← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 11 OF 108

Sashe 11

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wata dan'kareriyar mota Alhaji Tasi'u yazo daukarsu Wasila matasan unguwa suka dinga zind'en Wasila da Camas! cewar ba harkar siyasa kadai suka tsaya ba harda karuwanci ganin irin manya motocin dake zuwa daukarsu, ganin irin shigar da Wasila tayi ta fito dashi ya sanya suka sake gazgata zatonsu a kanta tana sanye da wani material roba roba anyi mata wani irin dinki riga da siket ne sun matseta ga wuyan rigar daga baya a fafake! daga gaba kuma anfutar da gidan nono ya matseta sosai Wasila akwai hips da brest duk sun fito sun das duk lafiyayyan namijn da ya kalleta a lokacin sai ya d'arsa wani abun a ranshi gashi ta kawo wani siririn mayafi ta rataya a kafadarta hannunta sakale da jakarta mahadin takalminta kana kallonta zaka gane ta soma wankuwa idanunta sun bude tar! tar! sai taunar cingum takeyi.....Alhaji Tasiu yaji jijiyarsa ta mike ganin tsarin jikin Wasila ashe cika da 'kasaitar yarinyar ya kai haka babu shakka dole xaiyi mata kwance kwance ya dandana zumarta.

Gaban mota ta shiga ta zauna camas ta zauna a baya Kana Alhaji Tasi'u As na gomna ya tuka motar suka fuce daga layin yara na jifan motar da fad'in"Ba mayi! Kano ta d'an Musa ce wallahi.....Alhaji Tasiu yace."Na lura jama'ar unguwar nan taku basayin wannan gwamnatin tamu shin bakya musu hasafi ne kin san fa dole ki sake musu kudi sosai saboda ranar za'be! su fito su mara miki baya.

Wasila ta sauke ajiyar zuciya tace"Na rasa abunda mutumin nan yake bawa mutanan jahar nan wallahi in kaga yanda jama'a ke sonsa sai ka rike baki ni kaina wani sa'in idan na fito jifana sukeyi sai nayi da gaske tukkuna." Alhaji Tasiu yace."Ai yana da masoya gaskiya dalili kenan da muke so mu dakusar da duk wani shirinsa muna so mu kashe masa gwiwa kan harkar yaji kwata kwata ta fita daga ranshi." Wasila tace."Kar ka damu insha Allahu bukatarmu zata biya a kanshi.

Alhaji Tasiu ya biya tashar redio *Salama* kudi masu kauri yace."Tun yanzu su soma watsa wa cewar zasuyi hira da *Wasila 'Yar gaske* Yar partyn Lawan Rabo governor mai ci a yanzu." aikuwa kafin ma su bar cikin gidan redion sun soma sanarwa kan zasu hira da Wasila 'Yar gaske a filinsu na Siyasarmu da misalin karfe takwas na dare."

Tun a cikin mota Alhaji Tasiu ke yi mata wani irin kallo yana lumshe ido tana hankalce dashi kawai tana basarwa ne babu zato taji saukar hannunsa kan cinyarta....kici kici tayi da fuska tace"Meye haka kuma kar ka kara kuskuran ta'ba jikina duk mutumcin da muke da kai naga zaka keta min martaba ta mutuntaka to zamu raba hanya."

As ya soma yake yana sosa kai yace."Har yanzu baki gane inda na dosa ba kenan *Yar gaske* ki taimaka min rana daya ki mallaka min kanki." Ta watsa masa wani irin kallo, kankance ido tayi tace"As ina ganin girmanka da mutuncinka muyi harkar data hadamu da kai wato siyasa ni ba yar iska bace bana kuma shiri da mazinaci saboda haka kada ka kara yi min magana irin wannan duk ranar da ka sake to kam zan fadawa mai girma governor yayi min tsakani dakai ka kyaleni nayi sana'a ta kaje ka nemi 'yar iska kuyi iskancinku amma ni ba wannan na fito ba."

As yaji ciwon magangunta Wasila butuluce meye bai yi mata ba a rayuwa da girmansa da komai take fada masa irin wannan maganar.....Shiru yayi bai sake tankawa ba Ita taci kunu tana tauna cingum dinta jefi jefi tana amsa waya Camas na baya da tata wayar a hannu tana chating duk tana jin abunda sukeyi tana ganin idan da itace Wasila da gudu zata amince wallahi ai duk sana'a ce a wannan zamanin samun irinsu As zaiyi wuya kuma ta fahimci mutumin bashi da mugunta iya kudi yana sakar musu ya kaisu su dungo siyayya harda ta banza ya biya kudin kuma ya basu wasu ita kam idan ya nemeta zata amince masa da gudu.

****
Washe gari gidan redion *Salama* suna bude tasharsu da abunda suka fara kenan "Jama'ar gari da misalin karfe takwas da rabi na dare zamuyi hira da Hajiya Wasila 'Yar gaske a filinmu na Siyasa kowa ya kasance da redionsa a kusa dashi a dai-dai wannan lokaci domin yaji abunda yake tafe da wannan shahararriyar 'yar siyasar."

Gari ya dauka kowa na jiran lokaci......Labari ya iske Ahamdu ta bakin abokinshi Khalifa wanda yake mara masa baya ga dukanin harkokinsa tare sukeyi kuma shine a matsayin mataimakin shi idan Allah ya basu mulki a hannunsu.........Sam bai wani damu ba da jin wai zai ai hira da yarinyar a tashar redio ta *Salama* yasan dai zancan gizo baya wuce na 'koki shirme ne zasuyi tayi har su gaji su daina, Khalifa kuwa yasha jinin jikinsa jiran lokaci kawai yake yi.

***
Karfe takwas da rabi an soma gudanar da shirin *Siyasarmu*
Jama'ar gari na makale da redionsu da wayoyinsu.

Mai gabatarwa ya fara magana kamar haka....

"Jama'a yau filin namu na da babbar bakuwa Hajiya Wasila 'Yar gaske wanda tun kafin zuwan wannan lokacin muke ta sanar daku cewar zata shigo cikin shirin Siyasarmu domin ta warware mana zare da a bawa kan wata kullalan kulli dake faruwa a wannan jahar wanda jama'ar gari basu sanshi ba yau dai tace bari ta shigo wannan fili ta fasa 'kwan! kowa yaji ya san abunda ke faruwa 'yan takarkarin da suke gwabzawa guda biyu, masha Allah *'Yar gaske!* filin Siyasarmu ya shirya tsaf hakanan masu sauraro suma sun shirya suna sauraranki."

*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

*YABON GWANI YA ZAMA DOLE*
🕺🕺🕺🕺🕺🕺🕺

*PEGE DIN YAU KACOKAN! NAKI NE UWAR ARZIKI MACE MAI FARAR ANIYA DA FARAR ZUCIYA KINYI MIN KINA KAN YI MOMYNA FATIMA MUSA NIJAR ALHERIN ALLAH YAZO INDA KIKE DAKE DA ZURIARKI BANTA'BA MU'AMULA DA MUTUM IRINKI BA BANI DA BAKIN GODIYA A GURINKI MOMY ADDUA CE A TSAKANINA DAKE UBANGIJI ALLAH YA DUBA 'KARSHEN KI YASA KI GAMA LAFIYA ALLAH ABUNDA KIKEYI MIN ALLAH YAYI MIKI MOMY BAZAN TA'BA MANTAWA DAKE BA DOMIN KINYI MIN ABUNDA BAZAN MANTA DASHI BA NAGODE NAGODE NAGODE ALLAH YA AMFANI ZURIA👏🏻*
~~~~~~~~~~~~~
*Free Pege13*
Cikin zazza'kar muryata tayi sallama har da addua kamar wacce za tayi abun arziki...."Bisimillahi rahamanir rahim rabi sharali sadari wayasirli amri wa'alal u'kudatun millisani yaf'kahu 'kauli ameen ya Allah, to jama'a assalamu alaikum warahamatullahi ta'ala wabarakatuhu kamar yanda mai gabatarwa ya fada musu suna hakane nice Wasila 'Yar gaske 'yar partyn mai girma Governor Lawan Rabo governor da ba za'a ta'bayin irinshi ba insha Allah to a yau dai na shigo wannan filin ne domin nayi tankade da rairaye kana kuma na fed'e muku biri har hutsiyarsa, to jama'a hausawa nacewa yabon gwani ya zama dole dan haka kafin in fara cewa komai zan yabi maigirma Governor na saboda ya cancanta a yabe shi duba da irin dumbin ayyukan da yake a wannan jahar tamu......*A dad'e anayi sai gaskiya Engineer Turmi kake sha sassaka! Gugan 'karfe sha kwarafniya! kayi mun gani jama'ar gari sun gani sun shaida! mun shaida! A daka a bari dole uwar na'ki! ayi ayi a hakura kai d'in dai kaine duk inda akaje aka dawo sai kai!!! Engineer ma'kiyan ka! sai da su mutu domin ka riga kayi musu nisa sai dai kallo daga nesa! mu dai kaine gwaninmu kai muka za'ba jama'ar gari kai suka za'ba kawai dai 'yan adawa nayi musu romon baka da kuma al'kawaririkan 'karya! tare basu tsohiyar hanci domin a siyi kuri'arsu mu mun yarda da kanmu ba sai munyi kamfen ba insha Allahu babu canji da yardar Allah sai mun maimaita 4+4 Ba sauyi insha Allahu."
Ta kare maganar tana sauke nuffashi, Mai gabatarwa yace."Hajiya Wasila wannan yabon da kikeyi fa ni sai nake gani kamar kune kukeyi irinshi dan tuntuni jama'ar wannan jahar tamu suka dawo da rakiyar wannan gwamnati a cewarsu har yanxu basu gani a 'kas ba ance za'ayi mugudanar ruwa kana za'a saki wutar lantarki za'a biyawa yara kudin makaranta za'a gina sabbin makaranta da asibitoci da dai duk ayyukan da mai girma governor ya fada zaiyi kafin hawansa kujerar mulki shuru kakeji malam yaci shirwa wasu ayyukan idan an fara gadan gadan sai ajiye a shiga wata sabagar gashi yanzu har kunci shekaru uku akan wannan kujera babu wani sauyi da suka gani shiyasa suke ganin gwara su nemawa kansu mafita tun kafin dare yayi musu."

Wata siririyar dariya ta saki tace"Haba d'an jarida kasa kunne kaji da kyau!! Wallahi wannan gwamnatin ayyukanta daban suke dana sauran gomnonin da suka gabata haba Alaji ka duba babbar gadar da mukayi wacce ta fara tun daga farkon titi gwaron dutse bata tsaya ba sai da takai unguwar na'ibawa, wannan katuwar kwatar ta jakara mun rufe ta ruf! idan ana ruwa mutane hankalinsu akwance duk wannan fargabar da suke a da sun daina sai ka fada min wace gwamnati ce tayi wannan aiki."?

''To ai ba anan take ba 'Yar gaske sufa jama'ar gari suna magane akan al'kawarrikan da kuka dauka baku cika ko daya ba ba wai gada da aikin katuwar kwata ne ya damesu ba burinsu kawai suga ruwa da wuta kana kuma 'yayansu su samu ingantaccan ilimi har yanzu fa akwai makarantun da suke zama kan buhu babu banci da sauran abubuwan amfani kuma kafin hawanku wannan kujera kunyi alkawarin kan zaku inganta ilimin yara kana kuma kuyi karin albashi ga ma'aikata."
Chapter 11 · 0% Book details