← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 18 OF 108

Sashe 18

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Cikin wata lafiyayyiyar lifaya ta fito Tana baza kamshi turarruka masu tsada da sanyin kamshi, Tayi ado da gold 'kirar dubai masu jajayen stones a jiki shi kanshi gyaran gashin da tayi wa kanta abun kallo ne tamkar wata balarabiya haka ta zama babu shakka kudi na iya canza mutum nan take Wasila ya zanzu dai da zata shiga cikin labarawan Itopia sai ta saje dasu saboda yanda fatarta ta goge ta 'kara fitar da kalarta chocolate color dama can haka kalar fatarta take Rashida ce fara itace ta d'ebo haske babansu Uwani kuwa ba za'a kirata fara ba kuma ba za'a kirata baka ba kusan kalar fatarsu daya da Wasilan amma dai yanzu ta Wasilar tafi kyau da gogewa, takalmi mai tsayi ta sanya kasancewar ba ta fiye tsayi sosai tana tsaka tsaki dai! Hannunta rike da pose da key na motar ta take takawa sannu a hankali.....Camas dake zaune na latsa waya ta kalleta "Wow! Kinga yanda kikayi kyau kawata, gaskiya lifayar nan ta miki kyau wallahi ke kin jima bakiyi kyau irin na yau ba tamkar wata amarya lalle ne kawai babu a hannunki da kafafunki.'' Murumsi tayi tace" Haka kawai yau nace bari nayi shigar bare bari ashe nayi kyau."? Camas! ta kwalawa Rashida kira ta fito daga kicin....Ganin Wasila ya sanya ta rude! "Aunty Wasila kece dan Allah nima ina son lifayar nan ki siyamin wallahi kinyi kyau! sai kallonta takeyi tana dariya Camas tace " Wai tambaya takeyi tayi kyau shine na kira ki ki fada mata." Rashida ta hau kod'ata "Wallahi aunty Wasila ko makaho ne yazo kusa dake ya tsaya sai ya kiyayi kansa babu wanda zaice kin hada jinsi da bahaushen mutum kamar wata balarabiya." Ganin yanda suke sambatu ya sanya ta dinga musu dariya...Uwani ma ta fito daga daki ta dinga nata shirma da zasu fita ta dinga yiwa 'yar tata kirari sai kace wata maro'kiya ita Wasila ma dariya suka bata tace"aikuwa dai tunda shigar lifaya nayi min kyau zan dawo yin irinta....

Suna shiga motar kiran As ya shigo wayarta ta dauki wayar tana dan ya mutsa fuskarta.....A nutse tayi sallama da sauri ya amsa yana fad'in "Gani a bakin gate din gidanki ki fito kawai muje mu dawo dan ma dai nayi alkawari ne da sai nace mu bari sai gobe ma futa yanzu aka kirani a waya karfe goma dai-dai muna da metting da shugaban 'kasa kin san tun safe ya shigo gari yanzu haka suna tare da mai girma governor."

Tace."To mai zai hana mu bari sai gobe." Da sauri yace." Ai ni kuma ba zan fuskanci komai ba gurin metting din nan mutukar banyi tozali da kyakkyawar fuskar nan taki ba." Murmushi tayi ta kashe wayar ta kalli camas tace"Ga d'an anace nan ya iso kawai ina zama na wai na shirya muje shan iska komai abunsa dole ya hakura dani wallahi wutsiyar rakumi tayi nesa da kasa

Camas tace"Tunda dai yaki hakura ba sai kiyi kwance kwance ki kwashi rabonki ba." Ke dai kawai fito muje dare nayi kudi kam ai kamar mahaukaci haka yake samun a account. " Camas taji inama itace dan a zahiri As yafi Alhaji Ma'aruf sakin hannu shiyasa taso ace As din ne ke mu'amula da ita tasan da tuni ta wuce gurin........Kamshi turaranta shine ya buwaye shi, yana draving yana kallonta idanunsa sun kada sunyi jawur babu shakka yau Wasila ta kaishi makura ga bukatuwa da ita yana ganin koda bai shiga wannan ramin ba a'kalla dai ta bashi dama ya d'an rage zafi a jikinta....Da kyar suka isa 'katon gurin hutawar wanda sai wanda ya amsa sunansa ke zuwa gurin......gurin tamkar rana ko ina haske tar tar jama'a nata shigowa da motacinsu da yawa daga ciki tare suke da mata wasu karuwansu wasu matayen su kowa harkar gabanshi yake.........As yayi kwance a gabanta yana lumshe mata shegun idanunsa da suke cike taf da sha'awarta duk sun kankace saboda jaraba, ganin yana matsowa jikinta ne yasa tayi saurin matsawa tana 'bata fuska.....Yace."Yana da kyau yau daya ki bani dama ko yaya ne na ra'bi jikinki babu shakka zuciyata na azabtuwa da so da kaunarki ki bari na rungume ki ko zanji dadi a jikina"

Ranta a bace ta kalleshi "Haba As wai yaushe ne zaka daina yi min irin wannan maganar? na sha fada maka ni ba 'yar iska bace amma ka kasa fahimta ko dan kana ganin Camas! kawata ce shine nima kake zargin halinmu daya da ita, Wallahi da zanyi karuwanci da tuni nayi amma ni ba layina bane kaje ka nemi karuwa ta debe maka kewa bani ba, idan kudin da kake turo min da wannan niyyar ne to dan Allah daga yau kar ka sake kuma tunda ka kasa daukata a matsayin abokiyarka to ka goge numbarta dake wayarka bana bukatar wata mu'amula ta sake shiga tsakanina da kai. Mikewa yayi zaune yana marairace fuska yana so ya kama hannayenta ta fuzge da karfi ta mike tsaye da sauri jikinta na rawa...Camas na can tare da wani alaji suna zance ta iskesu rai a 'bace tace" Ni zan wuce gida Kya biyo bayana." Mutumin yace."A bari nazo na kaiku mana." Ko sauraransa ba tayi ba tayi hanyar futa....Ita ko Camas! ganin alhajin nada kumbar susa a tare dashi sai tace"Rabu da ita Alhajina idan da wata bukata da kake nema a gurina yi min magana kawai kar kaji shakka." Ya shafa fuska yana lumshe mata ido yace."Muje mu kama daki zuwa gobe da safe sai na sallame ki." Ba tare da wata doguwar jayayya ba tabi bayanshi.

As yabi bayan Wasila yana nema neman duniya bai ganta ba guri ne babba ga jama'a na shiga suna fita ya fita bakin titi ya jima a tsaye yana waige waige bai ganta ba, haka ya koma ciki domin daukar motarshi anan kira ya shigo wayarshi kan lokaci ya kusa da zasu zauna metting dole ya nufi government house din ba dan ransa yaso ba yaso ko yaya ne ya rage zafi da Wasila amma ya dauki alkawarin komai tsantsaninta sai ya rusa shirinta.

Tana ganin futar motarsa ta fito daga inda ta 'buya babu shakka As so yake ya yaudareta ya rabata da budurcinta wanda da ta jima tana tattalinsa, tabbas zata janye jikinta dashi da lamuransa tunda ta lura shi baya abu dan Allah.

Koda ta fito titin tsif! babu abun hawa na haya dama kuma ba kasafai a dai-dai ta sahu ke shigowa gurin ba saboda babban titi ne na masu hannu da shuni yawanci motocin gida sunfi karakaina a kan titin.....Tsoro yasa ta kasa tsaida motar kowa sai ta kama hanya ta dingi tafiya ga cokalelen takalmi a kafafunta.

Tana daf da futa babban titi motar ta fito daga wani babban layi mai dauke da dogwayen gina gine, dole tasa ta ratse a gefe domin ta bawa mai motar hanya, haushi da takaici ya turnuke ta ganin yanda mai motar ke dallare mata fuska da hasken fitilar motar....Ta sanya hannunta ta kare fuskarta tana jan tsaki!!!

Ahamdu dake gaban motar gabanshi ya fad'i Allah yasa dai idonshi ba gizo yake masa ba, sai da suka zo daf da ita ya tabbatar da zarginsa Itace! ma'kale a jikin bango tana jira su wuce! sai ya shiga tambayar kansa, Yarinyar nan daga ina take a cikin wannan daran? shin ita da waye? kuma meye ya fito da ita daga gida. Bashi da me bashi amsa dole sai ita, da sauri ya sanya Garba ya tsayar da motar ya bude motar da zama ya fito ya iske inda take ma'kure!

*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

*Free Pege19*
Saboda yanayin hasken gurun ya sanya tun kafin ya karaso kusa da ita ta ganeshi gabanta ne yayi wata mummanar faduwa da azama! tayi kokarin barin gurin.....Taku biyu yayi ya cafki hannunta guda.....Cak! taja ta tsaya tana mai da nuffashi domin ganinsa ya sanya jikinta kyarma wanda shi kanshi sai da yaji a jikinsa sakamakon rike hannunta da yayi, Sai da ta dan samu nutsuwa sannan ta juyo fuska a had'e! Suka hada ido dashi yana tsaye shima tashi fuskar babu alamun wasa....Kafin tace"Komai ya mangantu.....'Karfe goma sha biyu na dare kina waje a matsayinki na 'ya mace mai daraja kin watsar da wannan 'kimar da Allah ya baki kin mai da kanki tamkar tunkiya kiyi nan kiyi can cikin dare saboda rashin sannin ciwon kai kin mai da kanki tamkar namiji namijin ma irin wanda bai san darajar kanshi ba."
murmushi tayi mai ciwo tace."
Idan hakane kai ma
Ashe kana d'aya daga cikin jinsin irin mazan da ka fad'a yanzu, Kai ma me ya fito da kai da daddare idan ka yarda da kanka? kana kirana tinkiya kai kuma sai ka kira kanka da bunsur......! kamar ya sanan sunan da zata kirashi dashi yayi saurin kife ta da mari! jikinsa na kyarma! yace."Ahir!! d'inki ki kirani da wannan suna! na kira da tinkiya din domin sunan da ya dace a kira ki dashi kenan, dube ki don Allah wai ke kinyi kwalliya kina yawo sa'ko da loko kina rabawa jama'a jikinki a banza job wane wawa ya jaki ya jaki ki bishi saboda rashin martaba kai ya jama'a ba zasu kira ki da sunanan tinkinya ba."!?
Chapter 18 · 0% Book details