← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 52 OF 108

Sashe 52

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 6 min read

Nan Wasila ta shiga warware mata abubuwan da suka faru da ita gidan Ahamdu da yanda ya dinga sumar da ita yana mata kamshin mutuwa amma kuma bata fada mata cewar mu'amular aure ta shiga tsakaninta dashi, ta fada mata irin bindiddigin da yake mata da furucin sa kan gidan da suke ciki cewar idan ya kar'bi mulki sai ya tuhumeta idan ya kama ma ya daureta sai ya daureta kan kud'adan mutane." Uwani tace"To ai kema baki sukayi ba sata Kikayi ba saboda haka kada ki wani damu duk barazana ce babu abinda zai iya yi miki, Amma kuma nafi so, gobe mu kama hanya mu wuce potsikum sai 'kura ta lafa sai mu dawo mu san abinyi, sai dai kawai yaji kira daga kotu." Tace."To shikkenan yanzu dai dole zanje banki in samu na ciro kudi masu dan kwari a hannuna kafin zuwa goben."

Da misalin karfe biyar da rabi na Yamma Wasila da Camas! suka fito daga bakin union duk wasu kud'addanta ta sanya ankwashe mata su daga asusunta an maida accont din Camas kudin sun tasamma miliyan hud'u da d'aruruwa, Cikin rashin dubara da wayo ta barwa Camas! Atm din a hannunta suka wuce gida,

Sai gab da magariba suka isa, Uwani tayi musu girki mai dad'i da nama sukayi sallah tukkuna kafin su zauna zaman cin abincin, kira ya shigo Wayarta....Sabida tsabar yanda ta haddace numbarshi yasa ta gane, gabanta ya dan fadi sai dai ta dake! tayi masa sallama Ya amsa yana tambayar ta mutan gida tace"Sunanan kalau." Yace."Ina fatan kin shirya ko dan ganinan kan hanya." A kumbure tace"Abinci zanci." Murmushi ya saki wanda har sai da taji sautinsa a kunnanta, taji tsigar jikinta ta mike, yayi amfani da wata iriyar murya "Ki aje min nawa."! Ta sakejin wani bakon yanayi a jikinta jin muryar da yayi amfani da ita, Sai tayi saurin fad'in" To! ta kashe wayar dan bata so ya samu nasarar kashe mata jikinta....Uwani tace"Shine ko."? daga kai tayi kawai tana jujjuya abincin, Jin muryarshi kawai ya sanya mata kasala da mutuwar jiki!Uwani tace"Kiyi da azama yana zuwa ku tafi ni wallahi so nake inga komai ya faru na gaji da wannan abu." Wasila ta sakejin wani karfi da kuzari gami da dakiyar zuciya yazo mata, ta dan caccakali abincin ta ajiye cokalin kana ta 'kame kan kujera tana jiran zuwanshi.

Littafin na kud'i ne....!
Kika fitar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 10:55 pm] +227 98 36 59 34: *_Afuwa jiya nayi mistake gurin sa numbar a mai makon 46 sai na sake sanya 45 nasan dai babu matsala tinda book din na tafiya kan tsari.......VIP 'Yar Banga! sannu ku da 'kokari! ina 'kaunarku kuna fitar da book ina 'kara samun costomars😅🤝🏻 masu karantawa baku biya ba kuma sannuku da kokari 😎yawwa! guys mu cigaba da gashi!! ku d'auki abu mai amfani na cikin book d'in nan ku watsar da mara amfani......Muje zuwa_*

'Yr Bngr Sys
*47*
Kimamin mintuna goma sha biyar da kiran wayarshi, ya sake wani kiran yana sanar mata da cewar gashinan a bakin gate dan bai shigo ciki ba ma saboda yanayin akwai hadari sosai dan har an soma iska da walkiya yace maza maza ta fito su tafi. Ta mike da sauri tana gyara jakarta, Uwani tace"Kada fa kiyi da wasa kina samun kufcewa ki nemi mafaka ki 'buya idan ya bar gurin sai ki fito, Tace"Ai As ma yana gurin dan yayi min bayanin yanda zanyi." Camas dake danna wayarta tace"Ni kam inanan sai gobe ma had'u a gest house din As nasan dai can zaki kwana ko." ? Tace"E mana amma da wuri zan fito xamu wuce fataskum sai komai yayi normal kana mu dawo." Tace."To shikkenan." Rashida dai na zaune bata sanya musu baki ba cikin maganarsu duk haushi suke bata har Uwanin sam basu san inda yake musu ciwo ba, shiyasa tayi al'kawarin daina sanya musu baki a maganarsu idan ta kwa'be musu ita 'yar kalloce tinda ta fad'a musu gaskiya sun'ki ji.

Har bakin gate Camas da Uwani suka rakota, sai da ta fita tukkuna suka koma ciki.....Tana fita aka soma yayyafi da sauri ya bude mata motar ta shiga tana gyara mayafinta, ya kunna motar suka bar gurin, Sai da suka hau titi sosai ya d'anyi gyaran murya yana kallonta yace." Ya mutanan gidan ina fatan kin mi'kamin gaisuwa gurin momy kafin naje da kaina." babu yabo babu fallasa tace"Eh tace tana amsawa." Motar tayi shiru bayan maganarta ruwa ya soma yin 'karfi gabanta na cigaba da fad'uwa!
Saboda yanayin goslow din dake tsakanin tal'udu da goran dutse ya sanya yayi yanke hanya ya shiga ta wajan ma'kabarta zai bi ta 'yan rake yana ganin hakan zaifi masa saukin shiga unguwarsu tasu ta tudun yola, duk wannan yanke yanken da Ahamdu yake yi da mota, Motar su *Mada!* na biye dashi amma saboda tsananin taku mutum ba zai gane hakan ba, Sosai yake gudu sam baya son ruwa yayi karfi wanda zai tilas tashi yatsawa a kan hanya shiyasa ya kara karfin motar, Wanda ita kuma sai zazzare ido takeyi kamar kace kyat! ta ruga a guje tunani takeyi ko tana ina su *Mada!* zasu fito........Kasancewar ruwan ya soma 'karfi ya sanya masu siye da siyarwar dake kan titin kansakali mahad'ar 'yan rake ya sanya suka fara kwashe kayaiyakinsu kowa na neman tsira titin tayi shiru hanya tayi tsit! sai saukar ruwa sai kuma ababen hawan dake ta sharara gudu kan kwalta kowa na so ya isa gida.

Yana fitowa daga tsukin titin kansakali ya hau titi sosai, yana kara karfin motar! Kawai motar su *Mada!* ta daki tashi motar wanda ya sanya hannunsa ya goce daga kan sitiyarin motar ta gangara wani layi! Dake titin dama motoci basu fiye binshi ba ya sanya jama'a basu ankara ba, bayan haka kuma ga ruwan da akeyi babu kowa a gurin masu wuce wa a baben hawansu basu fahimci komai ba dan dik wanda yaga motar Ahamdu cikin layin zai dauka a fake take dan bata nuna komai ba da zai dauki hankalin jama'a.

Ya jima yana kiran sunan Allah kafin yayi gaggawar bud'e motar ya fito ruwa na dukanshi, Can ya hango motar su *Mada!* ta silalo gurin.......Ya tsaya yana kallon motar har tayi parking kafin ya ankara yaga sun fito su uku ko wanne fuskarshi rufe da ba'kin abu, dake namijin duniya ne bai wani razana ba sosai! suka durfafo inda yake! Mada ya fito da wata bindiga yana saita shi da fad'in"Kud'i ko kuma mu dauki ranka."! Yace."Ai babu mai daukar ran mutum sai wanda ya halliceshi! *Lauje* ya kai wa bakinshi duka da sauri ya rike hannunsa yana girgiza masa kai! Yace."Kuce kawai na baku kudi sune bukatar ku amma kada ka kuskura ka ta'ba min lafiyata."

Zuruf! ta bud'e motar ta fito, sai ta fashe da kuka tana wata makyarkyata sosai tsoro takeji gani takeyi anya su *Mada!* ne kuwa, ganin sun saita shi da bindiga yasa gabanta faduwa ta shiga kuka tana basu hakuri."
Chapter 52 · 0% Book details