← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 62 OF 108

Sashe 62

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Tace"Uwani duka fa kudin nan saura dubu goma sha biyar ciki zamuyi kudin mota kana abinda yay saura a kudin mu siya musu tsaraba kin san dai ba zamu kwashi jiki muje musu gari hannu rabbana ba." Uwani tace"Ni dai bani kudi bana son wata magana." Mikewa tayi taje ta dauko mata ta bata Uwani ta mikawa rashida da fad'in"Kai masa kudinshi ai yayi mana mutuncin ma." Rashida ta kar'bi kudin da sauri ta fita.

Uwani ta zauna tana zauna kan kujera tana jan tsaki tare da cire mayafinta tace"Banta'ba ganin mara kirki da mutunci irin wannan mutumin nan ba wallahi, Duk wannan xaman da mukayi muna jiranshi 'karshe cewa yay ba zai fito ba sai dai mu dawo gobe saboda tsabar shi bashi da mutunci." Wasila ta dan bude idonta tana kallon mahaifiyarta ta ta mayar da idonta ta rufe tace"Sai fa dana fad'a miki kingani dai ai da idonki munyi asarar kudin mota a banxa." Uwani tace"Aikam gobe sai mun sake komawa dan baza fa mu tafi ba bai san da cewar kina tare da cikinsa ba.

Cikin jin haushi tace"Wai dan Allah Uwani dole sai ya sani ? dik ranar da ya kamata ya sani zai sani ni bana son haka wallahi na fad'a miki wahala kawai zaki sha da asarar kudin mota ba samun ganinshi zakiyi ba dan mugun dan wulakanci ne in bai sa kansa yin abuba babu me sa shi yayi dan haka kawai ki hakura idan kuma kince dole sai kin sake zuwa to ni bani da kudin motar da zan baki."

Uwani jikinta yay sanyi tace"Ai shikkenan tunda kin'ki cikin a jikinki yake kuma kece kike wahala dashi yau da lafiya gobe babu lafiya, saboda kulafuci kin'ki bari a zubar dashi! kuma kin'ki bari a sanar da meshi ni ina ganin idan an fad'a masa kina da ciki zaiyi wani abu akai dole ne ya bayar da kudin rainon ciki in da zaki masa kinga ai zasu taimaka mana ko."

''Uwani kyaleshi kawai dan Allah insha Allahu Allah bazai hana ni abinda zanci ba duk ranar dana haihu da kaina zan kai mishi d'anshi amma ba zamu dinga zuwa gidanshi muna zama cikin rana ba sai kace masu neman gafara."

Uwani tace"Ai shikkenan tunda haka kika ce." Rashida ta shigo tana fad'in"Wallahi wata masifaffiyar yunwa nakeji sosai bari na dora mana taliya tafi sauri." Da sauri ta shiga kicin din....Uwani kuma ta mike ta nufi daki tana surutai....Yayin da Wasila ta rufe idanunta tana jin dama Allah bai hallice ba ta *Astagafirullah! sautari bawa yakan fad'i wannan kalmar a yayin da ya shiga cikin wani yanayi mara dad'i sai ya dinga ji dama ya mutu ko kuma dama Allah bai halliceshi ba, Wa'iyazubillahi! Ai cikakken mumini baya zama haka kawai ba tare da Allah ya jarrabeshi ba, mutukar kaga a'lamuran ka na tayi dai-dai a duniya to ka binciki kanka, Ubangiji naso ya jarrabi bawanshi shi kuma bawan ya kar'bi jarrabawar hannu biyu tare da ya'ki da tawakkali kan cewar Allah ne yayi masa ba wani ba, Cikar mutum shine yarda da kaddara mai kyau ko mara kyau! babu kyau dan Allah ya jarrabeka ka dinga jin kamar ko baya sonka ne A'a sone ya jawo haka dan ba kowa yakewa abinda yayi maka ba, idan ka kar'bi kaddara da jarrabawar da yayi maka shi kuma sai yayi maka tagomashi me kyau! Allah kasa mu dace*

*******

Bayan sati uku al'amura da dama sun faru ta 'bangaran Ahamdu da Wasila ko wane bangare babu dad'i bangaran Ahamdu na cikin tsananin takura da masifaffiyar sha'awa dan har jiyya ya kwanta sai da Dr Nasir ya dorashi kan magani tukkuna ya dan samu sa'ida amma dai duk da haka duk daran duniya sai yayi hauka a dakinshi lokaci 'kankani ya zabge! kullum cikin 'bacin rai yake har khalifa yaso ya fahimci damuwa a tare dashi amma bai tambayeshi saboda ya soma zargin ko Allah ya soma ta'ba shi shima ai dama ba zai sha ba sai ya fuskanci kalubale tukkuna.

'Bangaran Wasila kuma Al'amura sun tsanantaa domin wani irin ciwon ciki takeyi sosai da sosai wanda ya sanya ta yanke shawarar zuwa babban asibitin murtala dake cikin gari a duba......Ana ya gobe zasu tafi Pataskum suka shirya ita da Rashida suka nufi asibitin murtala Muhammad da tsakiyar birin kano.

Saboda yanayin yanda takejin rashin 'karfi a jikinta ya sanya ta nemi guri ta tsuguna Rashida tabi layin kar'bar kati ta kar'bo mata kana ta mike suka kama layin ganin likita.............Dr nayi mata kallon farko ya gane tana jin jiki saboda ya hango rashin wadataccen jini a tare da ita da damuwa da kuma rashin bacci! Ya tambayeta abinda ke damunta, nan ta shaida masa cikinta ne ke mata ciwo sosai sai kuma zazzabi da jiri! Dr yace."Kina da ciki ko."? Daga kanta tayi hawaye na kokarin zubo mata.....Rubuce rubuce yay jikin wata farar takardar yace."Maza kije kiyi scanning yanzu ki kawo min." Ta kar'ba ta mike a hankali ta fita.....Rashida na tsaye jikin wata bishiya ta hango fitowarta ta karasa tana tambayar ta tace"Rashida muje lamco de yace sai nayi scanning! Rashida taji kwallah na kokarin zubo mata a idonta tace"Anti Wasila Allah ya rabaki da wannan cikin lafiya yana baki wuya Wallahi." Girgiza kanta tayi ta sanya hannu ta d'auke hawayen da ya sauka kan kuncinta cikin zuciyarta tace"Ameen." suka kama hanya suka fita wajen asibitin inda gurin Scanning din yake.......Allah yaso ta sako dubu biyu da dari biyar cikin jakarta shiyasa komai yazo da sauki.....Suka shiga gurin suka kama layi....Mai siyar da pure water ya kawo mata keda hufu ta siya a take ta shanye uku ta bawa rashida daya tasha....Kamar jira ake tasha ruwan mararta ta shiga wani irin juyi tana murd'a mata sosai takeji zafi zufa! sai yanko mata takeyi, cije bakinta take tana kiran sunan Allah har layi yazo kanta ta mike da kyar ta shiga dakin scanning din da kyar ta hau gadon......tana cijewa da daurewa gami da kiran sunan Allah aka ga mai mata ta sauko, a hankali ta gyara zaninta ta karbi sakamakon ta fita tana cire 'kafafu da kyar......Rashida ta rike hannunta suka fita, a hankali a hankali suke tafiya har suka isa gate din shiga cikin asibitin.....dai-dai lokacin kafafunta suka ri'ke gabakid'aya ta kasa d'agasu! Salati ta soma sai ta tsugune! a gurin tana kiran sunan Allah, Rashida ta tsuguna kusa da ita tana kuka hannunta gam! gam! da nata fad'i take "Anti Wasila sannu tashi mu shiga ciki dan Allah kiyi hakuri kinga mutane na wucewa." Jirkitattun idanunta ta d'ago tana kallonta dasu gumi duk saman goshinta hannunta na rawa tace"Rashida mutuwa zanyiiiii ni ka d'ai nasan irin ciwon da nake ji a marata." Rashida ta goge hawayen fuskarta hankali a tashe ta soma waige waige a gurin tana neman wanda zai taimaka musu.

Littafin na kudi ne.....!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasp numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
*BINTA UMAR ABBALE*🎉🎉🎉
[14/08, 12:04 pm] Farida Books: 'Yr Bngr Sys
*55*
Wata matace ke 'kokarin shigowa asibitin hannunta rike da kati ta kusa yin tuntu'be da Wasila dake durkushe tana rike cikinta......Da sauri tace"A'a ya kuke zaune anan ko ba haihuwa za tayi ba."? Rashida ta goge hawaye tace"Ba haihuwa zatayi ba Daga scanning muke shine ta kasa tafiya cikinta ne ke ciwo." matar tace"To maza kamata muje wancan rumfar ai nan kan hanya ce."Rashida ta kama hannunta ta dora kafadarta matar ta riko kugunta suka mikar da ita tsaye.......Horn din da ake zabgawa ne ya sanya matar juyawa a fusace tace"Mutane babu uziri shikkenan dan kana cikin abin hawa na 'kasa bai da 'yanci sai ai ta zabga masa horn mtsss! ta karashe maganar tana tsaki hade da dan matsawa motar ta kunno kai cikin asibitin.........Hafsa dake draving ta dan juyo tana kallonsu, sai kawai idanunta suka saukan Wasila tana sunkuyar da kai hade da rintse idonta.....Da sauri ta samu guri tayi parking ta fito.....Zeey dake kusa da tace"Ki shiga ki fito ni inanan." Tace"Zeey fito dan Allah Wasila ce matar governor ina tsammanin bata da lafiya fito da sauri." Zeey tai saurin bude motar ta fito......Suna karasa inda suke Hafsa tace"Sannu Wasila baki da lafiya ne."? Jin muryar Hafsa yasa tayi gaggawar dago kanta tana kallonta, a hankali ta lumshe ido bakinta ya bushe 'kamas! ta d'aga mata kai.....Hankali a tashe Hafsa ta kalli Rashida dake share kwalla tace"Kunga likita? kuma meke damunta dan da kagani tana cikin matsala sosai." Rashida tace"Munga likita har yace taje tai scanning to daga dawowarmu ne sai kuma jikin ya rikice." Hafsa tace"Muga scanning din." Ta mika mata da sauri ta bude tana dubawa....Da sauri ta dago tana kallon wasilan Ciki! mamaki takeyi sosai lallai babu yanda Allah baya tsara lamarinshi......Tace"Zeey dan Allah ku kamo ta keda Kanwarta ta muje." Wayarta tayi gaggawar fito dashi ta soma kiran 'kawarta dake asibin mai suna Aliya likita ce ta mata, tace"Aliya ganin nan na shigo asibitin ku amma ina tare da mara lafiya." Aliya tace"Okey ku shigo ofis dinmu ina shirye shiryn tashi ma dan dai kawai kince zaki shigo ne." Tace''Gamunan." Har da ita gurin rirrike Wasilan suka mikar da ita tsaye.......Sai me suna fara tafiya jini ya soma zirarowa daga kafafunta.....Salati suka sa Rashida ta dinga kuka tana rirrike wasilan da fadin"Innalilihi wa'ina ilaihi raji'un." A gaggauce Aliya ta karaso gurin, a take sukayi gaggawar dora wasila kan wani keke kai tsaye dakin 'yan 'bari Aliya tace a nufa da ita.....Hafsa Rashida hankalinsu yayi masifar tashi.....Hannu na kyarma ta kira wayar Khalifa ta shiga shaida masa halin da ake ciki....Lokacin ma yana hanyar zuwa gidan abokin nashi dan haka kawai sai ya juya akalar motarsho zuwa asibitin
Chapter 62 · 0% Book details