← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 3 OF 108

Sashe 3

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwani tace"Ki d'an gutsira min wani abu mana na kwana dasu a karkashin filona anya ma kuwa yau zan iya bacci oh! duniya kenan."

Wasila tace"Uwani kwanta kiyi bacci harda munsharri ai insha Allahu mu da talauci munyi hannun riga." Uwani ta dinga wata mahaukaciyar dariya tana fad'in"Ai dama ni nasan jari na haifa ke ba 'karamar mace bace idan ba'aso ki dan komai ba a so ki dan 'kirar jikinki ita kuma Rashida wannan farar fatar tata itace jarina."

Wasila tace"Uwani nifa ba karuwanci naje nayi ba sana'a muka fita mukayi ko ba haka ba Camas!." Tafada tana kallon Camas! dake irga kudinta.

Camas tace"Kwarai kuwa sana'ar mukaje mukayi ta siyasa gobe zamu fita da wurwuri shiyasa ma ban wuce gida ba."

Uwani tace"Kai amma wannan sana'a ta karbeku wallahi Allah ya bada sa'a ya taimake ku."

Suka amsa da "ameen." Sannan ko wacce ta gyara shimfida ta yada ha'karkari ta kwanta ana jira kuma gari ya waye a fita *Sana'a*

_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/11, 9:41 PM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

*Free pege4*
Cikin takun girma gami da 'kasaita ya shiga d'akin, lokaci guda 'kamshin turaransa ya karad'e hancinta, ta d'ago shanyayyun idananunta ta zubasu a kansa, tun kafin ya 'karaso inda take zaune ya 'kare mata kalau black beauty mara tsayi sosai da cikar kirji dauke kansa yayi daga kanta ya had'e fuska sosai wannan bakuwar tashi ba ta arziki bace duba da yanayin suturar dake cikinta.

Tana sanye da wata matsatstsiyar t_shart da dogon wandon jins wanda ya fitar mata da zahirin hallitarta ta sanya karamin hijab wanda ko kirjinta bai rufe ba tsakiyar kanta yayi tozo da tsayi da alama tana da gashi sosai tunda ga alamunsa nan ya nuna saman goshinta.

Hannunsa cikin aljuhu ya isa inda take, ta mike tsaye da sauri tana marmar da shegun idanunta masu rikita lissafin da namiji......Ya kura ma jikinta kallo tayi sosai dan bai hango makusa a tattare da ita ba ta cika har ta batse kuma tana da abubuwan da yake bala'in so a jikin 'ya mace sai dai kash! ba wannan ne a gabansa ba abunda ke gabansa a halin yanzu shine ya za'ayi talakawa su samu walwala da farin ciki.

Fuskarshi ya sake tamkewa tamau! yace."Baiwar Allah daga ina? ance dani nayi bakuwa na dauka ta arziki ce sai a ka samu akasi."

Wasila taji ciwon maganarshi kasancewar ta macen da bata daukar raini mussaman ga da namiji basarwa tayi ta matsa kusa dashi cikin salon janye hankali tace"Daga duniya na fito nazo ne in d'ebe maka kewa nasan namiji lafiyayye kamar ka na bukatar lafiyayyar mace ka mata.

Tsawa ya buga mata yana nuna ta da hannu"Ke! cikin gidana kika shigo kina min wannan maganar? ashe dama zargin da nake miki gaske ne okey get out from my house. "! Maimakon ta fita sai ta durfafeshi tana so ta rungumeshi, ya kai mata wani wawan mari! yana ya tsine fuska sai karkad'e jikinsa yake kamar wanda ya ra'bi motar daukar kashi.....Ya mutsa fuska yake yana korar shaid'an, yace." Za kici Ubanki yanzu yanzu zan sanya a xane miki jiki har gida zaki shigo ki kawo min iskanci ni ba'irinku bane." Fita yayi yana 'kwalawa Garba kira.

Wasila ta dauke hannunta dake fuskarta gaskiya yana da taurin kai ta lura ba zai bari ha'kansu ya cimma ba ruwa ba d'an iska kawai tayi irin wannan shigar ya dinga kauda kai yana ya tsine fuska anya ma kuwa lafiyayye ne? bata da mai bata amsa sai tayi maxa ta dauki jakarta zata futa suka buga karo dashi yazo zai shigo kirjinta ya daki kirjinsa yayi saurin ja gefe guda yana kallonta sai wani gumi yake kamar wanda yayi tsere.

A ya tsine ta kalleshi tace"Na d'auka ai lafiyayyan namiji ne ashe hotiho ne har kana zagina 'kato da kai baka kunyar zagi anzo a jiyar da kai dad'i kana gudu Allah ya kyauta kaje ka nemi magani."

Wata sha'ka ya kai mata ya matse ta a jikin bango (garo) ta dinga kakari idanunta sunyi jajawur!!! Cikin kaushin murya yace."Idan za'a had'a min iri-irin irinki guda dari duk zan gama musu aiki ba tare da nagaji ba, 'karyar iskanci kike yarinya da ina da bukatar mace a yanzu dana fatattaka ki kuma in kwana lafiya 'yar iska mara galihu."

Hannu tasa tana 'kokarin 'bam'bare hannunsa dake sha'ke da wuyanta duk ta muzanta sai kyarmar jiki take tana cizan le'banta.....Sai da ya gama galabaitar da isa sannan ya saketa aikuwa ba tayi wata-wata ba ta kai hanni gabanshi zata d'amka! yayi gaggawar ri'ke hannunta yana kallonta da mamaki a tare dashi.

Sun jima suna kallon juna ita dashi mugun mamakin 'karfin halin yarinyar yake wato shammatarsa take so tayi ta nakasta shi....Ido jawur! tace"Sake min hannuna."! Ya 'kara rike hannun tamau! yana sakin wani killer smile yace"Kina so ki ta'ba ne."? Wasila tayi tsuru-tsuru tana kallonsa sam ba tayi tsammanin guy zai samu galaba a kanta ba.

"Wannan kayan aikin da kike gani yafi 'karfin irinku 'yan iska! na kamilar mace ne mai addani ba irinki mai yawon ta zubar ba." A fusace! ta fuzge! hannunta ta watsa masa kallon raini fuuuuu!! ta kama hanyar fita......Taku uku yayi ya cimmata tare kofa yayi yana me bin jikinta da wani shu'umin kallo.

"Sosai kikayi babu wata makusa a jikinki duk inda 'yan mace ta kai kin kai yarinya sai dai sam baki burgeni ba idan ma turo ki akayi to sai kije ki sake sabon shiri ki sani Ahamad ya wuce tunaninki." Yana 'kare maganarshi ya 'kwalawa Garba kira.

Ya shigo da sauri yana fadin "Yalla'bai! gani.'' Yace." Maza rakata da bulala idan tayi gardama ka zane 'kafafunta." Garba Ya kalleta, "Wuce muje." Yafada cikin bin umarnin Ubangidansa.

Wasila kamar ta hadiye zuciya ta mace tunda take a rayuwa ba'a ta'ba tozarta irin yau ba lallai guy bashi da mutunci amma babu komai sun d'aura idan kere na yawo zabo na yawo watarana za'a had'u.
Kallon uku shaura kwata tayi masa kana ta gyada kai ta wuce shi.....Garba ya bita a baya da zabgegiyar bulalarsa....Harbar gidan ya fito ya tsanya tare da zuba hannuwansa cikin aljuhu yana kallo Garba ya tasa 'keyarta har bakin gate yanayi yana caud'a bulala a 'kasa kamar zai daketa hakan ya sake kular da ita ta sake 'kullatar guy girgiza kai kurrum take tabbas maganar da chamas! tayi gaskiya ne babu abunda yake cikin harkar Siyasa sai tozarci da wulakanci, Garba na ganin tayi nisa da layin sai ya juya ya koma cikin gidan.

_Muje Zuwa_
*BINTA UMAR ABBALE*
[7/12, 8:39 AM] Bintu: *'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

*Free Pege5*
Yana tsaye a inda yake Garba ya shigo ya sanya masa ido har ya 'karaso inda yake tsaye.....Kai a 'kasa Garba yace."Sir tayi nisa da layi sosai amma fa ina zargin wani dan gane da wannan yarinyar." Ido ya sanya masa a nutse yace."Kamar name kenan." Garba ya 'kara risinar da kanshi a kasa yace."Anya kuwa ba turo ta akayi ba kuwa kasan fa mutanan babu abunda ba zasu iya ba."

Murmushi yayi yace."Garba idan ma turo ta sukayi tayi min sharri ko abu makancin wannan to insha Allahu ba zasu samu nasara ba ni nafi karfinsu tunda bana nufin su da sharri sai alkairi harkata ta siyasa kuma yanzu na fara babu gudu babu ja da baya ni dasu Allah ya bawa mai rabo sa'a."
Garba yace."Ka gama magana Yallabai Allah ya baka nasara kan dukanin abunda kasa a gaba." Ya amsa da "ameeen.'' Ya juya cikin yanayin tafiyarshi ta gwazan maza, Garba ya take masa baya.

Wasila na fita daga Estate din ta hango motar Alhaji Ma'aruf a can tsallake a fake.....ranta duk a bace ta karasa bakin motar.....'Dan kwankwasa jikin motar tayi Camas! da Alhaji Ma'aruf suka firgita sukayi saurin sakin junansu suna gyarawa Ido jawur! ya bude mata motar yana fad'in" Ya akayi *'Yar gaske* Allah yasa kin aiwatar da komai." Rai a 'bace tace" Wallahi ya'ki bada had'in kai d'an iska kawai yasa na fitar da tsaraicina amma kallo ban isheshi ba."

Alhaji Ma'aruf yace."Kai! wannan d'an iskan mutumin taurin kanshi yayi yawa wallahi yanzu duk cikar ki da batsewar ki bai sanya yaji sha'awarki ba? anya ma kuwa yana da lafiya? duk mutum mai lafiya dai ya ganki sai yaji sha'awa ta kamashi." Ya 'karashe maganar yana bin jikinta da kallo.

Wasila ganin yana mata kallon iskanci yasa ta dan ja tsaki kadan ta mika hannu tana jan hijab dinta wanda Camas! take kwance a kai! Kallo guda tayi mata ta gane abunda ke faruwa wato bayan futar ta ayarsu suka she'ke! Allah ya kyauta.

Hijab dinta ta sanya tace"Alhaji kaimu gida dare nayi sai dai kuma mu sauya wata dubarar na gane guy sai an bude masa wuta dan a tsaye yake kuma wallahi kuka bari ya hau kan kujerar mulki sai kashin ku ya bushe duk sai ya kame ku.

Alhaji Ma'aruf ya kunna motarshi yana goge gumi yace."Maganar ki gaskiya ce *'Yar gaske* shiyasa muke 'kokarin muga mun kassarashi tun kafin ya cimmana amma babu damuwa zamu shirya masa wani sharrin."
Chapter 3 · 0% Book details