Sashe 17
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Tunda ta kunna wayarta sa'konni ke shigo mafi yawanci daga abokanan harkarta ne maza sunfi yawa babu wanda ta duba a cikin messages din wayar dai kawai take latsawa tana ya mutse fuska, ita kadai tasan me takeji a jikinta har yanzu gabanta bai daina faduwa ba mutukar zata tuna da mafarkinta na jiya.....Kiran As ne ya shigo wayar ta sai da ta kusa katsewa sannan ta dauka suka gaisa yace anya zaki fito yau kuwa?
Ya mutsa fuska tayi tace"Yau dai zan huta a gida Gaskiya sai dai gobe." Yace."To babu laifi ko nazo na taya ki hira ne."? a ya tsine tace"Ina da abokanan hira ka huta kawai." Mara zuciya sai ya sake cewa "Okey anjima zan shigo zamuje musha iska." Tace."Ba damuwa sai ka shigo amma dai ka bari sai bayan sallahar isha'i." Yace."Haka za'ayi gimbiya." Hira suka dan ta'ba tayi masa sallama da fad'in zata kwanta bacci ba dan yaso ba ya hakura. Kashe wayar tayi tana tsaki....Camas! tayi sallama ta shigo palon....Taci uwar kwalliya da material mai uban tsada wani shegen dinki akayi mata mai fitar da tsaraici gashi bata sa mayafin kirki ba Camas an samu duniya har mota ce da ita sannan itama Alhaji Ma'aruf yayi mata alkawarin mallaka mata gida cikin gidajensa da yake ginawa.....Tace."Kawata ya yau dai duk na ganki babu kuzari ne na jima da zuwa government house ina jiran zuwanki sai yanzu As yace yau ba zaki fito ba sai gobe."
"Camas yau hutawa zanyi wallahi na gaji kullum kana cikin maza shegu suyi ta kare maka kallo wani ma yana sane zai zo ya gogi jikinka wai bai sani ba, na kusa daina wannan harkar tunda bukatata ta biya." Camas tace"Wallahi karki soma shin me na kasa yace ballanta ya bawa na sama me kika mallaka me kika ajiye a account dinki karfa ki manta yanzu lokacin da zaki sake zage damtse ki tatsi abunda kika tatsa wanda ko bayan mulki ya bar hannunsu kin samu kasonki me tsoka ai wallahi ni yanzu na fara har sai naga abunda ya turewa buzu nadi." Ajiyar zuciya ta saki a hankali tace" Duk da haka dai zan dinga daga kafa ba kullum zan dunga zuwa government house din ba, kina sane dai da kallon da jama'ar gari ke mana ko wasu fa karuwau suke daukarmu, na tsani ace min karuwa wallahi." Camas! tace" Sun dade basu kirani da karuwa ba abunda ya damesu ne idan kace zaka daka ta mutane sai su cuce ka.'' Shiru kawai tayi tana girgixa kai ta tsani a kirata da karuwa gwara Camas idan sun kirata da karuwa babu laifi tunda tana ta'bawa amma ita ba taji ba bata gani ba ana kiranta da kalmar da tafi tsana a rayuwarta.
****
*RANAR JUMA'A*
Su shida ne kacal a cikin motar Ahamdu Kawu Almu da abokinshi sai Khalifa da mahaifinshi Alhaji Iliyasu sai Garba dake gaban mota yana draving, kasancewar shine yasan gidan ya sanya zai jagoronce su.....Ahamdu da Khalifa suna sanye da kaya iri daya farar shadda ce kal dinki babbae riga da yar ciki hula iri daya agogo iri takalamsu iri daya hattata da links dinsu iri daya ne sosai idan ba fada akayi ba ba zaka bambance waye angon ba a cikinsu.
Can bangaran su Malam mai allo kuwa sun shirya tsaf dan tuntuni malam ya shaidawa limamin dake sallahar juma'a a babban massalacin dake garin cewar bayan an idar da sallah akwai daurin auren da za'a gabatar.......To lokacin da suka sauka garin ana ta shirye shiryen tafiya massalaci dan haka a gurguje suka daura alwala suka bi ayarin mutane ya zuwa masjid d'in.
Bayan liman ya gabatar da hud'uba kamar yanda addini ya tanada sai aka tayar da sallah........An idar da Allah anyi addua kana kuma aka shiga daurin aure.............Ana shafa fatiha Garba da Khalifa suka soma rabon alawa da goro gami da dabino cikin bakar leda za'a bawa mutum goro da alawa daurin aure yayi albarka jama'a sai addua suke gami da fatan xaman lafiya ga amarya da ango.
_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_
*Free Pege18*
Su Kawu Almu suka rufawa Ahamdu baya zuwa gidan Malam mai allo dake cike taf da dangi, katuwar tabarmar dake shimfide a tsakar gidan suka zazzauna aka shiga gaishe gaishe 'yan uwa sai tambaya sukeyo waye angon ne tsakanin Ahamdu da Khalifa.....Ahmadu yayi kasa da kanshi a lokacin sai ya tsinci kanshi da jin kunya duk da a zuciyarsa auran yayi shine da wata siga ta daban amma sai yaji kunyar mutanan mussaman malam mai allo dake ta kai kawo yana hidima da mutane kana ganinshi kasan yana cike da farin ciki....Khalifa ne ya dinga nuna shi yana fad'in"Gashi nan wannan ne angon bani ba.'' Tsoffin ciki suka soma yi masa d'an biki suna tsokanarshi da fad'in ya tsinci dami akala tunda ya samu nasarar auran Wasila saboda haka ya riketa da kyau dan ba karamar mace bace." Shi dai jinsu kawai yake yi yanayin yanda suke mu'amular su ya bashi sha'awa mutuka kuma ya lura suna masifar son su Wasilar halinsu kawai suke gudu, magana cikin magana suke masa hannunka mai sanda kan yarinyar kan yayi hakuri da halinta da dai sauraransu, sai ya kara jin jikinsa yayi sanyi da al'amarin auran yanzu kuma ya soma da ya sani tunda shi har cikin zuciyarsa ba da manufa me kyau ya auri yarinyar ba amma kuma darajar iyayenta na nema ta sauya masa tunani.
Lafiyayyan towon shika da miyar taushe aka kawo musu miyar taji manshanu gefe guda kuma ga soyayyan naman zabi nan fal katuwar silba......Babu wanda yayi wasa a cikinsu duka suka zage suka ci abincin dan tsabarta da kayatuwarsa tamkar a restaurant babu wata alama da zai nuna abincin karkara ne kwanika sabbi aka zubo musu dalili kenan da ya sanya suka saki jiki suka ci suka koshi suka kora ruwa mai sanyi irin na randa.
Bayan sun kammala sai suka shirya tafiya gida,Malam mai allo ya ke'be da Ahamdu yana masa maganar kan ya za'ayi da tariyar Wasilar Yace." Ya bar komai a hannunshi.'' Malam mai allo yace."Nida nafi so yau yau yarinyar nan ta kasance a dakinta bana so mu shiga hurumin ubangiji ya kasance muna wasa da aure, tunda an daura auranan to ta tare a dakinta barin ta haka sasakai zai janyo matsala babba tunda dai ita bata san halin da ake ciki ba.'' Yace."Tabbas maganar haka take malam babu damuwa insha Allah yau zata tare a dakinta kamar yanda ka bukata din." Malam yace."To bari in baka sadakin a hannuka ka mika mata da kanka tunda dai mu ba ganinta Zamuyi ba." Yace."babu damuwa Malam." ya ciro dubu biyar din ya mika masa ya sanya hannu biyu ya kar'ba, kana ya shiga yi masa godiya sukayi sallama cikin mutunci da mutuntawa.....Har bakin mota suka rakosu sai da motarsu ta 'bacewa ganinsu sannan suka juya cike da farin ciki sun auran da Wasila saura Rashida zuciyarsu wasai mussaman malam mai allo yana fatan d'orewar zaman lafiya ga Ahamdu da Wasila.
Cikin mota tunani kawai yake yi kan al'amarin duk ya rasa wane matsayi zai aje wannan auran nashi zuciyarsa na kawo masa shawarwari iri iri tabbas ko A lahira wani nacin albarkacin wani babu shakka yarinyar taci albakarcin dattijo malam mai allo a gurinsa, da ya dauki mummunar aniya a kanta albarkacin mutumin ya rage kashi tamanin daga cikin abunda ya tanadar mata amma dai duk da haka zai ba zai kyaleta ba sai ta gane bata da wayo......Haka suka isa gida tunani duk ya addabe shi yanzu ya za'ayi ma ya tunkari inda yarinyar nan take dame zai fara ne." ? Khalifa yace."Naga ka shiga tunani da yawa ka bari muje gida mu dan huta tunani ya dawo tukkuna nasan abunda ke damunka a yanzu amma aka bi komai a hankali mai sauki ne." Ajiyar zuciya ya sauke ya dan gyara zamanshi ya sake mai da idonsa ya rufe ba tare da yace komai ba.