← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 23 OF 108

Sashe 23

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 11:49 pm] +234 803 238 4602: 'Yr bngr Sys
*22*
Yana fitowa da shirin zuwa masalaci yaci tuntube da ita a bakin 'kofa yayi saurin matsawa yana dan haske ta da wayarshi, ta bude idanunta da suka ci kuka suka 'koshi ta zuba a kanshi....Wani irin mugun haushinsa da tsanarsa ne ya kamata haka kawai ya daukota ya rufe a gida yana azabtar da ita, Da sauri ta mike tsaye! yayi saurin kaucewa ya bata hanya ya dauka dakin zata shige sai yaga tayi kansa ta cikwokwiye shi tana kuka." Ka dauke ni ka mayar dani inda ka dauko ni ba zan iya wannan rayuwar ba bana sonka kan me yasa zakaje ka sanya a daura maka aure dani ai wannan zalinci ne, Wallahi gwara na kashe kaina kan in zauna da kai na tsaneka." kuka take hai'kan! tana sake rike masa riga sai shigewa jikinsa takeyi gashi ya dauro alwala.
Yanda take gunjin kuka ya nuna masa da gaske takeyi abunda take fada har cikin ranta yake......Sai yaji rashin dadin hakan ranshi a bace ya ture ta daga jikinshi ya bar gurin da sauri! ta kuma mikewa a guje ta cimma sa ta baya ta rikeshi tam ta zagaye 'kugunsa da hannuwanta kirjinta na gogan bayanshi.....A zabure! ya juyo ya hankade ta hade da kifa mata mari! da hannu ya nuna ta "Kika sake kika 'kara ta'bani sai ranki ya 'baci! wallahi ba zan sake ki ba za kiyi ta zama a cikin kunci da bacin rai! ke da kin dauka nima sonki ne? Allah ya sawake na fada miki domin na karya alkadarinki yasa na aure ki shashasha kawai."! Juyawa yayi ya shige dakin....A gurguje ya sake sabuwar alwala yana jan tsaki ko yaya ta ra'bi jikinsa sai yaji sauyi a tare dashi abinda bai taba faruwa ba dashi.....Tana durkushe tsakiyar palon ya fito ko kallonta baiyi ba ya fice! yaji masifar haushin cewar da tayi bata sonsa yanzu ya soma zama da ita duk dan ya kuntatawa rayuwarta.

Can gidan kuwa Uwani da Rashida na ganin sha biyu na dare ta wuce sai suka hakura da jiran ta suka kwanta ba tare da wata damuwa ba saboda sun san dama ta saba irin wannan tafiyar wani sa'in ta kwana wani sa'in kuma ta dawo.......Gashi Rashida ta kira wayarta tana shiga bata dauka ba sai tayi zargin ko tana tare da mutane ne dalili kenan da ya sanya suka kwanta ba tare da sunsa wata fargaba ba a cikin ransu.

Bai jima da futa ba ta mike da azama! ta shiga dakin nasa nan idanunta suka sauka kan wayoyinta dake zube kan bed kusa da inda ya kwanta taga har da babbar wayarshi ma....Da sauri ta dauki babbar wayar ta tana duba contec numbar As take nema.....Sai taga ba kwata kwata babu sim card a wayar tayi saurin budewa wayar tana dubawa wai ko gocewa yayi taga duk babu, hannu na rawa ta dauki karamar ma taga itama ya cire sim card din gashi duka kan wayoyin babu numbar kowa ziro take........Hankali a tashe ta zube kan gadon tana rike kai! Wannan guy ya kassara ni! Innalilihi wa'ina ilahi raji'un! abunda take iya fada kenan jikinta na kyarma! babbar wayarshi ta kaiwa raruma hannu na rawa ta bud'e duka ta zare sim card din dake ciki ta zura cikin birziyarta rufe wayar tayi ta nemi guri ta zauna kan stoll tana jiran shigowarsa kwata kwata tunaninta ma baya kan ibadah burinta ta kubutar da kanta.

Tananan zaune ya shigo dakin...Kallo guda yayi mata ya ga alamun ba tayi alwala ba ballanta tayi sallah! Ya sha kunu tare da fad'in"Tashi kije kiyi sallah."! Ba tayi masa musu ba ta mike yabi bayanta da kallo tana muskuta d'uwawu cikin damammen wandonta da sauri ya kauda kai yana fadin"Mara kunyar 'karya." Sarai taji shi girgiza kai tayi tace"Wallahi kome za'ayi ba zan bayar da sim card din nan ba nima sai an bani nawa.

Sabon bursh ta bude ta matsa man goge baki a kai ta wanke bakinta tas ta dauro alwala ta fito.....Lifayar ta ta hango can karshen gadonshi ta haura kan bed din yana kwance yayi saurin gyarawa ganin kamar zata fado kansa, ba tare da ta damu ba ta dauko ta nad'a a jikinta ta nemi gefen kafet ta tada sallah! Yana kwance yana kallonta har ta tayar da sallahr.

Hannu ya kai ya dauki wayarshi yana dan dubawa sai yaga babu sim card ya bude wayar yaga babu ajiye ta yayi ya dauki karamar ita ya bude yaga ta cire! Murmushi yayi......."Ke! waye ya baki izinin daukar min waya kiyi min bunkice."? Kai tsaye tace"Nima waye yace ka cire min sim card din waya ta ina ruwanka da kaya dukanin sirrina yana waya ta ka duba min ni banyi maka bunkice a waya ba kawai na cire sim card ne sai ka bani nawa sai na baka."

Mikewa yayi zaune...sai ta zabura! ta matsa gefe da sauri! Hannu ya mika mata "bani Sim card dina tun muna shaida juna dake."

"Allah sai ka bani nawa zan baka." Tafada cikin dakewa da jajurcewa."!

"Nayi bunkice jiya a wayarki naga komai a ciki da irin mutanan da kike mu'amula dasu dalili kenan da ya sanya na cire sim card din, da da yanzu ba daya bane kina da aure yanzu ba kowa ya kamata kiyi mu'amula dasu ba sanna duk mutanan da naga numbarsu a wayarki basu da kirki babu wanda ban sani ba a cikinsu, ga yanayin yanda kika dauki wannan auran da rashin kima kina iya cigaba da mu'amula dasu dalili kenan da ya sanya na zare sim card din wayoyinki......Su kansu wayoyin anjima kadan zan bada kyautarsu ga mabu'kata." Ya kare maganarshi cike da rashin wasa.

"Ni wayoyi basu ne damuwa ta ba kawai ka bani sim card dina sunfi muhimanci a gurina idan kuma kace ba zaka bayar ba to kai ma naka sun mula."

Ya dan tsira mata idonshi yana kallo, kimanin minti biyu ya mike! Zabura tayi! Bai ko kalleta ba ya kwashi wayoyinta ya fita dasu a hannunsa.....Ajiyar zuciya ta sauke! ta rasa me yasa take jin tsoronsa duk lokacin da zai tunkareta....Tananan tsaye ya shigo dakin taga ya bude wardrobe din shi short nickar ya dauki da wata t_shart mai karamin hannu ya sanya a jikinsa ta matse shi sosai duk wasu hallitunsa suka bayyana....Ya zauna gefan bed yana kallonta, saurin sunkuyar da kanta tayi Yace."Mara kunya zo ki bani sim card dina zanyi kiran waya ko bakya ji."
'Ki tayi! Yace."Idan nazo nan fa ba zakiji dadi ba.

"Nifa ba zan bayar ba sai ka bani nawa." Tafada muryarta na rawa ganinshi a haka ya sanya mata wani irin shau'ki wanda bata ta'ba shiga cikinsa ba sai taji tana sha'awar taji ta kwance cikin fafaffadan kirjinsa....Idonta lumshe! wanda shi kuma a lokacin ya mike ya iske inda take tsaye sai hucin numfashinsa taji! Tana bude ido ta ganshi daf da ita ya babbake gurin ko kyallinta baka gani ya rufe ta ruf a jikin bango (garu) Kauda fuskarta ta shiga yi ya sanya hannu yana juyo da fuskar tana sauke kauda fuskarta gabanta sai faduwa yake!!! Cikin hosky voice yace."Ina kika kai min sim card."!? Shiru tayi masa....Ya sanya hannunwansa ya kama hannunta yana dubawa. bude masa tafikan hannayen tayi ya laluba tsaf babu! Ha'bar ta ya d'ago ya tsurawa le'bunanta ido....Ta fuzge fuskarta daga hannunshi Yace."Ke! zafin kai! zaki nuna min ko."? Ta sanya hannu ta ture kirjinsa da fadin"Ka dauko min nawa sai na baka naka." Saukar hannunsa taji kan nonowanta! Ta 'kwallara 'kara! jikinta na makyarkyata! sam ba tayi tsammani ba!!! Ya d'an 'bata fuska kad'an "Meye haka."? Yafada yana kallon 'kwayar idonta.

Shiru tayi tana so ta gudu ya sake matse ta da bango " Idan baki fito min da sim ba zanyi miki tsirara inyi miki sintir duk inda sim card dina yake sai na gani."

''Nima ka dauko min nawa." Tafada murya na rawa "Taurin kai ne dake Na fada miki dalilina amma tunda kin fiso nayi miki sintir irin naku na 'yan jagaliya to bari kiga." Da sauri ta buge hannunsa da ya dora kan blet din da ta matse 'kungunta dashi!! ya sake mai da hannunsa gurun fuzga daya yayi wa blet din sai gashi a hannunsa.....Ihun! hauka take masa tana tutture shi.....Ya 'bata fuska sosai da hannu daya ya hade dukanin hannuwanta ya rike ya daga sama ya kalleta ta kalleshi taga ya hade rai! sai hawaye ya wanke mata fuska da alama dai guy nan sintir din zai mata!!! "Ki daina 'bata hawayen ki a banza na fad'a miki ko a cikin wandonki kika 'boye min sim card sai na ciro kaya na." Yana gama maganarshi ya fara kokarin zare mata dogon wandon jins din dake jikinta.....Kafafunta ta sanya ta dinga harbinsa dasu tana bugunsa ko kallonta baiyi ba sai da ya zare mata wandon tayi saura daga ita sai pant! Kuka take tana masa Allah ya isa! Ya kalleta da jan ido "Kar ki 'kara yi min Allah ya isa."! babu wasa yayi maganar tace" To nima ka daina cire min wando wannan ai wulakanci ne." Yace."Ke! kika so a wulakanta ki." Hannu ya sa xai zare pant din! Sai ta kwala kara ta lauye ta lanjare! ta kanannad'e jikinta a jikinsa tana masa magiya! "Tsaya in dauko maka kar ka cire min wando! dan girman Allah ka tsaya kar ka tozartani!." Dariya yake so yayi amma ya dake! baiyi ba yace."Oya! maza dauko min." Yafada yana sakin ta.
Chapter 23 · 0% Book details