← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 22 OF 108

Sashe 22

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Yanayin parking ya fito hade da bude kofar da take tana kwance ruf da ciki kan site gashinta ya wargaje yayi buyaya lifayar ma ta cire dan saura kadan ta rabu da jikinta, Tsawa ya buga mata kan ta fito masa daga mota! shiru yayi ya sake kwatsa mata wata tsawar yaji shiru, sai da yayi magana sau biyar ba ta amsa ba, ya zura jikinsa cikin motar ya burkitota fuskarta ya tsirawa ido yana kallo....Idanunta a rufe ruf! dai-dai da gashin idon baya motsi! yaji faduwar gaba kadan ta kamashi Hannunsa ya dora a kirjinta minti biyu ya dauke! da sauri! ya kara hannunsa saitin hancinta nan ma yayi minti biyu babu alamun nuffashi a tare da ita....Babu shiri ya tattaro ta jikinsa ya taraiyaye ta daukar jarirai yayi mata ko motar bai rufe ba ya nufi cikin gidan da ita, hankalinsa a tashe.

*_TO JAMA'A NAN NA KAWO 'KARSHEN FREE PEGE NA WANNAN LITTAFIN GA DUK MAI BUKATAR CIGABA DA KARANTAWA SAI YA DUBA BAYANAN DA NAYI A SAMA KAZO KA BIYA KUDINKA KA KARANTA DOMIN KAR AYI BABU KAI WANNAN LABARI DAI YANZU MA AKA FARA AKWAI TAFIYA A GABA WANNAN D'ANDANAN GISHIRI NE..........HAR KULLUM INA FAD'A CEWA KUD'IN KARATU KIKA BIYA BA NA MALLAKA BA IDAN KIN YARDA KIZO KI BIYA KI KARANTA IDAN BAKI YARDA DA WANNAN TSARIN BA TO DAN ALLAH KAR KIZO KI BIYA KI FUTAR MIN DA BOOK KI RUSA NI KIYI ZAMANKI NAGODE SANNAN DUK MAI BUKATAR KARANTA NOVLS DINA AKWAI COMPLETED KAN FARASHI MAI SAU'KI KAR KU MANTA DAI HAUSAWA NACEWA SIYAN NAGARI MAI DA KUDI GIDA_*

'WADANNAN SUNE LITTAFAN NAWA

*NANA KHADIJA*
*YARO DA KUDI*
*GIMBIYA BALARABA*
*TSANTSAR BUTULCI*
*BABBAN YARO*
*LADIDI KWADAGA*
*MASHAHURI*
*SADAUKI OMAR*
*RUWAN DARE*
*NI DA YAYA SADAM*
*'YAR BANGAR SIYASA*

Kar ku manta da cewar ni Binta Umar Abbale nice mamalakiyar wad'annan novels din.....Saboda haka ga duk wani mai bukatar ya karanta completed dinsu sai ya nemi numbar ta ya biya ya karanta hankali kwance, Ina kara tunasar daku cewar kada kuje ku biya wani ko wata kudin wannan novels din dana jera muku 'karya yake 'karya take zasu siyar muku da hakkin da bana su ba kumai ba zama lallai su baku complete ba shikkenan sunci kudinku a banza, hanya mafi sauki anan ita ce ku tuntu'be ta wannan numbars din nawa
*08089965176*
*07084653262*

Masha Allah masoya sai naji ku🙋🏻‍♀️

[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: 'Yr bngr Sys.
*21*
Kan makeken bed dinshi ya shimfidata a gaggauce ya bude ma dai-dai cin firjin dake gefan bed din ya dauko goran ruwa mai sanyi ya bude murfin ya tsiyaya a hannushi ya soma yarfa ma a fuska, sai da yayi haka sau uku tukkuna ta sauke wata nannauyar ajiyar zuciya numfashinta ya dawo amma kuma idanunta a rufe ruf sai dai gashin idanunta dake motsi.....Tsayuwa yayi a kanta yana me 'karewa fuskarta kallo, Tunda yake da yarinyar bai ta'ba tsayuwa ya kare mata kallo ba irin yau! tana da masifar kyau! wanda sai ka dade kana kallonta zaka fahimta babu abunda yafi tafiya da hankalinsa irin karamin bakinta mai dan tudun le'be dai-dai sumba, bai san sanda ya tsotsi leb'anshi ba ya dan lumshe idonsa tare da sake budesu a kanta, karaf! suka hada ido lokacin ta bude nata idon yayin saurin dauke kansa yana dan ja baya daga kusa da ita.....Cikinta ta rike da hannuwanta tana rintse ido hawaye ya soma shatata! "Wayyo cikina wayyo cikina! wayyo cikina."!!!! Abunda take ta fad'a kenan tana matagugu kan bed din......Sai ya tsinci kanshi da kid'imewa ya zauna kusa da ita yana kokarin rike hannunta ta fuzge! da 'karfi! tana cigaba da murkususu da kiran cikinta.....Hayewa yayi bed din ba tare da ya sani ba ya rirrike ta jikinsa sai kyarma! yake " Menene! ina ne yake miki ciwo sannu daina kuka ko kin bugu ne."? Duka ya jero mata wannan tambayar lokaci guda.....Shiru tayi masa ta sane ta dinga kwanciya a jikinsa tana mutsika masa jikinta anashi tana kuka da kiran cikinta......Bai san sanda ya zura hannunsa cikin rigarta ba yana shafa kasan mararta muryarshi sanyi kalau! yake magana "Sannu daina kuka bari na duba miki magani ina kin buga gurin da jikin mota dole yayi miki ciwo mybe ma yunwa kikeji ko."? Ba tace komai ba sai aukin tureshi da takeyi daga jikinta yana sake rirriketa shi duk a tunaninsa da gaske take cikinta ciwo yake.....Ya mike da sauri yans fad'in" Bari na duba miki magani dare yayi yanzu da na kaiki an duba ki.''' Yana fita taja tsaki ta mike da azama! taje ta rufe kofar dakin tabar key din a jiki.....Komawa tayi ta kwanta tana sa'ka wacce zata fisheta.

Ya dawo dakin hannunsa rike da maganin ciwon ciki duk ya had'a uban gumi yana jan kofar yaji a kulle gam! gam!! Turus yayi da maganin a hannunsa yana tunani Babu shakka yarinyar nan yaudararsa tayi.....handle din ya sake murdawa yaji a rufe gam! gashi bedroom dinshi ne duk wasu abubuwan bukatunsa na ciki.....Wato tana so yayi mata magiya ta bude kofar shi kuma ya dauki alkawari kan sai dai ta gaji dan karan kanta ta bude tunda ya gane manufarta.....Wani bedroom din ya nufa ranshi a 'bace! amma yarinyar ta shammace shi gashi wayoyinsa na dakin hade da sauran makullan gidan.....Idanunsa suka sauka kan key din dake jikin kofar dakin da yake ciki....Da sauri ya mike ya isa gurin ya zare key din ya nufi dakin....Koda ya zura key din sai yaki shiga yayi yayi nan ya fahimci tabar key din a jiki. Ya juyo yana girgiza kai agogon bango ya kalla karfe daya na dare har da wani abu yarinyar nan ta hanashi bacci.....Idanunsa ne suka sauka kan pose dinta dake can bakin kofa yayi saurin isa inda take ya dauka tare da zama kan kujera yana budewa.....Wayarta babba da karama ce a ciki sai turaranta da wani zobe na gold a cikin gidanshi sai 'yan kudinta wanda basu wuce dubu takwas ba zuwa goma....Ya kunna wayar yana dube dube a ciki.

Tana kwance ta 'kurawa cilling ido tana tunanin yanda za'ayi ta kubutar da kanta daga hannun Ahamdu, ta mike zaune da sauri tana dube dube! sai yanzu ta tuna da pose dinta....Tsaye ta mike lifayar jikinta na hard'e tayi gaggawar cireta ta jefar a gurin babu ruwanta da yanayin kayan dake jikinta ta durfafi kofar futa.....Har ta murda kofar zata futa sai kuma ta fasa tsoro takeji kar ya ritsata ta k sanya kunnanta jikin kofar wai ko za taji alamun motsi taji tsit! a hankali ta murza key din ta ja kofar ta bude.......Yana zaune kasan kafet tsakanin kujeru shine dalilin da ya sanya ba ta ganshi ba sai ta fara dube dube a palon....Ya zuba mata idanunsa yana kallonta tar cikin jan 'kwan dake palon mai hasken tsiya.....Can yaga ta nufi bakin kofar futa domin anan take tunanin ta yar da Pose din nata....Ya mike a hankali ya iske inda take hannunsa rike da pose din nata....Tana juyowa suka buga karo goshinta ne ya daki kirjinsa......Tayi masifar razana!!! da sauri tayi nufi guduwa ya tare ta tare da matseta a jikin labule......." 'Kas tayi da kanta kunya ta isheta sai yanzu ta fahimci a yanda ta fito tama manta shaf da kananun kayane a jikinta.

"Kallonta kawai yake yi ya ma rasa abunda zai ce mata sai bin sasan jikinta yake da kallo yana ayyana abubuwa da dama a kanta.

Pose din dake hannunshi ta zubawa ido....Ya dage mata gira tare da fad'in" Kin bude kofa ne sabida kizo ki dauki jakarki ko."? Tayi shiru yace."Kin yaudareni da ciwon ciki kin kulle min daki....Daga taimako sai sharri ya biyo baya kinga dake bani da alhaki a kanki da kanki kin bude kofar wai ke me wayo ko? Okey jakarki gata a hannunta zan baki abarka amma zan dauki abu biyu a ciki."

Hannu ta kai da sauri zata fuzge! yayi sama da jakar yana kallonta sai d'age! takeyi Yace."Ki daina wani wahalar da kanki Ba komai zan dauka ba a ciki illah wayoyinki dukaninsu babu ke babu amfani da waya sai kinyi hankali."

Ido ta zare! hannunta na kyarma sai rirrike hannunsa takeyi tana so ta fuzgo pose din....Dariya ta bashi ganin yand ta dage tana d'age! 'kafafu Ya d'an ture ta daga jikinsa yana matsawa, Biyo shi tayi muryarta na rawa "Allah sai ka bani waya ta." Abunda take fada kenan tana rirrike masa riga....Ya 'bata fuska da fad'in"Idan ba ki daina tatta'ba min jiki ba sai na 'bata miki " Wallahi kinji na rantse ke da wayar nan har abadah sai nayi niyya nan gaba na yarda da hankalin ki sannan zan yarda ki rike waya."

Dajin wannan magana tashi sai ta fashe da kuka" Wallahi ban yarda ba haka kawai zaka takura min ka shiga rayuwa ta kace ba zan rike waya ba, Idan ka cuzguwa rayuwata nima sai na cuzguna maka kuma na fada maka wannan auran dashi da babu duk daya suke a gurina Gwara kawai ka sallame ni naje na cigaba da harkokina."

Ko kallonta baiyi ba ya cire mata agogonta da turaranta ya ajiye mata kan kujera ya nufu bedroom dinshi yana fadin"Wahala ce bata isheki ba yarinya sai kiyi tayi ke kadai, Ahamdu bashi da lokacin ki." Yana shiga dakin ya murza key ta tsaya jikin kofar tana bugawa ya share ta kawai ya kwanta bed din shi tare da rufe ido bacci yake ji sosai bayan haka kuma ga gajiya ta dabaibaye shi......Tun yana jin bugun kofarta sama-sama har ya daina ji bacci yaci karfinsa.......Itama da ta gaji da dukan kofar sai ta silale kofar dakin tana kuka da kiran sunan Allah shiru palon tsoro da farga duk ya isheta haka dai tayi kwance bakin kofar dakin ga sanyi Ac yayi yawa a palon tsoro ya hanata taje ta rage, Yanda taga rana haka taga dare domin a kunnanta aka soma kiran assalatu.

Kika futa da book din nan na barki da Allah kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar
*07084653262*
Chapter 22 · 0% Book details