← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 58 OF 108

Sashe 58

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Rashida tace"shikkenan bari na hada mana abin kari." Wasila ta mike suka shiga kicin din tare, sto ta bude tana duba abinda yay musu saura na kayan abinci shinkafa ce gatanan duka bata kai rabin buhu ba sai kwalin indomee biyu da taliya da macaroni mansu ma ya kare da kayan maggi babu siga saura kwali daya gwangwanin madara da milo biyu ya rage, hankalinta yay masifar tashi tace"Rashida abinda yay saura kenan?" Rashida tace"Eh mana kinga ni dai.'' Frige ta bude wayam! babu komai a ciki sai robobin lemo da ruwa wanda suka sha suka mayar ciki......Tace"Innalili wa'ina ilaihi raj'iun." Fita tayi daga kicin din ta koma palo ta zauna, tana kuka yanzu idan kayan abincin nan ya kare ya za tayi.......Shikkenan zasu komai rayuwar kuncin da sukayi a baya, Sai hawaye ya shiga zubowa daga idanunta tana tausayawa rayuwar da zasuyi nan gaba.

Tananan zaune Rashida ta fito da fulas din shayi da wata karamar kula data zubo musu indomee a ciki ta aje taje ta dauko sauran kayan da zasuyi amfani dashi gurin cin abincin, ta hada musu suka fara karyawa Wasila dai cin indomee kawai take hankalinta duk baya jikinta tunaninta ya ta'allaka gurin yanda za tayi asirinsu ya rufu....Rashida tace"Anti wasila ina gold din da kika siya kwanaki ba sai ki siyar dashi ba nasan kudin zasu isa ki fara sana'a dasu." girgiza kanta tayi cikin tsananin damuwa da neman mafita tace"Rashida kin mata ranar da Ahamdu ya dauke ni da sunan matarshi, ranar nayi ado da da gold din har nasa lifaya keda Camas! kuka dinga kwarzanta kyawun da nayi gabakid'aya gold dina na gidan Ahmadu in banda wannan zoben dake hannuna." Rashida jikinta yayi sanyi sosai babu shakka suna cikin tsaka mai wuya dama abinda takeji kenan gashi kuma ya faru, tace"Shiyasa tuntuni nake hanaki wani abun saboda dama ni tuntuni na dawo daga rakiyar Uwani wallahi duk wata masifa da muke ciki itace ta jefamu kullum burinta muje mu samu kudi ita tana zaune a gida, Allah ya baki miji nagari me kudi babba mai hankali wanda zai rike ki da kyau ta zugaki kin kashe auranki, gashinan komai ya jagu'be! dama abinda nake ta tunani kenan." Ajiyar zuciya ta sauke tace"Rashida mu bar wannan maganar don Allah hausawa nacewa tun ranar gini tun ranar zane duk abinda kikaga ya samu bawa to da sanin Allah, ammafa wani abun mutum shike janyowa kanshi Ni da uwani mun so zuciyarmu kuma gashinan ta kaimu ta baro amma babu komai Allah yasa ya zama izina a garemu ni da ita, yanzu mu gama karyawa sai muje can d'orayin gidansu Camas ko Allah zai sa mu same ta."

Uwani nacan na bacci suka shaida mata inda suka nufa cikin bacci tace dasu Allah ya kiyaye suka kadai kansu suka fita daga gidan.

Asabe mahaifiyar Camas! na zaune a kujera 'yar tsuguno tana tsince shinkifa taji sallamarsu, ta amsa tana musu sannu da zuwa tabarma ta shimfida musu tana fad'in "Wasila yau kece a gidan

namu, Ina tace Hadiza zata rakani inga inda kuka koma Allah bai nufa ba sannunku da zuwa." Suka shiga gaisawa, Asabe na tambayarsu Uwani sukace tananan lafiya lou. Wasila tace"Camas! kuwa tanan."? Asabe tayi kasa da kanta ran nan a 'bace tace"Yaushe rabon hadiza da kwana a gida ai tafi wata uku sai dai takanzo duk bayan sati biyu to wannan karon ma kinga satin ta uku bata zo ba." Wasila tace"Ayya! mybe tananan tafe." Asabe tace"To Allah yasa." Shiru sukayi kafin su ta mike Asabe tace"Har zaku tafi bazaku tsaya kuci abinci ba." Wasila tace"A'a Asabe mungode." Har soro ta rakosu tana fadin su gaishe da Uwani da kyau kafin tazo.

Suna fitowa Wasila tace na fad'a miki dama kinga munyi asarar kudin motarmu ko? gashi bamu dana komawa gida tsakanin dorayi da tishima akwai nisa sosai dan da kyar ma aka kawo su a dari biyar kona pure watar basu dashi.....Rashida tace"Mu shiga gidanmu wanda muka bawa malam 'Dayyabu nasan idan yananan zai bamu kudin mota da zamu koma gida." Wasila taji dadin maganar Rashida sai suka nufi layinsu na da, suna shiga layin suka hango, gidansu ya koma katin sai da kayan provision! tsayawa sukayi suna mamaki! wani yaro da yazo wucewa ya shiga kallonsu yaso ya ganesu Wasila tace"Kai waye cikin provision din can." Yaron yace."Jazuli ne na gidanmu malam d'ayyabu ne ya siyar masa da gidan shi kuma ya ruge yayi kanti." Wasila da rashida suka shiga mamaki! ashe malam dayyabu haka yake sun bashi gida domun ya zauna ya siyar ya kar'be kudin ya gwammace yayi ta yawon haya da yara da mata, cikin unguwar dama su Wasila da gidan malam dayyabu sune talakawa, gwara su wasila ma gidan kansu ne shi kuwa malam dayyabu gidan haya ne duk lokacin karbar kudi sai anyi rigima dashi masu unguwa sun taru a kanshi sannan zai bada kudin, shinda wasila ta tausaya masa suka bar mishi suna ganin tunda sun samu wani me zasuyi dashi ashe bayan tashin su da sati biyu malam dayyabu ya siyar da gidan ya kama haya ragowar kudin yasa a aljihu yana cin karansa babu babbaka dasu.......Ajiyar zuciya suka sauke a tare suka kama hanya suka bar gurin zuciyarsu cike da wasi wasin yanda zasuyi.

Sosai suka dingi tafiya kan titi wanda tun suna magana suka daina tafiya kawai sukeyi suna yanke yanken hanya har Allah yasa suka fito titin gadon 'kaya! Rashida ta sharce gumin dake goshinta tana haki! tace"anti wasila zama zanyi na huta na gaji wallahi." Wasila tace"Mu samu guri mu zauna nima nagaji." Suka sami guri dai-dai Gate din shiga Management suka zauna suna hutawa, sunanan zaune daliban dake makaranta suka soma fitowa 'yan mata maza zawara da matan aure wasu na fitowa da motocin su wasu wasu kuma na tare abin hawa! Wasila ta dinga kallonsu suna bata sha'awa suna da gata suna da galihu sunyi dacen iyaye sun tsaya musu kan ilimi su kuwa fa! sune nan sune can! Sai taji zuciyarta ta karye hawaye ya tsinke mata! tayi gaggawar sunkuyar da kanta kasa tana sharewa bata so Rashida ta gani sannan kuma jama'ar dake gurun suma bata so su gani, tana dago kanta suka had'a ido da Suhairat ita da kawayenta bakin wata mota! Zasu shiga macace take driving din, da sauri ta kauda kanta gabanta na faduwa tace"Rashida tashi mu tafi." Rashida tace"Anti wasila dan bari mu sake hutawa wallahi gurin akwai iska." Tace."Rashida hutun jaki da kaya kikeyi kawai ki tashi mu tafi mu samu mu fita babban titi na sabon titi." Rashida ta mike tana yafa mayafinta sukayi gaba.......Motarsu Suhairat ce taci burki a gabansu, da sauri suka matsa baya Suhairat ce ta bude motar ta fito sauran suna ciki suna hangensu

Gabansu ta tsaya tana watsawa Wasila kallon banza tace"Ke matar babban mutum ina zuwa haka? ya naga kina yawo a kasa ko satar hanya kikayi kika fito yawon tazubar d'in da kika saba."!? Wasila tayi shiru tana kallonta Rashida tace"Haba Suhairat wace irin magana ce wannan? kin manta anyi muku tsakani da anti wasila meye ruwanki da ita yanzu." ? Suhairat tayi dariya tana gyara zaman glass din dake idanunta tace"Rashida daga tambaya sai cibi ya zama 'kari! ai gani nayi bai dace ace kamar wasila matar *Ahamadu Musa* na yawo 'kasa ba, ai kamata yay mu ganta cikin katuwar mota

wacce ta amsa sunanta, ko da yake dai ina jin satar hanya tayi ta fito, Okey karfa ku damu da maganata, ba wani abun nake nufi ba, saboda haka na barku lafiya." Wasila da Rashida suka bita da kallo har ta shige motar tasu suna kallonta tana she'ka dariya tare da tafawa da 'kawayenta tana nuna wasila da hannunta su kuma sai dariya sukeyi, kafin wacce take driving din ta figi motar a guje suka bar gurin.

Wasila ji tayi gwiwowinta sunyi bala'in sanyi ta inda har ta kasa motsa kafafunta da niyar tafiya sai kawai ta nemi gefan titi ta zauna rana na kwallare mata fuska zufa! ta shiga ketowa daga jikinta

Rashida itama ta zauna kusa da ita tana fad'in"Amma wallahi suhairat din nan bata da mutunci shegiya guzumar banza wacce ta rasa mashinshine anti wasila ki kyaleta don Allah mybe suna da labarin Ahamdu ya sake ki shiyasa suke murna da dariya amma babu komai ai duk abinda mutum yayi kanshi.

Ba tace komai ba tana dai sauraran Rashidan da duk rarrashin da take mata ita kuma sai nanata kalmar innalilihi wa'inna ilaihi raji'un takeyi a zuciyarta, ji tayi komai na rayuwa yayi mata zafi ta dinga nadamar kuskuran da tayi a baya, kanta ne ma ya soma yi mata ciwo, rana ce ko damuwa ce ko kuma rashin bacci ne? babu wanda ya sani sai Allah.

Kusan mintina ashirin suka dauka a zaune a gurin masu babur din a dai-dai ta sahu sai tayi suke musu wai ko zasu shiga kowa na ganin lamun ba shiga zasuyi ba sai ya buga babur dinshi yayi gaba!..................

Cikin 'kwalleliyar ranar dake kan ganiyar ta, suka fita, titin sabon titin gidan 'kankanra lokacin sunyi masifar galabaita mutuka gashi ko na pure watar babu Wasila taja hannun Rashida suka fake wata inuwa still dai a bakin titin suke zaune suna mai da numfashi suna kallon ababen hawan dake shige da fice a gurun......."Wasila anti Wasila yunwa nakeji da shiru kinji ma'kogwarona kuwa kai anya ba zamu nemi taimako ba kuwa."?

Wasila tace"Nima nagaji Rashida taimako a ina zamu nema."? Anti wasila mu nemi left gurin masu motar gida sai sunfi sauki akan masu a dai-dai ta sahu tunda su kinga sana'a suka fito." Wasila tace"anya kuwa Rashida."
Chapter 58 · 0% Book details