sai shine yace."Idan ta kwana biyu zan kawo miki ita amma bana son gulma." Hafsa tace"Kasan kuwa idan mun hadu sai munyi gulmarku." Yace."To na fasa kawo ta tunda d'abia mara amfani zakuyi." Hafsa ta dinga dariya tana fadin"saboda rashin gaskiya ba, ai da kafarta nasan zata zo inda nake mu kashe mu binne."

Murmushi kawai yayi bai sake cewa komai ba, suka nufi kofar fita a tare, Wasila tana tsaye daga inda take tana musu fatan alkairi da sauka lafiya.

Sai da ya tabbatar motarsu ta fita daga gidan sannan ya koma cikin....Parlo yay zamansa yana kallo da tunanin yanda zai kai kansa gurin yarinar da daddare baya jin zai iya daga mata kafa a yau din nan.

***
Camas! kuwa lokacin da ta bar gidan Wasila kai tsaye gidanta dake tishama ta nufa, lokacin su Uwani da rashida abin duniya ya damesu sun tasa lafiyayyan abinci a gaba sun kasa ci sai tunini suke, Da jin labarin da Camas tazo musu dashi sai hankalinsu ya kwanta, jin cewar Wasilan na cikin koshin lafiya gashi har ta bada sallahun a fada musu cewar tanan kalau kuma su kwantar da hankalinsu tanan fitowa ta cigaba da rayuwa a tare dasu, Uwani ce kawai taji dadin wannan magana amma ita Rashida sam bata sha'awar wasila ta fito daga gidan Ahamdu tana ganin Allah ya gama yi mata suttura tunda ya gamata da miji nagari kamar wannan bawan Allahn.

***
Camas! bayan ta bar gidan su Uwani sai ta wuce can getshouse din As wato Alhaji Tasi'u lokacin yana tare da baki sai da tayi jira tukkuna ta shiga.....Yana ganinta yace."Tuntuni nake saka ran zuwanki shiru da yanzu nake tunanin kiranki a waya.

Tace."Wallahi kuwa ai ina tafe na dan tsaya wani guri ne." As yace."Okey bani labarin yanda kukayi kin samu ganin Wasila.....Tace."Kwarai kuwa har mun shirya shawarar yanda za'ayi." Tiryan tiryan! ta fada masa yanda sukayi da Wasila da irin alkawarin da tayi kan in ta fito daga gidan Ahamdu to ya saka ransa cewar ta zama mallakinsa.

As ya dinga washe baki yana shafa sumar kanshi tabbas idan hakane to ko nawa ne zai iya kashewa duk dan ta samu nasarar fitowa daga wannan gidan....Yace."Yanzu abinda za'ayi shine ki bani accont numbar naki zan miki sending din kudi masu dan kwari, wanda zasu isa kuyi abinda zakuyi dasu, gaskiya naji dadin wannan labari naki dole ne ma nayi miki alkairi."

Camas! dadi ya isheta tasan As bashi da kwauro mutum ne shi mai sauki da dogon hannu har yaso yafi governor mi'kawa, itana wasilan duk da bazarsa take rawa, ta bashi account numbar dinta a take ya tura mata dubu dari hudu yace nata duba dari dubu dari uku kuma taje tabawa masu gadin gidan Ahamdu idan sunki amincewa ta dawo zai kara wasu.
Godiya tayi sosai sukayi sallama da juna, tare da sharadin gobe zata fara aiwatar da aikinta...

***
Tun yamma Hadari ke had'owa daf da magariba gari ya turnuke sosai da kura iska na tashi da ledoji.....Dai-dai wannan lokaci Afnan ta tashi daga baccin da ya dauketa tun bayan tafiyar iyayenta, Wasila da ta fito daga toilet ta ganta zaune a kan bed tana mutsika ido, tace."Afnan kin tashi." Yarinyar ta kalleta tana gyada kai...Tace."Kin sha bacci ko abinci baki ci ba tashi muje na rakaki kiyi brush baccin yamma bashi dadi ko kadan." Afnan ta sauko daga bed din suka nufi toilet Wasila ta matsa mata man goge baki a sabon brush, ta karba tana fadin"Aunty Amarya ina momyna da Abbahna."? Kai tsaye tace"Ai sun tafi tun dazu ke kina ta bacci." 'Dif! yarinyar tayi tana goge baki har ta gama wasila tace"To daura alwala muyi sallah sai kici abinci ko."? Daga mata kai tayi, Wasila ta kalli fuskarta taga babu walwala sam! bata kawo komai ba, ta mika mata, mayafin abaya ta yafa kana tasa hijab suka tada sallah.......Sanye da jallabiya ruwan toka ya shigo kanshi sanye da hular labarawa fara tas da ita ya saje sak da balaraban saudia....Ganinsu suna sallah sai ya zauna kan Sofa yana cigaba da jar carbin dake hannunsa.....Suna idarwa, Afnan tace"Dadyna! ina Abbahna." ? Ya kalleta da sauri yace."Ke! haka ake daga idar da sallahr babu addua sai magana." Rakykyakya'be fuska tayi sai hawaye shaaaa! ya bude baki cike da mamaki yana kallonta, hannu ya mika mata "Zo nan.! Taje ta tsaya tana goge fuska da bayan hannunta, Yace." Me akayi miki kike kuka."? Shiru tayi......"Ko auny Amarya ce ta dake ki."? Wasila tayi saurin kallonshi jin abinda yace....Afnan ta girgiza kanta..."Ni dai a kaini gidaaaaa."! Yarinyar tafada muryarta narawa still hawaye na zuba....Yace."Ai kinyi kad'an yarinya ba zaki bani wahala ba wallahi sai kinyi iya adadin kwanakin da kikace zakiyi sannan zai mai dake." Tsalle ta buga, ta hau kurma ihu! "Wayyo!! Abbana Momyna! ni gida zani ba zan zauna ba a kaini gidaa!!!! Hannunsa yasa ya toshe kunnansa, Afnan akwai lafiyar karadi sai kara take musu a kunne.

Wasila tace" Kiyi shiru mana kin fasa zama dani kenan ashe bakya sona Momyna." ! "Umum! ni dai a kaini gida bazan zauna ba." Tafada tana tsalle tana tumami!! hanyar fita ta kama a guje!! Yayi saurin rike hannunta, yarinya ta dinga kokarin fuzgewa tana kuka.....Ya kalli Wasila dake tsaye tana mamakin yarinyar ko da yake dama iyayenta sun fadi rigamarta ."Zo ki rakani na kaita dama na sani ai ba zama za tayi ba wahala kawai zata bani."
Tace"Afnan ba zaki zauna dani ba." Gyada kanta tayi tana kuka Yace."Kina batawa kanki lokaci ne kan yarinyar ba zama zatayi ba karshe ta hanamu bacci.'' Fita yayi da Afnan din tana ta kuka da kiran momynta, Wasila na bayansa da hijab dinta na sallah!....Ashe ruwa ake sosai kuma me karfi....Ya kalli Afnan din yace kinga ruwa ake ki bari ya tsagaita." Ihu! tasa! ni a'a ni momyna nake so." Ta dinga fada tana dukan fuskarta, Wasila tasa dariya da fadin"Lallai ma yarinyar kina kuka kina dukan kanki saboda tsabar masifa.

Wayarshi ya ciro ya kira Garba yace ya kawo mishi mota dai-dai kofar palor zai fit...Minti biyar motar tayi parking daukar afnan din yayi ya sa'ba a kafada suka fita, cikin gaggawa Garba ya bude masa mota ya shiga, ta shiga ta zauna...
Key din ya karba hannunsa, Garba yace."Allah ya tsare hanya." Hannu ya daga masa ya juya kan motar, suka nufi bakin gate....

Tun a mota ya kira Khalifa ya shaida masa abinda ke faruwa Khalifa ya dinga she'ka dariya takaici yasa ya kashe wayar yana rankwashin Afnan dake jikin Wasila sai faman ajiyar zuciya take.

Lokacin da suka isa gidan ruwan ya dan tsagaita, khalifa ya kirashi a waya da fadin"Fito ka dauki masifaffiyar yarinyar nan ta kusa kashe min kunne da kuka."
Khalfa yace."Ah haba dai ba zaku shigo ba." Yace."Ba zuwa nayi dan na zauna ba 'Yarku na kawo muku." Khalifa yace."Ai na bar maka ka juya da ita." tsaki yaja ya kashe wayar...Khalifa ya dinga dariya yana fadin"Dama afnan ce zata zauna a wani guri yasan dole hakan zata faru.

Tare suka fito da hafsa, suna dariya da jajanta al'marin shi dai bai ce komai ba, afnan na ganin iyayenta ta sauka daga jikin Wasila taje ta rungume mamanta, Hafsa tace"Amarya afuwa afnan bata kyauta ba wallahi ta taso ku cikin ruwa.
Dan mirmushi tayi tace."Ayya babu komai aikin yarinta ne ai.....Ahamdu kam juya motarshi yayi yana kallon afnan da fad'in"duk sanda nazo kika sake cewa sai kin bini sai na cire miki kunne! Makale kafada yarinyar tayi tana sauke ajiyar zuciya alamun taci kuka takoshi, Hafsa da khalifa dariya suke masa sun gane taji haushin abinda afnan din tayi musu, hannu suka daga musu har suka fita daga gate din gidan.

Suna fita babban titi iska ta taso gari ya sake rikewa sabon ruwa ya kece kamar da bakin kwarya ake sheka shi har da kankara irin wannan ruwan ne, yasa dole ake tsaida ababan hawa saboda gudun afkuwar matsala, sai ya samu gefan titi yayi parking din motar, yana fadin"Yarinya ta taso mu haka kawai cikin ruwa." Shiru tayi masa, ita tsoron ma titin take shuru sai uban ruwan da ake shekawa wanda take gani kamar zai tafi da motar.......Kimanin mintina goma a tsakani babu wanda yayi magana a cikinsu sai dai saukar numfashinsu a cikin motar....A hankali taji hannunsa kan nata, tayi saurin kallon jikinta, ya akayi har ya zura hannu a cikin hijab dinta ba taji ba, tasan ta kudundune jikinta da hijab dinta sabida sanyi amma sam ba taji sanda ya zura mata hanninsa a ciki ba......Ji tayi yana shafa tafin hannunta a hankali a hankali yana murza tsakiyar hannu...Tayi nufin kwacewa ya rike da sauri ta kalleshi suka 'Kurawa juna ido....Wani irin shu'umin kallo taga yanayi mata yana lumshe mata tsumammun idanunsa dake mugun kassara mata ga'ban jikinta....
Chapter 38 · 0% Book details