Sashe 76
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read
Da 'kyar Rashida ta iya gane hanyar gidan ta dinga nunawa Garba hanya yana bu ta cikin kunyar gonakin mutane gwajab gwajab din da motar take ya sanya ta bud'e idanunta tana d'an motsawa, sai kawai taga duk rabin jikinta a jikinshi, yayin da shi kuma yayi wani irin zama a cikin motar kamar wanda zai kwanta yayi hakan ne domun taji dadin yin baccin a jikinsa........Da sauri ta mike zaune tana gyara xamanta had'e da gyara mayafinta ta d'ora saman kanta.......Ya mi'ke zaune sosai yana ya mutsa fuskarsa, hakuri kawai yake yi amma wannan kwanciyar da tayi a jikinsa ta ya mutsa shi, sosai ya d'an saci kallonta sai yaga tana hamma! da alamun baccin bai isheta ba, sai kuma ya mutsa fuska takeyi cikinta ne ya soma 'kullewa yunwa na sasakarta dama 'ka'ida ne idan tayi bacci ko yayane ta farka sai taci abinci.......Jikinta ne ya soma rawa, ta dinga zare ido tana mutsu mutsu ta rasa ya za tayi a yaron dake cikinta yana mata wani irin motsi da zillo tare danno mararta kamar me shirin fitowa waje, cikin rawar murya tace"Rashida ina kayanmu suke."? Rashida tayi saurin juyawa tana kallonta ganin yanda idanunta suka kad'a ne ya sanya ta gane yunwa takeji da sauri tace" Suna bayan mota." Still murya na rawa tace"To sai kizo ki dauko min kin san dai cewa nayi ki rike min a hannunki saboda zan iya bukatarshi cikin ko wane irin yanayi me zai sanya kisa a cikin akwati.'' Rashida tace."Yi hakuri anti Wasila ai mun kusa sauka." Tsaki taja tana motsa bakinta.....Ya kalli Rashida cike da kulawa yace."Menene."? Tace." 'kwai dafaffe ne Bitan ta bata shine tace na ri'ke mata a hannu na ni kuma wallahi na manta nasa a cikin jakar kayanmu gatacan a bayan motar." Shiru yayi kawai ya juya bayanshi da kanshi ya kinkimo jakar kayan nasu ya d'ora saman cinyarshi ya zuge zif din jakar ya soma dubawa.....Nan ya d'auko daurin leda yaluwa da dafa
ffan 'kwai a ciki kusan guda ashirin, a jikinta ya d'ora ledar ya mai da zif din jakar ya zuge kana ya maida ita inda take ya gyara zamanshi yana kallonta a nutse yace."Gashinan karkiyi kuka gama naga shi kike shirin yi." Shiru tayi masa ta cigaba da kokarin kwance ledar.......Kar'ba yay ya kwance mata ya d'auko d'aya ya soma 'bare mata , ya mi'ka mata ta kar'ba da sauri gutsira biyu tayi masa ta cinye.....Tana kallon hannunshi dake kokarin 'bare mata wani, Haka dai yayi ta aikin 'bare mata kwai tana taunewa sai da taci guda tara sannan ta hakura ya mi'ka mata ragowar ruwan swan din da yasha d'azu ta 'karba tana sha tana lumshe idonta sai yanzu taji dama dama a jikinta.
Uwani na tsaka da shanya kan katanga taji tsayuwar mota, dake katangar bata da tsayi sosai ana hange na waje kafin ta ankara taga Rashida ta fito daga cikin motar Wasila ma ta fito da sauri ta ajiye rigar dake hannunta ta nufi cikin dakin da take kwana mayafi ta dauko tayi hanyar fita tana kokarin yafawa a jikinta, a soro sukayi kicibus da Rashida sai ta rungumeta tana fad'in "Rashida sai yau kuka tunani dani ko? ke da waye a cikin mota ina Wasila ya jikin nata."? Rashida ta dinga kallon mahaifiyarta ta ganinta gaje gaje yayi masifar daga mata hankali, Wasila ta shigo ta gansu sai itama ta shiga bin Uwanin da kallo jikinta sharkaf da ruwa......Gashi duk tayi wani wujuga wujuga da ita. Uwani ta rumgume Wasila tana hawaye tace" Yarinyar nan kullum dake nake kwana nake tashi a raina Alhamudullihi jiki yayi kyau masha Allahu ga cikin ki ya girma dama ai nasan mutukar kun koma gaban mai allo zai kula daku mutum ne shi mai tausayi kuma yana kaunarku." Wasila da Rashida suka shiga binta da kallo jin abinda take fad'a kan mai allo wai yau Uwani ce ke yabon mai allo lallai duniya.
Gidan suka shiga gabad'ayansu, Wasila ta dinga bin gidan da kallo ko ina kaca kaca da kazanta iri iri ga wani wari na tashi da alama shaddar gidan ta cika tana bukatar agaji warin yayi yawa.....Ta dinga bin mahaifiyarta da wani irin kallo na tsantsar tausayi da jin kai. a hankali tace"Uwani wannan wane irin 'kuraje ne a jikinki? dubi yanda fatar jikinki ta kod'e kinyi wani iri duk kin rame."! 'Kwallah ta cika kwarmin idon Uwani tace"Ku mu shiga ciki babu komai." Bin bayanta sukayi suna mamaki tabbal akwai abunda ke faruwa da mahaifiyar tasu.........Kuluwa ta fito daga dakinta kirjinta daure da dadd'aud'an zani!!! kanta babu d'ankwali tamkar hammatar d'an iska yayi wani cibiri cibiri dashi dan saboda tsabar dauda gashin kan nata har ya soma d'aukewa da kanshi wani guri da a kwai wani gurin babu.....Ganinsu Wasila yasa tasha kunnu tana fad'in "Ku kuma yaushe kuka zo."? Wasila tayi saurin kauda kanta daga kallonta dan ji tayi tsigar jikinta na tashi kallon gashin kanta ya sanya mata tashin hankali amai na taso mata....Rashida tace" Yanzu muka zo Baba mun same ku lafiya."? Kuluwa tace "Lafiya lau ina fata dai yau zaku juya domin dai muma bamu da abinda zamu baku koda yake dai ga uwarku nan na neman kudi zata iya daukar dawainiyarku." Babu wanda yace mata ta tafasa ballanta ta sauke suka shige dakin ina Uwani ke zaune tana jiran shigowarsu......Nan suka tarar da ita a zaune a gefen wata guntuwar tabarma ta zabfa tagumi! Wasila ta dinga bin dakin da kallo daki sai kace zai rufta ya durkushe gashi babu labule babu ledar kasa sai wata guntuwar tabarma wacce take nuni da cewar nan ne makwancin mahaifitar tasu.....Kwallah ta zubo mata murya na rawa tace"Uwani wannan wace irin rayuwa kike ma'kaskanciya, wannan d'akin da kike ciki ya ru'be wallahi saura kad'an ya rufta bakya tsoro watarana ya rufta dake."
Uwani na hawaye tace"Ya zanyi Wasila! Ya zanyi? nice na cuci kaina na kuma cutar daku na tabbata da kina gidan Alhaji Ahmadu da duk wannan wahalar bamu shigeta ba, nasan da tuni munfi karfin gurin zama da ci da sha da suttura, na cuci kaina na cutar daku Ubangiji Allah ya yaye mana wannan masifa."!!! Ganin tana kuka sai suma suka fara kuka ta goge hawayenta tana fad'in "Idan dan kunga ina kuka kuma kukeyi to na daina yi sai kuyi shuru." Wasila ta goge fuskarta tana kallonta.....Uwani a nutse
ta soma basu labarin wahalar da takesha a gidan da yanda kullum take cin ruwa sai kace agwagwa.
Wasila tace"Ai dole sanyi ya kamaki Uwani wannan wace irin masifa ce ace kullum mutum na cikin ruwa dubi fatar jikinki ta kod'e ta bushe ga wasu kuraje marasa kyawun gani sun feso miki a jiki.
Uwani tace"Wai sunanan ina sha musu magani da ai sunfi haka yawa a jikina." Wasila ta shiga girgixa kanta tana tunanin yanda za tayi ta kubutar da mahaifiyarta daga wannan ukuba.
Uwani ta kalli Rashida tace"Wai waye ya kawo ku a mota ne."? Rashida tace"Alhaji Ahamadu ne mijin aunti Wasila." Da sauri ta kalli Wasilan tana neman karin bayani......Rashida itace ta shiga fada mata yanda al'amura suka faru.....Uwani ta dinga washe bakinta tana fad'in "Alhamdullhi Allah nagode maka daka amsa adduata kullum.burina mutumin nan ya dawo garemu naji dadin wannan zuwan naku kuma yau zanyi bacci harda munshari." Wasila tace"To sai ki sauya kaya kije soro ku gaisa dan da kunya a shigo dasu wannan 'kazamin gidan." Uwani ta mike da sauri ta bude jakar kayanta ta dauko atamfar data rage mata dan duk kayan da tazo dasu Kuluwa ta sace taje ta siyar, sai dai kawai in ta fita taga kayanta a jikin mutane idan ta tambayesu sai suce kuluwa ce ta siyar musu shaddar wasila ma data sace gidan ma gari ta kai suka siya.........Suna kokarin fita daga cikin gidan Kawu Madu ya shigo gidan yana washe bakinsa hannunsa rike da kud'i sabbin 'yan dubu dubu kar kar dasu......Kuluwa yake kwad'awa kira ta fito daga d'aki da saurin gaske dan har zaninta na 'kokarin fad'uwa ta rike da kyau! tana fad'in "Malam ya akayi ne." Yace."Ki fito kizo ki dangwali arziki ki barshi ashe yarinyar nan Wasila matar babban mutum ce, ikon Allah yafi gaban wasa! Kuluwa kinga uban kudin da mijinta ya bani yana waje shi da abokinsa sunzo cikin wata 'karuwar mota kamar jirgin sama."! A d'amauce! Kuluwa tayi hanyar waje tana tafiya kamar zata kifa 'kasa saboda sauri! Kwata kwata ta manta a halin da take ciki babu dankwali da riga daga ita sai daurin kirji.....