Sashe 8
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Suna shiga motar sanyi Ac da kamshi ya bakunce su, Uwani ce a farko sai Rashida Wasila ta zama karshen shiga motar sai dauke kai takeyi bata so su hada ido dashi gashi sun zauna a site daya tana kallon fuskarshi ta mirror ya hade rai! sai itama ta hade nata ran! tayi kasa da kanta, ita sam wannan taimakon baiyi mata ba saboda babban abun kunya ne guy nan yaje yaga makwancinta duk da haka dai ba zata bari su shiga ciki ba a bakin titi zasu sauka.
Jin surutun da su Rashida yayi yawa yana nema ya karasa wata damuwar bayan wacce yake ciki......Sai ya sanya hannunshi ya kunna redio karatun alkur'ani ya soma a tashi daga bakin *Ahamd Sulaiman* Duk da haka dai su Uwani basuyi shiru ba sai surutu suke suna ta zancan 'barayin da suka tare su.
Gyaran murya yayi sai suka yi shiru suna kallonsa....Wasila ta dan ja tsaki kadan tace"Dan Allah kuyi shiru idan munje gida kwayi maganar haba."
Shiru sukayi basu sake cewa komai ba motar ta cigaba da tafiya.
A hankali ya dago idanunsa dake sakaye da gilas yana kare mata kallo ko da wasa baza kace ita yake kallo ba saboda yanda yake wani basarwa.......Yarinyar nada kyau! sosai sai dai bata da kunya ko kad'an! shi kuwa baya shiri da mara kunya marasa ganin girman na gaba dashi.
Dai-dai bakin titin 'yan babura Wasila tace"Ajiye mu anan ba sai ka shiga damu zamu karasa da kafafunmu.
Uwani tace"Haba 'yar nan ki bari mana a karasa damu mana mutumin nan fa taimakon yake yi kar ki katse masa hanzari." Dan Allah aunty Wasila ki bari a karasa damu." Rashida ta fadi maganar tana karyar da kai.....Sai magiya take mata kamar zatayi kuka."
Yace."Garba shiga da motar nan ka kaisu har kofar gidansu kar ka dakata maganar ta." Yace."Angama Yallaba.'!
Uwani tace"Mungode sosai Allah yayi albarka alhaji Allah yasa a gama lafiya, Allah ya raya zuria." Ya amsa da "ameen." yana duba wayarshi....Wasila kam! sai shan kunu takeyi sam bata so haka ba dan dai kawai sunfi karfinta ne.
Wani tsukakken layin suka shiga motar ta dinga gwajab gwajab!! tana cijewa......Ya dan gyara zamanshi yana duba yanayin ungywar kai da gani kasan unguwace ta marasa galihu gidaje kananu babu tsayin katangar arziki ga kwatoci duk sunbi hanya abun babu kyan gani sam unguwar bata yi masa ba, bai shiga mamaki ba sai da yaji muryata na fad'in"Tsaya anan ga gidanan ai." Yabi gidan da kallo yana mamaki! wai sunan angyara ansa kofa da lokacin buhu ne abun sai ya bashi mamaki dan adam ke rayuwa cikin wannan gidan rubabbe lokacin damuna mutum na cike da fargaba da alhini kar ya rikito masa amma su haka suke kwanciya hankalinsu kwance......Tausayi suka bashi yanzu ya gane abunda ya sanya yarinyar famtsama harkar Jagaliya talauci masifa ne! da'alama kuma su kadai suke rayuwa a gidan.....Tunaninsa ne ya katse lokacin da ya hangota tana bude gidan...Uwani da Rashida sai faman godiya suke masa, Ya bude wani guri a cikin motar kudi ya dauko a daure a kyaure! ya mika ma Uwani ta karba hannunta na rawa gwiwa kasa ta zube tana godiya yace."Tashi dan Allah kamar hakan bai dace ba nayi niyya ne na baku amma akwai 'yar shawarar da zan baku idan babu damuwa." Tace"To Alhaji Yace."Ki hana 'kanwarki harkar Jagaliya sam bai dace da 'ya mace ba ni zan taimake ku sannan idan kun samu mijin aure kuyi aure ni zan dauki nauyin komai naku." Sai Uwani ta fashe da kuka tana fadin "Alhaji labarinmu mai tsayi ne Wasila kuma ba kanwata bace babbar 'yata ce sai Rashida su kadai na haifa marayu ne babansu ya mutu tun kafin suyi wayon haka sannan duk dangi sun guje mu saboda bamu dashi mune muke ciyar da kanmu kaga kuwa har jagajiya ai sana'a ce bazan iya hanata ba tunda gashi ta rufa mana asiri."
Yayi shiru yana sauraronta tausayinta yaji ashe itace mahaifiyar yaran shi ya dauka yarsu ce, Ganinta tana kuka ya sanya yace." amma al'amarin akwai hadari a ciki tunda kun daukeshi a matsayin sana'a Allah ya taimaka." Uwani ta amsa da "ameen tana sake godiyar kudin da ya basu....Ahamad ya bawa Garba Umarnin tafiya Garba yaja motar suka bar gurin Wasila kuwa ta jima da shiga gida sai haushin tsayuwar su Uwani takeyi a waje Allah yasa dai ba ro'konsa suka tsayi ba tasan halin masifar kwadayi da roko na mahaifiyar tata.
*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko oragne_
*Free Pege10*
Suna shiga cikin gidan Wasila ta rufe su da masifa,"Haba Uwani nifa bana son 'karanta bisabillahi yanzu minti na nawa da shigowa cikin gidanan kuna can kuna maula da zubda mutunci dama tunda naji shiru nace to kun tsaya roko wane irin rayuwa ce ban saka kaina ba a akanku amma duk da haka sai kun watsa min kasa a ido idan kuka ce haka zaku dinga yi to wallahi zan barku da halinku ko na samu kudi in boye kaya na."
"Haba 'Yar nan, mutumin nan ya cancani a tsaya ayi masa godiya ba don komai ba sai dan taimakon da yayi mana a wannan zamanin ba ko wane mai kudi ne zai tsaya ya taimaki talaka ba yanzu idan da badan yazo gurin ba da me kike tunani zai faru tsakanin da 'barayin nan nasan wallahi sai sunyi mana tas! wannan budurcin naki da kike tattalawa su keta shi da wagari ya waya ai dole a tsaya ayi masa godiya ba abunda kike tunani ne ya tsayar damu a gurinsa shine dai yayi niyya ya bamu kudi kingasu ma."
Ta mika mata daurarrun kudin dake hannunta, Wani banzan kallo tayi wa kudin kafin tace"Yanda ya baku kudin to ku ajiye ko lissafawa bance ayi ba ni ina da a'kida idan ina son mutum a siyasance ina sonsa idan bana son mutum bana sonsa dan haka banga abunda kudinsa zasuyi min ba tunda dai ina dasu."
Uwani da Rashida suka saki baki suna kallonta da mamaki! wannan kudin masu tarin yawa zasu aje to akan me? ai su ba 'yan siyasa bane kuma ai ba ita ya bawa kudin ba su ya baiwa ballanta tace.
Wasila tace"Ko kuna so dai inyi muku bayani dalla dallah akan mutumin nan domin naga kudinsa duk ya furgitaku."
Uwani tace"To ai kece naji kina wata magana a wannan zamanin ayi maka kyautar kudi ka mayar gaskiya abin da kamar wahala."
"Uwani wannan guy fa shine dan takarar Governor a yanzu dashi suke fafatawa da Governor mai ci a yanzu kuma duk kudin da kikaga na samu ta bangaran harkar siyasar nan to ta dalilinsa ne dan akanshi muke jagaliyarmu saboda haka duk ranar da mai girma governor yasan da cewar ina bangare biyu a wannan harkar to yan kudin da nake samu zai hanani dazu fa cewa yayi zai zauna dani na fada masa dukanin bukatuna sannan kuma ya sauke mukamin wani a dora ni a kai nan gaba kadan ina ganin zan zama 'kusa a harkar dan haka banga amfanin da wad'annan 'yan kudin zasuyi mana gobe insha Allah kafin mu isa government house zan kai masa kudinsa har gida bama bukata."
Uwani tace"Kuma fa hakane maganarki Wasila duk ranar da governor ya gane baki da a'kida to kashinmu ya bushe gwara ki tsaya a bigire guda mussaman yanzu sune ludayin su yake kan dawo zamu kwashi roman da mukarad'iya gwara mu tsaya da kafafunmu kafin ya sauka.
Wasila tace"Ashe kin gane abunda nake nufi dan haka bani kudin na ajiyesu taimakon da yayi mana kuwa shine yayi niyya 'yan kudinsa baza su sanya ni na sauka daga a'kida ta ba." Uwani ta mika mata kudin ba dan ranta yaso ba sai dan ba yarda zatayi da 'yar tata.
******
Tunda suka doso layin suke ganin cincirindon mutane wasu na shiga wasu na fita ga 'katon gate din da ya zama security ga estate din a bude jama'a sunja dogon layi sai kar'bar tallafi sukeyi layin mata daban na maza daban.....Camas! tace"Kawata me yake faruwa ne naga mutane sunja layi." Wasila ta gyara ni'kab din dake sakeye da fuskarta tace"Zai wuce kamfen yake domin yaudarar al'umma amma dai bari mu tambayi wannan matar."
"Baiwar Allah dan Allah me akeyi anan gurin."? Matar ta tsaya tana washe baki tace" Tallafi mai girma Governor mu na gobe yake raba mana mata dubu goma maza dubu ashirin."
Wasila tace"Ke kin samu kenan."? Cike da farin ciki matar tace"Na samu mana gasu ma nasa a cikin jakata, zuwa zanyi na siyo gyada buhu biyu mu dinga soyawa da yara na kafin muga abunda Allah Zaiyi."
Wasila tayi murmushi tana jan tsaki tace"Kin san wani abu."? matar ta girgiza kai...."Zan baki baki dubu ashirin yanzu kije ki watsa masa kudinsa kice baki so kudinsa basu isa su siyi 'kuri'arki ba mulki kuma sai dai yaga anayi." Matar tabi Wasila da kallon mamaki.! Wasila tace"Ko dai kudin da na fada sunyi miki kadan ne to na kara miki talatin akai sun zama hamsin nasan dai zasu isheki kija jarin ko wace sana'a ce."
Matar tace"Bana son roman baka yarinya in fara gani a'kas! tukkuna." Wasila ta zaro jakarta dake rataye a kafada ta lissafa kudi dubu hamsin cif tace kin gansu a hannuna kina aiwatar da aikin dana saki zan baki su.
Laraba na ganin kudi dumus a hannun Wasila sai ta gigice! tace"To yanzu ya za'ayi na shiga gurinan akwai 'yan sanda sosai a gurin kuma suna ganin shige da ficen jama'a kana suna gane wanda ya fita da wanda ya shiga kuma kina ganin idan na aikata hakan ba za'ayi min komai ba."