Sashe 12
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
"Humm! ai kaji gareje irin na mutane jama'a basa tsayawa suyi aiki da lura wannan gwamnati fa kafin hawanmu akwai abubuwan da muka tarar akai akwai tarin bashishshika da gwamna na baya ya bari bai biya ba tilas! mu muka biya wanda har yanzu ba'a karasa ba haba jama'ar gari ku kwantar da hankalinku kamar tsumma a randa insha Allahu dukanin abunda mai girma gwamna ya ambata zaiyi to zaiyi ku dai kawai ku mara masa baya a za'be na gaba ya maimaita insha Allahu zakuyi mamakin aikin da zaiyi muku kano zata koma tamkar kasar waje saboda yanda za'a gyarata da titina da makarantu da asibitoci da sauransu."
" 'Yar gaske na tabbata jama'ar gari na sauraranki da duk bayanai da kikeyi to amma inda gizo ke sakar anan shine! sufa a halin yanzu duk wata magana da zaku fito ku fad'a a yanzu ba zasu dauketa da muhimanci ba saboda zuciyarsu ta riga ta gama makancewa da kaunar wannan d'an tahalikin mutumin wato *Ahamadu Musu* wanda suke masa inkiya da *(Ba'iya ka!)* shine nima nake ganin gwara kawai ku hakura ku bar masa tunda a zahiri kamar yafi ku mutane a wannan tafiyar."
Dariya ta saki harda tafa hannu "Oh! mutane kenan!? Ni wallahi ma abun mamaki yake bani idan naji suna kiran wannan mutumi da sunan dan takarar gwamna banta'ba jin inda *Gwauro* yayi mulki ba babban mutumin dan kimanin shekaru ar'abain da biyar yana zaune banu aure ai dole a bunkice shi.....To jama'a yau dai bari na fad'a muku abunda baku sani ba akan wannnan mutumi da kuka nace ya zama shugabanku.....Ahamdu dai tunda yake bai ta'ba aure ba duk wani mai shakku yaje yayi bunkice akai, yana zaune a gidanshi yaci karansa babu babbaka ya kawo duk macen da yake so yayi mu'amula da ita tamakar matarshi....Jama'a ni Wasilatu 'Yar gaske zancen dai da nake muku nima ya auna ni a gidanshi Allah ne ya tseratar dani nasan mutanan da suka je gidanshi kar'bar tallafin da yakeyi duk karshen wata sun gani lokacin da ya sanya aka daura min ankwa babu ji babu gani ya sanya aka shiga dani ciki gidanshi a kulle da kwado..... dan jaridar ya katseta da fadin" To Yar gaske ya akayi kikeje gidanshi bayan kowa yasan ke ba 'yar bangaranshi bace shin ko zaki fadawa masu sauraranki dalili."?
Shiri fa ya dauki zafi!!
Zama ta gyara tace"Eh tabbas jama'a zasu zargi haka to abunda ya kaine gidanshi shine sati biyu da suka wuce yazo har kofar gidanmu da niyyar yaudarar kanwata sai ni kuma Allah ya nuna min shi ya dauki makudan kudi ya bata nice nan na hanata ta'ba kudin washe gari na nufi gidanshi domin na bashi kayanshi sai na tarar yana rabawa jama'ar gari kudi......Kafin nayi aune! kawai na ganshi tare da wata mata a kaina tana nuna masa ni wai nice! 'kawata Camas! da muke tafiya tare ta shiga rudani a gaban mutane ba tare da yayi wani bunkice ba ya kira police yasa aka buga min ankwa aka tasa 'keya ta cikin gidanshi a kulle to wannan damar ya samu yaso ya biya bukatarshi a kaina sai Allah ya kare ni."
Dan Jaridar maganar tasha masa kai sosai.....Ashe bashi kadai ba harda jama'ar gari dake sauran shirin kafin kice kwabo zantuka sun soma tashi a garin wanda tun kafin a rufe shirin gari ya hargitse da hayaniya kowa na fadin albarkacin bakinsa kan Ahamdu ashe dama bashi da aure Gaskiya magana ta fito kan zargin da mutane ke masa gurin bada kudin da yake a cikin gidansa yana lalata da 'yayan mutane, sai wad'anda akayi abun a gabansu suka fara gazgatawa har suna bada larabi zance fa yayi tsanani a gari anata kace!kace! masu tsinewa Ahamadu sunfi yawa kan wadanda suka karyata maganar.
Wani irin gumi yake tsiyayarwa a jikinsa ita kanta rigar dake jikinsa sai da ta jike saboda tsananin tashin hankali ashe dama alkairi yana zama sharri! bai ta'ba nadamar zamanshi a haka ba sai yanzu shin wai yama akayi yarinyar nan tasan bashi da aure.....Shine taje ta kwancewa zani a kasuwa tilas masu karamin tunani su gazgata maganarta, Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un! bai ta'ba tunanin al'amarin siyasa ya kai hakaba amma kuma wannan siyasar da sukeyi kamar ta sa'bawa dokar 'kasa 'kazafi! babu shi a siyance.
*Humm! Ahamdu kenan har yanzu baka san meye Siyasa ba.!*
Garba da Hadi suka fusata sosai Suka mike cikin zafin nama zasu fita Khalifa ya dakatar dasu da fad'in"Ina zakuje a wannan halin."? Garba Yace."Yallabai yarinyar nan yau sai tayi nadamar uwarta bata haifeta ba mu za tayiwa 'kazafi! banta'ba ganin butulu irinta ba, wallahi da ba don Yallabai yace tun farko a kyaleta da yanzu na zubar mata da hakora da tuni tana kwance tana jinyar kanta dan sai nayi mugun sa'ba mata kammani."! Khalifa yace."Ku dawo ku zauna ku samu nutsuwa." Suka koma suka zauna suna huci! yanda suka fusata niyyarsu subi Wasila gidan redion tana fitowa suci ubanta sai kuma aka katse musu hanzari.....Khalifa yaje ya zauna kusa dashi ya sanya hannu ya dafa kafad'arshi a hankali yace."Siyasa ce f........! katse shi yayi ta hanyar d'aga masa hannu Khalifa ya tsira masa ido ganin yanda duk ya wani burkice har yanzu yana digar da gumi kamar dakin babu Ac 'yan ya tsunsa biyu ya d'ora saman fatar le'bunansa ya tsurawa guri daya ido yana girgid'a kansa.
MYSON, NAJIB SA'ID*
Tare da kai da
*LAWAN RANO*
Nagode kwarai da kulawar ku akan wannan book din Allah ya 'kara kauna ya baku mata na gari👏🏻
~~~~~~~~~~~~~~~~
*Free Pege14*
To ganin Malam mai allo ya nufi masallaci yasa suma suka daura alwala domin gabatar da tasu sallahar kafin ya shigo gidan su tattauna abunda yake faruwa, suna zaune kan tabarma ya shigo bakinsa da sallama kamilin mutum ne wanda karatun al'kur'ani ya ratsa shi fari tas dashi kana ganinshi kaga bafulatani usul......Bitan! ta gyara masa tabarma ya zauna yana fad'in"Ashe bakuwa mukayi a gidan Hajara kece kike tafe."? Ta amsa da "Eh wallahi malam tun kusan azuhur nake gidanan Bitan tace min kana tsangaya tare da yan makaranta malam ya gida ya damuna dafatan duk mun same ku lafiya."? Ya aje carbin hannunsa a gefe ya amsa da fadin" Lafiya lau Haraja ya yara ya mai gidan naki."? Duk sunan lafiya kalau wallahi ai yace ma a gaishe ku da kyau."! To masha Allah muna amsawa amma dai za kiyi mana kwana biyu kafin ki koma." Murmushi tayi "A'a malam gobe nake sanya ran komawa dama muhimaniyar maganace ta taso wanda shi mai gidan nawa ne ma yace lallai nazo na shaida maka abunda ke da akwai." To Allah yasa alkairi Hajara ina sauranki." Malam mai allo ya gyara zamanshi yana fuskantar Hajara wacce ta soma warware masa abunda ke faruwa ga iyalin Dan uwanshi Yahuza mai rasuwa.........Ta kara da cewa"Malam yana da kyau ku sanya ido sosai kan wannan yarinyar domin a gaskiyar magana abun da takeyi ya soma wuce gona da iri watarana zata dauko muku abin kunya ko kuma taje ta zagi wani babban mutumin da zai daureku gabadaya yau da al'amarin ma a kanta zai tsaya da sauki wani abun idan ta dauko to ku da bakuji ba baku gani ba sai ta shafeku wannan shine dalilin da ya sanya nace to bari nazo na fada muku halin da ake ciki."
Malam mai allo yayi shiru yana jimanta al'amarin, to har yausha hakan ta faru basu sani basu sani ba ko da yake hakan zata iya kasancewa tunda bayan rasuwar Yahuza rigima suka dinga tafkawa da Uwani mahaifiyar yaran kan dole sai an raba gado an bata na yaranta shi kuma yace ko za'a raba gado to ba za'a bata na yara saboda ita mace ce su kuma yaran lokacin suna yara kananu za dai a siyar da gona a raba kudi kaso biyu shi ya dauki kashi daya sauran kuma ya zama magada wato Wasila da Rashida kenan in yaso ita sai a fitar da ita na tuminin takaba kamar yanda addini ya shara'anta.....Nan ma sai ta tada ballin masifa taje 'yan uwanta suka zugota tazo tana yiwa su malam rashin kunya wanda hakan ya janyo sukayi mata fatata fatata! sannan suka kwace su Wasila daga hannunta, kwana biyu da faruwan lamarin Wasila dake tana da wayo a lokacin ta kai kimanin shekaru goma sha biyu sai ta fakaici malam din ya tafi tsangaya ra rike hannun kanwarta suka gudu da malam ya dawo ya samu labari yace."Suje idan shine sai sun tako da kafafunsa sun neme shi, to hakance ta kasance koda su Wasila suka koma gaban mahaifiyarsu sai wahala tayi tsanani a garesu da kyar suke ci daya a rana Wasila itace yawon bin gidajen amare tana musu wanke wanke da raino da share share su bata kudi da abinci ita kuma Uwani itace aikin wankau da dakau da sauransu.....Wasila ta yanke shawarar tun karar wan mahaifin nasu domin su bashi hakuri suka shirya tsaf suka nufi Garin nasu Garko!! Malam ya dinga musu fad'a sosai yace."Duk tsiya dai nine mahaifinku tunda babu ubanku kuna bin shawarar mahaifiyarku kuna bijere ma dangin ubanku to ko auranku ake nema gurinmu zaku zo gwara ku nutsu kuyi hankali ku zauna tare damu zaman ku cikin wannan gida ku kadai bai dace ba saboda haka na yanke shawarar zan baku daki daga ku zauna har Allah yasa ku samu mijin aure ita kuma Uwani ta tafi gidansu itama bata wuce aure ba idan ta samu miji tayi aure....Da jin wannan magana ta malam mai allo sai su Wasila suka yanke sgawarar guduwa domin a ganinsu yanda suka saba da zaman birni zasu cutu a kauye....Washe gari Uwani ta tasa kan 'Yayanta da asuba suka gudu....Wannan abu da sukayi ya batawa malam mai allo rai tun daga lokacin ya dauke hannunsa daga kansu idan ma sauran 'yan uwa suka kawo masa maganarsu sai ya koresu yace kar wanda ya sake kawo masa maganar wadannan yaran marasa kunya suje duniya ce zata koya musu hankali.
*Wannan kenan*