Sashe 2
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
*Free Pege3*
Kunnanshi ma'kale da waya ya fito daga bedroom din shi ya zauna daya daga cikin shirga shirga kujerun dake palon ya wani d'ora kafa d'aya kan d'aya yana masifa!....."Khalifa wad'annan mutanan fa babu Allah a tare dasu ni wallahi tuntuni na dawo daga rakiyarsu shin wai mulki hauka ne!? duk wannan kashe kashen da akeyi da sace sacen yara kananun mun san daga ina ne kawai saboda ana jin tsoronsu sai ayi shiru to wallahi daga yau na shirya d'amarar ya'ki! dasu mulki suke so nima shi nake so Allah ya bawa mai rabo sa'a haba! wannan al'amarin ya ishi talakawa wuya tayi wuya mutane sai mutuwa sukeyi gobe ka fito da wuri zamu fara yawon kamfen insha Allah." Khalifa dake daya bangaran yace."Insha Allahu zan fito da wuri amma yana da kyau ka tanadi matakan tsaro kafin fitar tamu.'' Yace."Kar ka damu da wannan insha Allah Allah zai karemu tunda domunshi muke." Sallama sukayi da juna ya kashe wayar tare da ajiyeta saman tevur din dake gabanshi.....Zuba masa ido nayi ina kallo wai! Allah yayi hallita a gurin kyakkyawa ne ajin farko fari gaggausa yana da dogon hanci da manya ido da gashin gira kewayayyiyar fuskarsa na dauke da sisirin sajensa wanda yasha gyara ya zauna das ya kawata fuskar tashi......Ya wuce ka kirashi yaro gaskiyar magana kenan domin idan ka tsaya ka kalleshi da kyau zaka fahimci shekaru sun d'an tura masa a 'kalla yanzu shekarunsa ar'bain da biyu zuwa da uku........
*Ahamad Musa (Ba iya ka!)* ainin sunansa kenan Matashin saurayi mai jini a jiki mai tashen kudi wanda bai san iya adadinsu ba, shi ya sanya jama'ar gari suke kiranshi da wannan suna *Ba Iya ka!* shima ya samo shi gurin mahaifinsa *Alhaji Musa (Ba iya ka)* wanda ya shahara yayi shura a zamaninsa Allah ka ji'kan maza.
Ahamad kawai ya haifa shima kuma kafin ya haifeshi din sai da ya futar da rai! da haihuwa lokacin duk girma ya baibayeshi ya auri wata 'yar filani ashe rabon a jikinta yake haduwarta ta farko ta dauki ciki.......Farin cikin da ya shiga a lokacin Allah yayi yawa dashi ya dinga sadake sadake yana kai mutane saudiya suyi wa matarshi addua Allah ya sauketa lafiya.
Allah babu yanda baya tsara lamarinsa gurin haihuwar Ahamad mahaifyarsa ta rasu sosai iyalin Alhaji Musa sukaji mutuwar daga bisani suka barwa Allah lamarinsa.....Sai suka dawo kan Ahamad suka dinga nuna masa so da kulawa mussaman mahaifinshi Allah ya jarrabeshi da kaunar yaron nashi ashe ba zasu dade da juna ba Allah ya dauki rayuwar Alhaji Musa....Mutuwar da ta girgixa zu'katan al'ummar gari suka dinga kuka da fadin"Bango majin ginar talakawa ya fad'i!! Jama'a sukayi dafifi a harabar gidan suna masa addua da fatan Allah ya kai rahama kabarinsa.
Tunda Ahamad ya taso yaga yanda mahaifin shi ke taimakon al'umma sai ya dora a inda ya tsaya tun yana dan shekara ashirin a duniya sunanshi ya 'bace a gari mutukar baka kira
*(Ba iya ka)* ba to babu in zaka kwana kana kiran Ahamad babu wanda zai gane wanda kake nufi....
Ahamad jama'ar gari ne suka kwadaita masa sha'awar mulki da sam ba tsarinsa bane ya fiso yayi harkokinsa to shima kuma da ya zauna yayi nazarin yanda al'amuran siyasar ya ta'bar'bare sai kawai yayi sha'awar fantsama kansa a harkar domin ya taimaki al'ummar da suke galabaita a jahar mussaman talakawa sune dama abun tausayi.
Kallo guda za kayi masa ka gane yana da fuskar Salihai! a zahirinsa kenan a bad'insa kuwa mutum ne shi mara hakuri kuma sam baya barin ta kwana kamar zawo yake mutukar kayi masa abu idan bai rama ba sam baya jin dad'i....bayan wannan halin nasa bai da wani mummunar hali dama ance adan adam tara yake bai cika goma ba Ahamad nada tausayi da taimako sai nace muku ma duk rabin neman kudinsa yanayi ne kan jama'ar gari marasa galihu da na kasassu gami da marayu.......Dalili kuwa bashi da nauyin kowa a kanshi tunda shi ba aurene dashi ba ballanta ayi maganar yara, Jama'ar gari duk sun dauka yana da aure da iyali shiyasa duk adduarsu a kan iyalinsa take 'karewa sai dai kawai amsa da "ameeen"
Nasan zakuyi mamakin namiji kamar Ahamad mai jini a jika sannan uwa uba kudi! ga kyau da kwarjini da haiba da yake dasu amma me yasa bai aure ba? Yana zaune hakane ba wai dan bashi da lafiya ba ko kuma rashin matar aure akwai 'yan mata bila adadin dan ba zasu lissafu ba, kawai duk cikinsu bai ga wacce ta kwanta masa a ransa bane ya ajiye maganar aure a gefe saboda yasan cewa lokaci ne idan Allah ya kawo masa matar lokaci guda za'ayi a gama.
'Daya daga cikin masu tsaronshi ne ya shigo palon....Ya d'aga kanshi yana kallonshi A nutse yace."Ya akayi."? Garba yace."Kana da bakuwa tana dakin 'baki mun sauketa."
Jim! yayi yana nazari wace 'bakuwa yayi kuma yanzu karfe goma na dare! Ko da yake ai tunda ya fara wannan harkar kuma yayi ta ganin jama'a ya mike a nutse Garba ya bashi hanya ya wuce kana ya take bayanshi.
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*Free Pege5*
Yana tsaye a inda yake Garba ya shigo ya sanya masa ido har ya 'karaso inda yake tsaye.....Kai a 'kasa Garba yace."Sir tayi nisa da layi sosai amma fa ina zargin wani dan gane da wannan yarinyar." Ido ya sanya masa a nutse yace."Kamar name kenan." Garba ya 'kara risinar da kanshi a kasa yace."Anya kuwa ba turo ta akayi ba kuwa kasan fa mutanan babu abunda ba zasu iya ba."
Murmushi yayi yace."Garba idan ma turo ta sukayi tayi min sharri ko abu makancin wannan to insha Allahu ba zasu samu nasara ba ni nafi karfinsu tunda bana nufin su da sharri sai alkairi harkata ta siyasa kuma yanzu na fara babu gudu babu ja da baya ni dasu Allah ya bawa mai rabo sa'a."
Garba yace."Ka gama magana Yallabai Allah ya baka nasara kan dukanin abunda kasa a gaba." Ya amsa da "ameeen.'' Ya juya cikin yanayin tafiyarshi ta gwazan maza, Garba ya take masa baya.
Wasila na fita daga Estate din ta hango motar Alhaji Ma'aruf a can tsallake a fake.....ranta duk a bace ta karasa bakin motar.....'Dan kwankwasa jikin motar tayi Camas! da Alhaji Ma'aruf suka firgita sukayi saurin sakin junansu suna gyarawa Ido jawur! ya bude mata motar yana fad'in" Ya akayi *'Yar gaske* Allah yasa kin aiwatar da komai." Rai a 'bace tace" Wallahi ya'ki bada had'in kai d'an iska kawai yasa na fitar da tsaraicina amma kallo ban isheshi ba."
Alhaji Ma'aruf yace."Kai! wannan d'an iskan mutumin taurin kanshi yayi yawa wallahi yanzu duk cikar ki da batsewar ki bai sanya yaji sha'awarki ba? anya ma kuwa yana da lafiya? duk mutum mai lafiya dai ya ganki sai yaji sha'awa ta kamashi." Ya 'karashe maganar yana bin jikinta da kallo.
Wasila ganin yana mata kallon iskanci yasa ta dan ja tsaki kadan ta mika hannu tana jan hijab dinta wanda Camas! take kwance a kai! Kallo guda tayi mata ta gane abunda ke faruwa wato bayan futar ta ayarsu suka she'ke! Allah ya kyauta.
Hijab dinta ta sanya tace"Alhaji kaimu gida dare nayi sai dai kuma mu sauya wata dubarar na gane guy sai an bude masa wuta dan a tsaye yake kuma wallahi kuka bari ya hau kan kujerar mulki sai kashin ku ya bushe duk sai ya kame ku.
Alhaji Ma'aruf ya kunna motarshi yana goge gumi yace."Maganar ki gaskiya ce *'Yar gaske* shiyasa muke 'kokarin muga mun kassarashi tun kafin ya cimmana amma babu damuwa zamu shirya masa wani sharrin."
Suna tafiya suna zan can Ahamad dashi da taurinka kansa Alhaji Ma'aruf na fada musu yanda suke dauki ba dad'i a kan suga bayanshi amma abun yaci tura yace shi har jinin kad'angare ya sha duk saboda yaga bayan Ahamd amma asirin bai kar'beshi ba a lokacin ma so yayi ya dawo kansa sai da bokan da ya kulla asirin ya warware tukkuna ya samu lafiya.
Wasila tace"Ka rabu dashi Alhaji duk ku daina wahalar da kanku da kudinku da yawon bin malamai a kanshi sharrina ma kad'ai ya isheshi sai nayi fata-fata da rayuwarshi."
Alhaji Ma'aruf yaji dadi maganar ta yace.''Mu kuma munyi miki alkawarin baki dadin duniya *Yar gaske* zaki fantama sosai da kudi sai dai ki bawa wasu."
Da jin wannan magana tashi sai Wasila ta sake daukar aniyar babu gudu babu ja da baya a kan Ahmadu Musa *(Ba iyak ka)* har sai taga abunda ya turewa buzu nadi.
'Karfe goma sha biyu saura na dare ya ajiyesu a kofar gidansu Ledoji cike da kayan dadi ya bawa Wasila rafar kudi ta dubu dari camas ya bata dubu hamsin sukayi sallama da juna kan cewar zasu fito da wurwuri domi zuwa yawon kamfen........
'Yar 'kofar da suke karawa Wasila ta tura firgigit Uwani ta mike zaune dama ba baccin take ba tana zaune tana dakon dawowar 'yar tata.
Wasila ta mayar da 'kofar ta kare gidan kana ta saki buhun dake sakale suka shiga cikin gidan suna ihu! kamar ba dare ba.
Uwani da Rashida suka fito a guje! Wasila ta farke rafar kudin dake hannunta ta soma mannawa Uwani a saman goshi.....Uwani na ganin Sabbin 'yan dubu-dubu na watsi a a tsakar gida sai ta fasa ihu! ta rungume! 'yar tata suka kama rawa wata lafiyayyar gud'a ta dinga rangadawa tana sakarwa 'yar tata kirari......Ita kuwa Rashida kudin take bi tana tsince tana ta faman kyalkyala Dariya sai kace mahaukaciya.
Sai da suka gama murnarsu sannan suka dauki ledojinsu suka shige ru'babbiyar rumfarsu da ta kusa ruftawa Rasida ta samo katon faranti suka baje wasu 'kosassan kaji guda shida wanda komai zulamar mutum bai iya cinye guda saboda girmansu ga had'ddaun lemuka masu sanyi nan suka baje suka dinga yagar kaza suna yi mata cin ala tsine uwar me karya, wai! yaushe rabon duniya da ayya raye."!! Uwani ta fada tana shigowa dakin bayan taje ta wanko hannunta........Wasila tace"Yanzu dai mu kwanta muyi bacci dare yayi sai gobe in yaso sai kuji labarin abunda yake faruwa.