← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 34 OF 108

Sashe 34

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Littafin na kudi ne........!
Kika futar min da book! Ke da Allah! Kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: 'Yr Bngr Sys
*31*
Koda ya shiga dakin kai tsaye toilet ya nufa yayi wanka ya fito sanye da rigar wanka, tsayuwa yayi gaban mirror ya goge jikinsa kana ya shafa vasilin a jikinsa gami da turaran jiki ya sanya Karamar t-shart mai yankakken hannu da boxer tamkar wani sauri dan 20 years haka ya dawo kuruciyarsa ta fito fili dama kuma in dai zai sanya 'kananun kaya haka yake zama dan saurayi sosai suke masa kyau sai da kuma bai da ra'ayin sanya su ya fita 'karkarin shi ya sanya a gida kawai....Parlor ya fito ya nufi daining komai tsaf tsaf Rabe ya jere masa kayan abinci babu alamun an ta'ba komai a gurin.....Cikin mamaki ya fara bude kulolin abin bai ga alamar wani ya d'iba, ya zuba iya dai-dai cikinsa yana ci a nutse yana had'awa da lemo, tunaninsa duk ya ta'allaka ne kan yarinyar babu shakka shima sai yanzu da ya zauna yayi nazarin abinda yayi mata yaga bai kyauta ba, bai kamata yayi nufin tozarta uwarta a gabanta ba duk lalacewar uwarka ba zaka so wani ya ci mata mutunci a gabanka ba, amma baya jin ko da wasa zai iya tunkarar ta da niyyar ya bata hakuri idan ta gaji da fushin za ta daina........Sai misalin sha biyu da rabi ya bar palon.....Yau kadai da zai kwanta shi kadai a dakin sai yaji wani iri tsayin kwanakin da tayi a gidan tana kwana a dakinsa har ya saba da hakan duk da kafin suyi bacci dukaninsu sai suyi fada sau nawa hakan nayi masa dadi in dai zai ga giftawarta a dakin, shi kanshi ya fahimci zuciyarsa ta damu da yarinyar kuma ya soma zargin wani abu ya soma ziyarta zuciyarsa dangane da yarinyar.....Da kyar! bacci ya dauke shi mai cike da tunani da mafarkin gashi yana saduwa da ita.

To itama nata 'bangaran hakane ya kasance....Tun rana da suka rabu ta kudiri aniyar bar mishi dakinsa tunda ya kirata da kazama, har yana mata gorin daki kana kuma yana cin mutuncin mahaifiyarta a gabanta yasa taji sam ba zata iya had'a numfashi dashi ba domin wani irin tsanar sa takeji a cikin zuciyarta, haka ta kwana ba taci abinci ba tun bayan abincin da taci da rana har garin Allah ya waye babu komai a cikinta.

Shida dai-dai na safe! Ya fito daga bedroom dinshi cikin shigar Kayan motsa jiki wani wando ne da rigarshi masu dan kauri wandon iyakacinsa gwiwa kuma ya matse masa jiki sai rigar mai yankakken hannu itama ta kamashi sosai power dinshi ya fito kafarshi na sanye da booth, ya nufi kofar fita ba tare da yayi tunanin buga kofar dakinta ba yasan 'batawa kansa lokaci zaiyi kawai idan ya gama abinda yake ya dubata.......Ke'batancen gurin da gym dinshi yake girki ya nufa, Ya hau kai ya soma yi babu ji babu gani Garba da Hani na tsaye a gefan hagunshi da damanshi, Ya jima kan Gym din kafin ya sauka ya kwanta kasan gurin yana hutawa, sararin samaniya ya zubawa ido yana kallo yana mai da numfashi Garba ya miko masa sassayan ruwan swn ya mike zaune ya karba ya fara tuttulawa cikinsa, a kuwa gumi ya yanke masa kamar wanda ya watsa ruwa, wata iriyar kwanciya yayi ya soma training a haka ya kai ya kawo haka ya dinga yi ko wace jijiya dake jikinsa ta mike gashin jikinsa ya mike tsabar yanda jikinsa ke budewa, sai da ya kai kimanin minti talatin yana mota jikinsa a kwance kana ya saurara, ya kar'ni karamin towel dake hannun Hadi, yana goge jikinsa

Kira ne ya shigo wayarshi dake hannun Hadi yana daga kwance ya mika hannunsa ya 'karba, Hajiya babbah ce! mikewa yayi zauna ya kara wayar a kunnanshi ya risinar da murya yana gaisheta ta amsa da sakakkiyar murya tana tambayarsa iyali! sai yaji wani iri jin abinda tace wai ya iyali? ya waske da fad'in"Lafiyarsu lau hajiya ya gida kwana biyu uzirrika sun sha kaina ban samu na shigo mun gaisa ba." Tace."Aikam dai jama'a nata cigiyar ango ranar da nayi yini na da jama'ata kowa haka ya hakura, duk sunayi maka Allah ya sanya alkairi." Ya amsa da "Ameen Hajiyata mybe gobe ki ganni insha Allahu." Tace."To to ai sai mu d'aga tamu tafiyar tunda zaka zo da mun shirya zuwa gidan naka tare da matan Kawun ka Almu." Yace."To babu laifu Hajiya sai kunzo din zan tsaya jiranku duk da ina da babban uzirin da zai fitar dani goben amma babu matsala naji dadin zuwanku." Tace."Ai ba za'ayi haka ba kuma kada mu katse maka hanzari." Yace."Ko wane irin hanzari gareni idan ina neman albarka dole in tsaya in saurari zuwanku." Taji dadin maganarshi sosai tace"To Allah yayi maka albarka Ahamdu kaima Allah ya baka 'yaya masu yi maka biyayya." Ya amsa da "ameen ya rabbi nagode. Sallama sukayi ya mikawa Garba wayar kana ya mike da towel din a hannunshi yana karkade gwiwarshi da ta dan 'baci! Yace." Garba zan shiga in kwanta in huta yau babu in da zani Khalifa nan zuwa tare da iyalinshi idan ya kira waya kace na kwanta nasan sai bayan axuhur za su shigo lokacin na matse insha Allah." Garba yace."Okey sir zan fad'a mishi insha Allahu." Ya kama hanyar shiga cikin gidan.......Suka ce a tashi lafiya Yallabai." Ya amsa da "ameen." Yana daga musu hannu.....Dai-dai lokacin da ta fito daga dakin da take a dai-dai lokacin ya shigo palon......Sai da ta kusa faduwa saboda razana! masifaffiyar yunwa ce ta fito da ita wacce take baraxanar cinye mata 'yan hanji taji zata mutu ta futu afujajan domin samawa kanta abinci....Shi kuma wannan motsa jikin da yayi cikinsa kamar anyi masa yasa haka yake ji sai kokawa 'yayan hancinsa sukeyi...Kalon kallo aka shigayi tsakaninta dashi, fuskarsa akwai alamun sassauci ba kamar ko da yaushe ba, Juya tayi ta koma dakin fuskarta babu walwala har yanzu haushinsa takeji......Girgiza kai yayi ya nufi daining din, Rabe ya shirya break fast kamar yanda ya saba, a nutse ya had'a komai da kanshi ya zauna yana karyawa hankali a kwance.

Gefan bed ta zauna ta zuba tagumi! abin duniya yayi mata yawai wai shin ya za tayi da wannan kad'dararran auran da aka la'ka ba mata, komai na rayuwarta ya tsaya! ta taso da kwajinta da bajinta an tsugunar da ita guri guda, wai me take jira ne? da ba zata nemawa kanta mafita ba, Wata zuciyar tace mata "Ta ina zaki nemawa kanki mafita cikin wannan gidan dake tsautsare da matakan tsaro? Shawarar Camas! itace abun dubawa dole duk haushinsa da takeji ta saki jiki dashi ta samu ya bata Pose dinta domin tsira da muhiman abubuwanta dake ciki, sashe na zuciyar ta yace mata " Kinga idan yaga kin saki jiki a gidan kin karbi auran hannu bibbiyu to zai dauka kin hakura xaki zauna zaman auran dashi kuma zai sassauta matakan tsaro a kanki daga nan sai ki samu damar guduwa abinki ki kai su 'kara kotu daga shi har malam mai allon.! Wannan shawara ta yanke a zuciyarta.

Yana gama break fast dinshi ya nufi bedroom dinshi wanka yayi ya fito ya shiya still cikin 'kananun kayan dai, farare tas riga t_shart da wando 3Qutar mai aljuhunai gaba da baya, gaban rigar hoton zuciya ne an rubuta heart da bakin rubutu, sosai yayi kyau ya taje saisayayyiyar sumarshi mai tafe da sajensa cikin tsari! ya fesa turarenshi mai dadin kamshi, har yayi nufin kwanciya sai idanunsa suka sauka kan ledojin da ya shigo dasu jiya da daddare , 'Kananun kaya ne ya shigo mata dasu yasan za tayi amfani dasu tilas watarana, daukar ledojin yayi ya bude dakin......Idanunsa suka sauka a kanta zaune kan kujerar daining din da cup din tea a hannunta tana kurba tana hadawa da plantain, Ya karasa kusa da ita saitin kafafunta ya dure ledojin ''Gashinan nasan zasuyi miki amfani watarana." Kamar yanda bai kalleta ba sanda yake maganar haka itama ko inuwarsa bata kalla, Har yayi nufin barin gurin sai kuma ya tsaya ya d'an kalleta da gefan ido, Yarinyar nada wani irin madarar kyau! gani yake har yanzu bai gama saninta ba kullum sai ya sake ganin abinda ke burgeshi a jikinta....."amm!!! Magana yayi niyyar yi sai kuma ya dagata, Ta kalleshi sa kwala kwalan idanunta da suke furgita 'yan maza! ta wani risinar da kwayar idon cikin tashi tana masa wani malalacin duba, ta lura da akwai magana a bakinsa sai kawai ta dauke kanta tana cigaba da kurbar tea din a yangace sai kace wata d'iyar sarakai!! Hakan da tayi masa yasa yaji wata irin shakkar ta abinda bai ta'ba faruwa dashi ba kenan ace yana jin shakkun yiwa wata d'iya mace magana, Dauriya ya aro a take yace."Idan anjima muna da baki! nasan dai zaki shaida babban abokin nan nawa Khalifa, shine zai zo tare da Iyalinshi."! Ya kare maganar idanunsa tsaye a kanta.

Ta'be bakinta tayi ba tare da tace masa komai ba.....Yasan taji abinda yace, sai bai tsaya sauraran iskancin da take masa ba ya kama hanya ya shige bedroom dinshi ya kule yayi kwanciyarsa.

Tana kammala breakfast din ta dauki ledojin da ya ajiye mata ta shiga dasu dakinta.
Chapter 34 · 0% Book details