Sashe 14
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Cikin girmamawa Ahamadu yace."Alhamdullahi naji dadi da hakan ta faru dama ni nafi so nayi magana baki da baki da mahaifin yarinyar dan haka Garba kana iya tafiya babu damuwa." Garba ya bar gurin yana godiya....Ahamadu ya sake mikewa Malam hannu suka sake gaisawa Yace."Malam kan maganar wannan yarinya ne Wasila.'' Malam mai allo ya kalli Ahamadu ganin nutsuwa da kuma a kamala a tattare dashi ya sanya hankalinsa ya kwanta yace."Alhaji ina fatan dai yarinyar nan ba wani laifi tayi muku ba dan wallahi dukkanin abunda takeyi bamu sani ba tunda bama tare dasu labarin abunda takeyi ne ya iskemu hakan ya sanya hankalinmu tashi, muka yanke shawarar zuwa domun mu tattara su mu koma can inda muke da zama dama kuma zamansu hakan bai dace ba a matsayinsu na 'yaya mata komeye zai iya faruwa da rayuwarsu.
Khalifa yace."Kwarai kuwa malam muma abunda muka hango kenan ya sanya muka sa ayi mana bunkice akan asalin yarinyar sai kuma Allah ya takaita mana lokaci guda kazo gari ashe ma ba a kurkusa kuke ba." Malam yace." Mu 'yan karamar hukumar Garko ne Yahuza mahaifin yaran ciki daya muke dashi mu hudu iyayenmu suka haifa ni ne babba sai Habibu sai shi Yahuza sannan kanwarmu Kattime To shi kadai ne ya tsalle a cikin mu ya tawo nan yake sana'oinsa har Allah yasa ya samu sana'a ya siyi gida kana yayi aure ya hayayyafa yanzu shekaranshi Takwas da rasuwa bayan karamar jinyar da yayi wanda muma sai labarin mutuwarsa mukaji......Dalili kenan da ya sanya nazo da kaina na dauke yaran har da ita mahaifiyar tasu na tafi dasu can garin namu ko sati daya ba suyi ba suka gudo........Tiryan tiryan Malam ya zayyane musu rayuwar dasu Wasila suka dinga yi tun farkon mutuwar mahaifinsu da irin rashin kunyar da mahaifiyarsu ke sawa suyi musu da yanda shi kuma yayi zuciya ya zare hannunsa daga kansu....Sai wannan karon da yaga abun yayi tsamari ya sanya yace bari ya dauki mataki na karshe kan abunda sukeyi.
Ahamadu yace."Arrama yanzu idan ka tafi dasu can Garkon kana da wanda zaka bawa auransu ne."? Malam yace."Ba za'a rasa ba Alhaji kasan shi auran karkara ba'a tsawwala da yawa insha Allahu sati biyu ba zasuyi a gida ba zab daura musu aure."
Yace."To idan babu damuwa ni ina son abani auran babbar kuma bana so a ja dogon lokaci idan da hali wannan juma'ar mai kamawa nake so a daure aure."
Malam yace."Alhaji da dai 'karamar ka dauka dan sai naga kamar tafi babbar hankali hankalin ka zaifi kwanciya da ita karamar." Yace."Kar ka damu malam shi aure ni'ima gareshi watakila ta sanadiyar auran namu sai kaga tayi hankali fiye da tunani mai tunani idan da hali a amince mun in bada sadaki na yanzu." Malam yace."To to ai babu damuwa nima zanfi jin dadin hakan kaga sai in koma gida da karfin gwiwa ta kuma in sanar da 'yan uwa abunda ke faruwa."
Ahamadu yace."Kwarai naji dadin yanda ka yarda dani ka amince min auran yarinyar da wuri ba tare da kaga waliyai na ba insha Allahu ranar juma'a zamu zo tare da kanin mahaifina Wanda shi kadai ne ya rage min a halin yanzu kasancewar nima tun ban kai matsayin wannan shekarun ba mahaifina ya rasu na rayu tare da yan uwansa wannan kuma da kake gani a zaune kusa dani abokina ne sha'kikina tare mukayi karatu kuma muke harkokinmu a tare insha Allahu tare zamu zo dashi ranar juma'a."
Malam yace."To masha Allah Alhaji ai ni ganin farko da nayi maka naji hankalina ya kwanta da kai wallahi babu d'ar! zan baka auran Wasila koda banga Waliyinka ba nasan zaka rike mun ita da kyau da amana, babu abunda zance sai dai ince Allah ya saka da alkairi saboda ka gama min komai tunda har ka yarda zaka auri wannan yarinya." Ahamdu yace."Babu damuwa malam, ai an riga an zama daya kuma Allah dai ya kara girma." Mikew yayi ya nufi cikin gidan..........mintuna goma yayi a ciki ya fito hannunsa rike da wata doguwar takarda dake cike da kudi." Ya mikawa malam na fad'in"Wannan shine sadakin Wasila malam."
Malam ya kalli uban kudin da ya mika masa sai ya girgiza kai a nutse yace."Ashe baka so auran yayi albarka ba Alhaji Annabi Muhammdu SAW yace."Mafi albarkar aure shine karamin sadaki wannan da yayi yawa duk da ban lissafa na gani ba amma idona ya gane min kudi ne masu yawa, saboda haka dubu biyar kacal zaka biya sadakin wannan yarinya."
Ahamadu yace."Malam ka ka'rba don Allah ai ba wani kudi masu yawa ba dubu dari ne kacal kuma kasan dai yanda kudin mu suke basu sa wani daraja kar damu insha Allahu aure zaiyi albarka."
Malam yace."Shi dai ba zai kar'bi wannan zunzurutun kudin ba a matsayin sadakin Wasila ya fiso idan yayi mata aure ta zauna mutuwa ce zata raba.....Ahamadu da Malam suka dinga ta'kardama da jayayya shi ya dage sai ya 'karba shi kuma yace ba zai kar'bi dubu dari ba dubu biyar zai 'karba....Khalifa ne ya raba gardama ya ciro kudi daga jikinsa dubu goma ne ya irga dubu biyar ya mikawa Malam yace."Ga sadakin Wasila daga Ahamadu." Malam ya sanya hannu biyu ya kar'ba yana fadin"Ubangiji Allah ya tabbatar da alkairi Allah ya basu zuria mai albarka." Khalifa ya amsa da "ameen rabbi malam muna godiya da karamci."
Ahamdu yaji haushin abunda khalifa yayi masa amma bai nuna ba sai ya aje takardar kudin kan teble din gabansa dauki wayarshi ya kira Garba......Garba na zuwa yace maza ya fito da mota ta zuba kayan abinci komai da koma yazo ya dauki malam ya kaishi har Garko Garba ya wuce da sauri domin aiwatar da aikin da aka sa shi. Ahamadu yace."Malam yanzu Garba zai kai gida maganar su Wasila kuma da kaina zan sanya a kai maka su har inda kake daga gobe jibi insha Allahu." Yace."To Alhaji Allah ya saka da alkairi ya biya dukanin bukatu na alkairi."
Bayan tafiyar Malam mai allo Khalifa ya kalli Ahmadu yace."Na lura wannan dattijon na arziki ne wallahi sai duk naji jikina yayi sanyi musamman yanda naga ya tsaya kai da fata akan ba zai kar'bi wannan kudin da ka bashi a matsayin kudin sadaki na fahimci yana so auranku da yarinyar yayi albarka wanda kai ba haka abun yake ba a zuciyarka, dan Allah ka kar ka watsa wa mutumin 'kasa a ido ka rike yarinyar nan amana ko dan saboda karamcinsa kamar yanda ka fad'a masa watakila ta sanadiyar auran sai kaga tayi hankali duk abubuwan da suka faru a baya su wuce kamar ba'ayi ba."
Shiru yayi yana nazarin maganar khalifa din yace."Nima jikina yayi sanyi lokacin da naga mutumin sam! ban dauka zanga kamilin mutum daga bangaran yarinyar ba ashe ta fito daga tsatso mai kyau gaskiya wannan mutumin ba duniya ce a gabanshi ba ka duba ka gani kudi a wannan zamanin sam basu gabansa wasu iyayen da suke so in kaje neman auran 'yayansu ka sakar musu kudi a gurinsu hakan burgewa ce, shi kuma na lura albarka kawai yake nema."
Khalifa yace."Shine ai shawarar da nake baka rike masa yarinyar shine zai sanya ya tabbatar da cewa kai d'in mutumin kirki ne.""
Murmushi yayi yace.''Kai nifa ina nan kan bakana wallahi! sai naci uban yarinyar nan wallahi in keta ta kuma in saketa."
Khalifa yace."Subahanallahi! wai me yasa kake hakane? ka sani kake takewa yanzu meye amfanin hakan da za kayi."? Sosa kanshi yayi yace."Ai kai dama ba za kaga amfani ba saboda ba kai akayi wa auran nan da zanyi zanyi shine da manufofi da dama kaga na farko zan tashi daga sunan Gwauro kamar yanda ta fad'a zata zame min garkuwata a siyance na biyu zan dawwamar da rayuwarta a cikin 'kunci da ba'kin ciki in takure ta guri guda in muzguna mata har sai ta durkusa gwiwa bibbiyu tana bani hakuri na uku kuma na taimake ta daga wannan yawace yawacen banzan da takeyi a gari tana zubda mutuncinta na killace ta a guri guda....Na hudu kuma auranta zai wanke ni daga zargin da tasa jama'ar gari suke min....Ita ta nufe ni da sharri ni na saka mata da alkairi kaga anan jama'ar suka ji labarin na aureta za tasha tofin ala tsine da zagi sannan ita da harkar Siyasa har abadah! na biyar bukatata ta biya na raba abokanan adawata da ita tunda yanxu kamar itace a matsayin yarinyar su wacce suke sanyawa nayi musu abu ba tare da shakkar kowa ba, nasan kafin su samu 'yar siyasa mai mutukar a'kida irinta za'a sha wuya, kasancewar siyasarmu ta yanzu ta zama sai a hankali duk inda mutum yasan zai samu nan zaije hakanan za kagansu yau su zagi wancan gobe su zagi wanannan sam basu da gwani mutum in dai zaka bashi na 'batarwa shikkenan magana ta kare, amma ita yarinyar ns fahimci ba wannan ke gabanta ta tsaya bangaransu su kadai shiyasa suka riketa hannu bibbiyu saboda sun lura abokiyar tafiya ce....Kuma kasan ba zasu ta'ba bari tayi aure ba zasuyi ta bata kudi tana shirme a gari rayuwarta ta lalace a banxa a wofi.''''' Khalifa yace."Kayi tunani me kyau gaskiya amma dai duk da haka don Allah ka sassauta mata idan ta shigo.
Murmishi ya saki mai dauke da manufofi da dama ta'be bakinsa yayi yace."Kana 'bata bakin ka ne khalifa yanda yarinyar nan tasa ni 'bacin rai itama ranta sai ya 'baci."
_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/18, 10:18 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_