← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 68 OF 108

Sashe 68

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Uwani ta bishi kan tabarma suka zauna tare Kuluwa ta 'karaso gurin hannunta rike da ludayi ta zauna kujera 'yar tsugo tana fad'in "Eh ai gwara muji bayanin komai domin mu samu kwanciyar hankali." Uwani ta share hawaye a hankali ta soma warwarewa masa abubuwan da suka faru da rayuwarta ita da 'yayanta komai bata rage masa ba sai da ta fad'a mishi......Kuluwa tace"Duniya kenan yanzu ke Uwani bakiji kunya ba, wato lokacin da kuka samu kudi kuka samu dad'in duniya baki tuna damu ba sai da wahala ta taso ki sannan zaki tuna damu ki kwaso jiki ra'be ra'be da 'yaya kizo ki d'ora mana nauyi to ba zata ta sa'bu ba! Mu ba zamu dauki nauyin ki kuma mu d'auki nauyin 'yayanko ba, Dan haka gobe gobe yaran nan zasu bar gidanan suje can dangin mahaifinsu tunda suna raye, kema abinda yasa ba zamu kore ki ba saboda mun san ko kinje can gidan Kawunki ba zai kar'be ki ba saboda haka ke kad'ai zamu ri'ke saboda kece tamu."
Kawu Madu yace."Kwarai kuwa Kuluwa wannan magana taki gaskiya ce, Yaran nan baxa su zauna mana a gida ba sabida bamu da hakki a kansu dan haka kamar yanda kika fada hakane kwana guda zasuyi su bar mana gida suje can cibiyarsu.........Uwani ta dinga kuka tana fad'in "Haba Kawu ku duba al'amarin fa kada kuyi min haka bani da kowa sai 'yayana bani da uwa da uba bani da miji sai 'yayana su nake gani naji sanyi a raina." Kuluwa tace"To ai tunda hukuncin da muka yanke bai miki ba to sai ki bi 'yayan naki haba! wannan 'kulafucin son 'yaya dame yayi kama.'' Ta mike tana jan tsaki ta shiga dakinta.....Kawu Madu ma ya mike yana fad'in "Na fad'a miki Uwani na yanke hukunci Kuluwa ta yanke hukunci saboda haka shawara ta rage gareki." Ya buge babbar rigarsa ya 'kara gaba.

Wasila da Rashida kam! basu ciwo ba dalili dama sunfi son su tafi can garkon shiyasa sukaji dadin hukuncin da Kawu madu ya yanke a kansu amma basu nunawa mahaifiyar tasu ba, sai suka shiga kwantar mata da hankali da fad'in ko sun tafi insha Allahu zasu dinga zuwa a kai akai suna dubata.....Uwani dai jinsu kawai takeyi abin duniya ya taru yayi mata yawa bata ta'ba nadamar rayuwa ba irin yau.

Kuluwa ta dinga shige da fice a tsakar gidan tana sakin 'ba'kaken maganganu wanda ya sanya jikin Uwani yi sanyi taji a zuciyarta gwara kawai su Wasila su bar gidan dan ba zata iya jurar rashin mutuncin kulawa tana aibata mata yara da kiransu karuwai watarana tana ganin zata iya mayar mata da martani kan maganar da takeyi, ta dinga jin wani irin d'aci! da bakin ciki a raina ashe haka abun yake da ciwo a duk sanda aka danganta d'anka da wannan suna (karuwai) gaskiya ta gode Allah da ya bata 'yaya masu hankali da hange nesa tasan da bada hakan ba da tuni sunanan da kuluwa ke kiransu dashi ya tabbata tunda ita da kanta ta dinga turasu karuwancin, tagode Allah da yasa wannan cikin dake jikin Wasila ta sameshi ta hanyar halak ba haram ba.

Kuluwa na ganin irin tsarabar da suka kawo sai ta hau washe bakinta ta dauki turmin atamfofi irin na leda guda biyu tace wannan ni zan d'inka in sa a jikina wannan yadin kuma na malam ne, sauran kuma Iya mai waina da Tabawa su kasafta a tsakaninsu." Su dai kallonta kawai sukeyi duk tabi ta kwashe kayan ta shige dakinta dasu sai murna takeyi ko Kawun ma bata nunawa ba.

Sai dare suka samu suka sanya abinci a cikinsu shima abincin Inna Tabawa ce ta kawo musu cikin katuwar Samira shinkfa da wake ne da manya da wani uban yaji da yaji gishiri da citta! haka suka cuccusa dan gwarashi kan narkeken towon dawan da Kuluwa ta kawo musu, Wasila dai kad'an taci tasha maganinta ta nemi gefenan tabarma ta kwanta tana mai da nuffashin wahala.............Duhu sosai gidan babu wadatacciyar fitala sauro da kwari ka sukayi sallama! Wasila ta gigice ta dinga soshe soshe kukan sauro duk ya cika mata kunne! Uwani tace "Ku tashi mu koma daki mu kwanta kunga mutanan gidan sun shige sai mu kadai a tsakar gida ga sauro." Rashida tace "Yanzu cikin wannan kazantar zamu mu kwanta ga yara nasan suna fitsarin kwance." Uwani tace"To ya zakuyi ai da zama cikin sauron nan gwara cikin rumfar." Wasila tace"Uwani ku shiga ku ku barni anan Rashida ki dauko min zanin atamfa cikin kayanmu in rufe jikina." Uwani tace"Akwai fa damuwa kwanciyar ki anan." Tagoge kwallah tace"Uwani nan yafi min kan in shiga dakin nan inzo ina kakarin amai da daddare d'an abincin da naci ya dawo, kuma wannan matar tazo tana miki masifa."

A sanyaye Uwani tace"Shikkenan ai." Ta mike a hankali ta shiga dakin rashida tabi bayanta......Nan su kaga yara birjik a rumfar ko wanne ya wargaje kafafunshi wasu sun soma sakin fitsari abinsu sai barci suke.....Uwani ta ra'ba can wata kusurwa ta karkad'e wani buhu ta shimfida ita kuma rashida ta nufi dakin Kuluwa dan jakkunan kayan nasu na cikin dakin........Nan ta tarar da Kuluwa ta bude musu kaya sai bunkice takeyi musu, tana ganin rashida sai ta diriri ce ta hau ya'ke...."Am...dama ai nace bari na gyara muku kayan naku in adana muku su guru guda." abinda tace kenan tana sosa kanta....Rashida bata ce komai ta dauki zannuwa uku na atamfa ta fito daga dakin....Ita kuluwa tana ganin rashida ta fita daga dakin sai ta cigaba da bincika kayan ta dauko manya manyan shaddodin Wasila masu uban stone work ta d'aga 'kasan katifarta ta sanya ta mai da katifar......Da sauri ta gyara jakkunan kayan ta fito daga dakin tana zare ido.

Wasila kudindine jikinta tayi. ita kadai kwal a katon tsakar gidan ko tsoro bataji gari yayi shiru sai kukan tsintsaye kawai ke tashi.......... Cikin ikon Allah bacci mai nauyi ya dauketa ta dalilin magungunan da takesha

Fitowar Kawu Madu daga dakinsa ne ya tayar da ita Sai taji ana kiran sallah da alama asuba tayi, Kawu Madu ya kalleta yana mamaki yace." Ke anan kika kwanta." Sunkuyar da kanta tayi kawai sai ya girgiza kanshi ya nufi bandaki da buta a hannunsa........Yana fitowa ya daura alwala ya nufi masalaci,
Kasa shiga bandakin tayi sai kawai tayi gaggwar tsugunawa a bakin rariyar tayi fitsarinta ta kwara ruwa, kana ta matsa gefe guda ta daura alwala ta bar gurin.

Shimfidar data kwanta ta dauke ta cire dankwalin kanta ta gyara hijab dinta ta tada sallah......Uwani da rashida suka fito a tare suma alwalar suka daura nan tsakar gidan sukayi sallah domin dai cikin rumfar babu guri bayan haka kuma ko ina kasa 'kafarka fitsari ne.

Suna zaune a tsakar gidan gari yayi haske Kuluwa ta fito tayi alwala ta goge bakinta da gawayi kana ta shiga kichin ta kunna wuta ta dora ruwan kunu sannan ta nufi daki domin yin sallah.

ၥYaran dake dakin suka soma fitowa su kusan bakwai wasu jikinsu da fitsari wasu babu ba tare da sunyi alwala ba suka soma wasa a tsakar gidan wasu kuma tuni sun fice waje da abubuwan wasan su......Su Wasila suka dinga mamakin wannan rayuwa....Nan rashida take shaida musu abinda taga kuluwa nayi musu da kayansu....Fitowarta yasa tayi saurin yin shiru to itama Kuluwar a kunyance take dan haka sai tayi saurin fadawa kichin tana sosa kai! Wasila abin dariya ya bata sai ta shiga girgiza kai tana fad'in ''Ni dariya ma take bani wallahi." Rashida tayi dariya kasa kasa tana kallon kicin din.

Wani tsalan kunu ta kawo musu cikin kwanon sha da kufuna guda uku sai 'kullin sikari akai....Uwani ta gaisheta tanayi mata sannu suma suka gaisheta Ita kuwa ta kasa tsayawa a gurin kunyar hada ido da rashida take......Tana shiga kicin Wasila ta saka fuskarta cikin hijab taci dariyarta ta koshi, kai mara gaskiya dai ko a ruwa gumi yake.

Fitowa tayi daga kicin din da katon farantin silba da narkeken d'umamen towo an yanyanka shi sai miya tsululu towon sai iyo yake cikin miyar....Ta kalli rashida tana fad'in 'kawata ga d'umame nan idan kunsha kunun sai kuci kwaji dad'in tafiya da karfinku." Rashida tace"Mungode Kuluwa." Da sauri ta bar gurin tana kwalawa yaranta kira wai suzo su dauki kununsu da duk ta zuba musu a kufuna 'kudaje sai bin bakin kufunan sukeyi.....aikuwa da d'ai- da d'ai yaran suka dinga shigowa suna daukar kufonan kunun suna sha ba tare da sun wanke bakinsu ba.

Kawu Madu ne ya shigo da sauri yana fad'in "Ina Wasila da Rashida." Sukace gamu Kawu Yace." To maza ku fito ga motar abokina ya kawo ice yanzu zai fita cikin gari sai yaje ku a tasha ku shiga mota." Suka mike da sauri Rashida ta shiga dakin domin dauko musu jakar kayansu, dama tasu daya ce ta uwani daya.

Uwani ta mike tana yakar zuciyarta hawaye ne yake so ya 'balle mata tana mayar dashi, suka je bakin kichin din da Kuluwa ke ciki tana zaune dirshan gabanta da karon bokintin da ta dama kunu tana katsewa gefanta kuma tukunyar miya ca bude ga ludayi a kasa....Uwani tace"Zasu tafi." Sai ta hau washe baki tana fadin"Bari na taso inyi rakiya ni kuwa me zan baku. 'Yayan nan."? Fitowa tay ta shiga dakinta da sauri ta dauko wata yar takarda fara ta mikawa rashida tana fad'in 'Kawata ga yariruka kwa sanya ku gaishe da kawunan naku." Rashida ta karba tana godiya tabi bayan Wasila da Uwani da suka riga sukayi gaba.
Chapter 68 · 0% Book details