← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 88 OF 108

Sashe 88

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Hajja da Inna hajara suna zaune a palo bayan sun karya Wasila na cikin daki tana kimtsa kayanta irin wanda ta samu masu uban yawa turaman atamfofi babu adadi ga uban kudin da bata san iya adadinsu ba, dan abokananshi kyauta kudi suka dinga yi mata wanda takasa irgasu ballanta tasan adadinsu, shi kansa khalifa kyautar kusan dubu dari biyu yayi mata tare da sit din akwati cike da kayanta dana baby Zahra......Ya shigo dakin cikin farin yadi anyi masa dinki irin na zaman gida, idanunsa sakaye da farin gilashi, tana ganin ya shigo dakin sai gabanta ya fad'i! ciki ciki ta amsa sallamarshi tana dan gyara kafafunta, ya karaso ya zauna kusa da ita yana nani'karta, kamshin turaransa ya bugi hancinta, ajiyar zuciya ta sauke lokacin da taji saukar hannunsa a bayanta yana tattare gashin kanta daya sauka a bayanta, kafad'arta ya rike sosai ya matso da ita jikinsa murya a kasa yace."Laifin me nayi ne aka daina shigowa gaishe dani da safe."? Dan turo bakinta tayi gaba! Ya sanya dan yatsansa kan le'banta na 'kasa yana shafawa cikin wani irin salo, kallonshi tayi da idanunta da suka dan soma sauyawa, ya dan daga mata girarshi guda daya da munafikin murmushi a fuskarshi.........ta mai da kanta kasa gabanta na faduwa kadan kadan......Cikin wata irin murya yace." To tunda ke kin kasa zuwa inda nake ni gani nazo kin san hausawa nacewa garin masoyi baya nisa duk inda kika shiga kika 'boye sai na biki." Shuru tayi masa ba tace komai ba, ya sanya hannunsa ya tallafo fuskarta suka kurawa junansu ido.....Wani irin zallan sonta ta dinga hangowa cikin kwayar idanunsa, ta dinga kallon kyakyawar fuskarshi wacce annuri ke sauka akai a take taji wani masifar kaunarsa na ratsa ilahirin jikinta.....Lumshe idanunta tayi gabanta na wani irin bugawa da karfi da karfi.....Tana jin sanda yake lasar le'bunanta yana dan tura harshensa cikin bakinta ta wani makale a jikinsa tana sake ri'keshi a jikinta, harshensa dake wasa dashi saman le'bunanta tayi gaggawar sarkafoshi dana ta shiga tsotsa da sauri da sauri tana shafa wuyanshi da saisayyar sumar kanshi...........

Littafin na kudi ne.......!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Wasap numbar
*07084653262*alliya:
'Yr Bngr Sys
*74*
Inna Hajara ce ta murd'a 'kofar dakin hannunta rike da baby zahra dake kukan yunwa tashinta daga bacci kenan tun bayan wanka safe da akayi mata bacci ya dauketa shine ta tashi tana kuka.....Inna hajara na fad'in "Ai dolene ki tashi da yunwa 'yar nan....kasa k'arasa maganar tayi ganin Amadu zaune a kusa da Wasila tayi fi'ki fi'ki da ido shi kuma ya sunkuyar da kanshi 'kasa kunyar duniya ta isheshi Allah yasa ma sunyi gaggawar sakin junansu lokacin da sukaji muryar Innan, to amma dai duk da haka inna hajara sai da ta fahimci wani abu tunda dai ai ita ba yarinya kankanuwa bace." A'lamarin ya bata mamaki sosai dan dukaninsu suna zaune a palo sam basu ga sanda har ya fito daga dakinshi ya shiga dakin ba, Karasawa tayi tana dan gyara fuskarta tace"Kar'beta ki bata nono kada ta soma wannan kukan nata kin san ba zakiji da dad'i ba." A sabu'le ta kar'bi yarinyar tana kokarin fito da nono.....Ya mi'ke tsaye yana dan gyara gilashinsa, ba tare da yayi kuskuran kallon innan ba yace."Inna antashi lafiya ya kwanan su Fad'ima." Inna Hajara itama dake ta iya duniyan ci sai ta maze kamar bata gane komai ba tace"Lafiyarsu kalau Alhaji ga Fad'imatu nan tayi wayo tubarkallah.'" Dan mirmushi yay yace."Allah yayi mata albarka." Inna ta amsa da "ameen." Yana fita daga dakin Inna hajara ta zauna kusa da ita fuskarta murtuk!!!! tace"Wallahi duk sanda na sake gani ya shigo dakin nan kin sakar masa fuska ya ta'baki sai ranki ya 'baci kwana tara da haihuwa har kin soma sakarwa miji jiki ke wace irin 'kwad'ayayya ce ne? ashe baki da wayo Wasila! ashe kin mance irin wahalhalun da kika sha kafin ki haihu shine sabida rashin kamun kai zaki saki jikinki har ya shigo yana tatta'baki ko."

Wasila ta kama kuka tana kokarin kare kanta Inna Hajara tace"Rufe min baki ni bana son shashancin banza da wofi! kefa da kanki kike fad'a min anyi miki d'inki a matuncin ki to har yaushe ya warke da zaki komawa miji shashasha mara wayo kawai."

Cikin kuka tace"Wai Inna me kika shigo ki kaga munayi kawai sai faman fad'a kike min ke baki shigo kinga munayin wani abu ba."! Inna Hajara ta kai bayan hannunta ta make bakinta tace"Dan Ubanki yarinya xaki mayar dani." Wasila ta kame bakinta tana hawaye.....Inna Hajara ta cigaba da sababi tana fad'i na shigo dakin na ganku makale da juna kuna tsotsa tsotse sannan ki raina min hankali."! Da sauri ta sunkuyar da kanta 'kasa tana mamaki ashe duk gaggawar sakin junansu da sukayi sai da ta gansu kai Inna hajara muguwar 'Yar sa'ido ce........Inna hajara tayi 'kwafa cike da takaici tace"Wallahi zan saka ido sosai a kanki duk ranar da na kara ganin kin sakar masa jikinki har kuna rungume rungume da tsotse tsotse to a ranar zan tattara nawa nawa nayi tafiyata tunda ke kin zama mara kamun kai da rashin kintsi.......Har yaushe akayi abun ? guri duk a d'anyace baiyi kwari ba amma saboda rashin hakuri irin naki ki biye masa ya cuceki a banza a wofi."!!! Cikin kuka tace"Ni Inna abar maganar dan Allah naji shikkenan zan kiyaye dan Allah kada ki tafi." Tsaki Inna hajara taja tace"Ai bana magana biyu na sake gani da idona sai dai ki nemeni ki rasa a gidanki." Tana gama maganarta ta fita daga dakin ranta dik a bace

Wasila kuka taci ta 'koshi ta share hawayenta tana cigaba da shayar da babynta tana tunanin abinda ya faru tsakaninsu itama fa ta hango wautarta gaskiyar Inna hajara haihuwar fari tayi, ya kamata ace ta kame kanta a guri guda gudun azo a haifi dan da bashi da ido tasan ita dashi duk basu da hakuri a wannan fagen, gashi kuma bata so Inna hajara ta tafi tilas ne ta kama kanta ko ya shigo ta daina sakar masa fuska, wannan ce sha'awar data yankewa kanta.

Hakance kuwa ta kasance kwata kwata Amadu ya daina ganin walwalarta ko ya shiga dakin ta dinga dauke dauken kai kenan idan ya zauna kusa da ita sai ta sauya guri idan ya dame ta tasa masa kuka tace dole sai ya bar dakin.....Abun da takeyi ya dinga bashi mamaki sosai ya soma jin haushinta yana dai daurewa ne, kawai baya so ya nuna mata fushinsa, ya kuma lura da yanda Inna Hajara ke zurga zurga a dakin duk sanda ta ganshi ya shiga da safe, dama da safe kawai yake

shiga kafin ya fita da daddare baya dawowa da wuri kafin ya dawo sunyi bacci sai ya wuce dakinsa kawai, shi ba yaro bane tsaf ya fahimci akwai saka hannun Inna hajaran gurin abinda Wasilan ke masa duk sai yaji zaman matar a gidanshi ya isheshi tunda ba abun arziki take sa'kawa ba.

*****
Yau kwanansu ashirin da shida kenan har ta soma sallah dan jinin biki da wuri ya dauke mata, tana kwance tana bacci dama 'ka'ida ne idan tayi wanka ta karya sai ta kwanta tayi bacci dan cikin dare ba sosai takeyi ba baby zahra na yawan tashi shan nono.........Cikin shirin fita ya fito daga dakinshi yana sanye da shadda fara 'kal da ita wacce kana ganinta kasan me tsada ce d'inki hannu ne na 'bakin zare wuya da hannuwa sai yay amfani da 'bakar Hula (dara) 'yar gasken mai gashi gashi a jikinta agogon dake hannunsa na dama shima 'baki ne na fatar damisa takalman kafarshi masu gidan ya tsa suma ba'kake sosai yayi kyau tamkar wani sauri dan shekara ashirin da takwas......Suka gaisa dasu Hajja da Inna hajara ya nufi dakin nata, Inna hajara idanunta a kansa tana so tagani idan taga ya jima bai fito ba tabi bayanshi.

Yana shiga dakin ya tarar da ita tana bacci tana sanye da wani material roba roba dinki riga da siket ne dama can kayan sun matseta ballanta yanzu da ta sake cika da cikowa irin ta haihuwa......A hankali ya isa bakin gadon ya d'an tsaya a kanta yana 'kare mata kallo.....Cikin baccinta ta dinga jin 'kamshin turaransa, bud'e idanunta tayi sai taga inuwarshi tayi saurin daga kanta tana kallonshi.

Mi'kewa tayi zaune tana mutsika idanunta, a hankali tace"Ina kwana."? Ya amsa babu yabo babu fallasa......mikewa tsaye tayi tana d'an jan rigarta da duk ta tattare tayi sama, ya bita da kallo tana kokarin wuce shi ya tari gabanta.
Sai ta 'bata fuska tana kallonshi......Shima fuska a 'bace yace."Me yasa kika sauya halinki? wane dalili ne ya sanya duk sanda na shigo dakin nan kike 'bata rai idan na zauna kusa dake ki sanja guri idan na rike hannuki ki saka min kuka meke faruwa dakene."?

Murya a sanyaye tace"Babu komai." Ya had'e ranshi sosai yace."Bana son 'karya ki fad'a min dalilin da ya sanya kike gudana ko zugaki akeyi ne."? Tayi saurin kallonshi......Yace." 'Kwarai kuwa ai da ba haka kike ba cikin 'yan kwanakin nan kika sauya d'abi'u dole ne nayi zargin ko zugaki ake."

Sai ta tsargu! ta dinga kallonsa tana son tayi magana! Sam bata so ya zargi Innarta dan tana so ya cigaba da ganin mutuncinta kamar yanda yake gani ba zata so ya gane cewar Inna Hajara ce ke zugata ba........Tace"Ni babu wanda yake zugani kawai dai ina ganin kamar be dace ba ace muna had'uwa a d'aki ni da kai saboda banyi ar'bain ba."

Ya dinga kallonta yana mamakin maganarta akwai kuruciya da rashin wayo a tare da ita, wannan maganar da takeyi sam bata da tushe ballanta makama kuma ba tunaninta bane, yasan innarta ce ke zugata.
Chapter 88 · 0% Book details