← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 79 OF 108

Sashe 79

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

A can gest house din nashi Khalifa ne tare da Alhaji Muktari daura dan takarar governor jahar katsina ya kawo masa ziyara tare da dashi da mu'karrabansa, dake jam'iyarsu daya shiyasa suke zumunci kuma kusan halinsu yazo d'aya da juna, Alhaji Muktari ya ta'ba zama governor a jahar katsina yanzu yana so ya maimaitane yana kuma so ya karya al'kadarin governor dake ci a jahar tasu mai suna Engineer Haruna Haruni mutum ne mugu wanda yake mulki bisa zalinci halinsu d'aya da mai girma governor Lawan Rabo governor dake ci a jahar kano, duk wani 'kulla 'kulla gami da cuta da zalinci tare sukeyi dan duk abinda Lawan Rabo yayi a jahar sa to lashakka Haruna haruni shima sai yayi a tashi jahar, Wannan dalilin ne ya sanya Alhaji Muktari zuwa gurin abokin nashi domin su shawarta abubuwan da zai amfane su ya kuma amfanin al'ummar jahohinsu...............Tunda Governor Lawan Rabo ya samu labarin zuwan Alhaji Muktari garin sai ya dami kanshi, sosai ya kira Abokin nashi ya shaida mishi abinda ke faruwa, Haruna Haruni yace." Nasan ba zai bar garin ba tilas sai shigo ku gaisa kada ka nuna masa komai kamar yanda suke abunsu a lullube muma zamu bisu a haka, ai yanzu ya'ki d'an zamba ne muke kan kujearar mulki sai munso wani zai hau ka daina tayar da hankalinka kan komai kuma Amadu ya daina firgitaka, komai fa na hannuka a yanzu koda Amadu ne ya cika za'be sai munyi juyin mulki ballantana kuma muna da mai matacciya wannan maimai d'in ko sun so ko sun'ki sai munyi idan zaka shigo katsina ka shigo a shirye domin tilas ma a wannan karon mu kauce hanya mubi matasan yaran nan a sannu su samo mana 'kananun yaran da zamu bawa mai matacciya yayi mana aiki a kansu, tabbas dai nasan baka mance abinda ya faru ba a shekaru uku da suka gabata." Lawan Rabo ya sauke ajiyar zuciya yace."Tilas shawararka ita

ce abun dauka a gaskiya yanda naji dad'in wannan kujerar zai yi wuya na barta kai tsaye kai ni ko da d'an da na haifa za'a bu'kata zan iya badashi tunda dai nasan ai ba gama haihuwar nayi ba.'' Haruna haruni yace."Haka ake son cikkaken namiji jarumi me a'kida, kada ka damu idan Muktari ya shigo fadar gomnati ka kar'beshi hannu biyu zamu 'bullo musu ta bayan fage, mulki dai sai dai suga anayi insha Allah duk jama'ar da suke dashi sai ta dusheshe ranar za'be mune zamu lashe." To Wannan maganganun da sukayi ne ya sanya Governor Lawan Rabo kwantar da hankalinshi kamar tsumma a randa, ya tabbatar suna da ya'kinin akan cewar mutukar bokan da yayi musu aiki da 'kuk'onan kawunan yara yana nan a raye cikin duniyar to sun tabbata sai sun watsa shirin su Amadu da Muktari

Amadu na isa gest house din nashi Alhaji Muktari ya soma tsokanarshi da fad'in "Da har ina cewa bari mu tafi tunda dai mu gaisa da Khalifa ya isa kai sai ayi maka uziri tunda kana tare da Uwargida." Amadu ya zaune kan kujera yana murmshi hularshi ya cire yana kallon Khalifa yace."Nasan wanda ya fad'a maka cewar ina tare da Uwargida" Khalifa yace."Nine na fad'a mishi da kayi zamanka ma yayi maka uziri ko bakaji abinda yace bane." Murmushi yayi yana girgiza kanshi yace."Uwargida bata da 'koshin lafiya me kuke tunanin za'ayi."? Alhaji Muktari ya bashi hannu suka tafa suna dariya a tare Yace."Yana da kyau dai muje na dubata kafin na wuce, dan Khalifa yanzu yake shaida min an samu 'karuwa to Ubangiji Allah ya raba lafiya." Amadu yace."Ameeen ya rabbi, yace." Khalifa ya fad'a maka na samu 'karuwa shi bai fad'a maka tashi 'karuwar ba.''? Alhaji muktari ya kalli khalifa da son jin 'karin bayani." Khalifa yasa dariya yana kallonshi shima Amadu yace."Shima iyalinshi juna biyu gareta." Alhaji Muktari ya shiga girgiza kanshi yana kallonsu da fad'in "Gaskiya mutanan nan bakwa wasa." Khalifa na dariya yace."Bama wasa ko dai baka wasa Alaji matanka biyu 'yayanka shida ai kaine shugaba gwara mu da mace daya muke zaune." Alhaji muktari ya dan tura hularshi 'keya yana gyara zamanshi yace." Ai mata biyu shine jin dad'i Alaji sai ranar da kukayi zaku gane haka.'' Amadu dai murmushi yake yace."Duk mutumin dake da mace biyu bashi da kwanciyar hankali Alaji bana jin zan iya had'a mace biyu a gidana in dai ba Allah ne ya 'kaddara ba."

Khalifa na d'auke da murmushi a fuskarshi yace."Ni kam ina tsammanin had'a mata biyu anan gaba dan gaskiya ina da ra'ayin yin hakan." Alhaji Muktari ya bashi hannu suka tafa.....Amadu kuwa kallonshi yay da mamaki a fuskarshi yace."To tunda ka tona asirin ranka sai na fad'a mata kasan ni da Hafsa akwai amana ba zan yarda kaci amanarta ba."

Khalifa yasa dariya yana fad'in "Kafi tsuntsu gudu dan Allah! haka kawai Allah da annabi sun halasta min ace kada nayi, Kasan Allah idan lokacin aurena yazo dole ne Hafsa tayi hakuri dan ina da wannan niyyar." Amadu ya dinga girgiza kai yana kallonshi, shi kam a nashi ra'ayin bai son had'a mata biyu ko sama da hakan a ganinshi duk damuwa ce mutukar matarshi zata dinga dauke mishi dukanin laluranshi bai damu da lallai sai yayi wani auran ba koda kuwa ya samu mulki a nan gaba.

Tattaunawa suka shigayi da sabbin tsare tsaren da zasuyi mutukar Allah ya cika musu burinsu akan abinda suke nema mutukar sun samu nasarar d'arewa kujerar mulki to babu shakka Al'ummar jahar kano da katsina zasuyi farin ciki zasu ga sauyi ta ko wanne 'bangare

Misalin 'karfe tara da rabi na dare suka fito daga gest house d'in Alhaji Muktar yace yana so ya duba Wasila kafin ya koma dan gobe da asubah yake so su wuce, To dan kar ya watsa masa 'kasa a ido ne ya sanya ya amince da bukatarsa, saboda baya son abinda zai sanya girma da mutuncinsa ya zube a idonshi, baya so suje gidan Yarinyar tayi wani abun wanda zai nuna babu jituwa a tsakaninsu domin har yanzu ya lura da ita bata wani saki jikinta ba sosai.

Goma shaura motarsu ta shiga cikin gidan garba nayi parking ya fito cikin sauri ya bude musu kofa suka fito, tare suka nufi cikin gidan dukaninsu harda khalifa.

Rashida ce ita kad'ai a palon tana kallo Hajjah tuni ta shige daki ta

kwanta dan tanayin sallah isha'i take kwanciya, Wasila kam bata jima da barin palon ba itama wanka ta shiga tayi ta kwanta dan har yanzu jikinta bai dawo dai-dai ba akwai sauran gajiyar hanya

Rashida ta mi'ke tsaye tana musu barka da zuwa, ta gaishe su a nutse tana kokarin shigewa Har zai yi mata magana sai kuma yaja bakinshi yayi shuru ya kalli Abokan nashi a nutse yace."Bari na fito da ita." Khalifa yace"Kada kayi wannan dad'ewar da ka saba." 'Karamin tsaki yaja ya yana girgiza kanshi ya tura kofar dakin ya shiga wanda yayi dai-dai da lokacin da ta fito daga toilet jikinta daure da towel iya cinyarta.....Sallamar dake dauke a bakinsa ce ta gagara fitowa, da kyar ya janyo dauriyarshi da jarumtarshi ya shiga dakin, 'Dan tsayawa tayi tana kallonshi tana turo bakinta gaba, shiyasa ta'ki shiga dakinsa ta gudo nata ashe bata tsira ba yazo zai takura mata, 'Bata fuskarta tayi ta wuce a hankali taje ta zauna gaban mirror tana bud'e man shafawa

Bayanta ya tsaya yana kallonta ta cikin mudubin tana shafa mai a hankali tana shafawa a hannunta, ba tare da yace komai ba ya sanya hannunshi cikin vasilin din ya soma shafa mata sassan jikinta, jin saukar hannunsa a jikinta ya sanya ta sauke ajiyar zuciya me tafe da tashin tsigar jiki, hannunsa ta cire wanda yake kokarin cusawa cikin towel din ta sake daure kirjinta dashi, bai ce mata komai ba, ya dan rankwafa a hankali ya d'an ja 'kafafunta ya soma shafa mata vasilin din a cinyoyinta da kafafunta.......Ido ta tsira mishi yayin da kanshi ke 'kasa, taji wata 'kwallah na kokarin zubo mata daurewa tayi ta dauke kanta da sauri lokacin da ya dago ganshi, bayan ya gama shafa mata vasilin din, Ta mike tana sake rike daurin towel din a kirjinta wardrobe ta nufa ya bi bayanta, kayan bacci masu taushi ya dauko ya rike hannunta a hankali yake kokarin kwance towel din, tasa kuka tana tureshi, ya mi'ka mata kayan da fad'in "Kiyi gaggawar sanyawa tunda baki so nasa miki akwai 'baki na jiranki a palo abokina ne yazo duba jikinki.'' Cikin rawar murya tace" Ni ka fita to nasa kayan zan fito yanzu." Harararta yayi yace."Meye abinda zaki 'boye min a jikinki ? wai ke dan Allah yaushe zaki daina wannan 'kauyancin ne? Shiru tayi mishi ta nufi bed da kayan a hannunta, zama tayi gefan gado ta soma zura dogon wandon tana kare cinyoyinta da towel, shi dariya ma take bashi wallahi, yay tsaye a kanta har ta gama sanya kayan ya mi'ka mata 'katon hijab d'inta na sallah tasa kana ya nuna mata hanya da hannunsa......Gaba tayi yabi bayanta haka suka fita palon.

Alhaji Muktari ya kalleshi a lokacin da suke karasowa inda suke yace."Ashe dai da gaskiyar khalifa shiyasa kafin ka shiga ya tuna maka.'' Amadu yayi sauri bagarar da zancen dan baya so ta fahimci inda zancen nasu ya dosa, shi baiga wani dad'ewar sa a ciki ba sa'ido ne kawai irin na khalifa.
Chapter 79 · 0% Book details