← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 80 OF 108

Sashe 80

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 7 min read

Ta gane khalifa, d'ayan ne bata gane ko waye ba, a nutse ta zauna kusa da mijin nata ta shiga gaishesu, Alhaji Muktari ya shiga mamakin 'kan'kanuwar yarinyar wai itace matar abokinshi Yo ai wannan za tayi sa'ar babbar 'yarshi Sa'adatu, babi shakka dole abokin nashi yace bashi da sha'awar 'kara wani auran saboda yasan yana da wacce zai mori 'kuruciyarshi da tsufanshi.
Cikin kulawa yake amsawa ya dan tsokanta ita kuma sai sunkuyar da kanta take kunyar mutumin takeji sosai ganin kamar ma ya girmi mijin nata, Wanda sam ba haka bane Alhaji Muktari sa'an Amadu ne dan shima baifi shekaru arba'in da biyar ba , kawai dai dan yayi aure da wuri ne kuma yana da jikin girma ba kamar Amadu da bai da 'kiba ba, Tana zaune tana sauraransu suna hira duk ta 'kosa ta bar gurin ta d'an muskuta a hankali zata tashi, Ya ri'ke mata hannunta ba tare da ya kalleta ba ya juya suka cigaba da magana da Khalifa, tamkar zata fashe da kuka haka ta kalleshi to meye amfanin zamanta a gurin bayan sun gaisa ba sai ya kyaleta taje ta kwanta ba......Kirane ya shigo wayar Khalifa sai lokacin suka san dare yayi sosai sha d'aya da rabi Hafsa taji shuru bai dawo ba ta kira wayarshi, Ya mike da sauri yana kallon agogonshi, yace"Ashe dare yayi sosai sha d'aya da rabi yanzu." Duk sai suka mi'ke tare Alhaj

i Muktari yace."To Uwargida kuma amarya xamu tafi Allah ya 'kara sauki ya kuma saukeki lafiya insha Allahu muna nan zuwa ni da iyalina duk ranar da kika haihu." Tace"To Allah ya kawo ku lafiya mungode." Ta kalli khalida da yayi gaba hankalinshi duk yayi gida tace"A gaishe min da Afnan da momynta." Yace."Zasuji insha Allahu.......Ta dauka zai musu rakiya sai taga ya tsaya bakin kofa yana fad'in To Alh sai munyi kenan a sauka gida lafiya nagode da ziyara insha Allah nima ina nan tafe." Khalifa yace."Wai kana nufin daga nan zaka tsaya."? Yace."Meye a ciki to akwai gajiya a tare dani ina so huta ne." Khalifa yasha jinin jikinsa, ya kalli Wasila dake tsaye a kusa dashi yabi ya rike mata hannu gam kamar wacce zata gudu.....Yace." 'Kanwata ina fata baki mance abinda Dr Aliya ta fad'a miki ba ko." Wasila tayi jim!! Tana nazari sai kuma ta kalli Khalifan jikinta a sanyaye ta daga kanta.' alamun bata mance ba........A ranar da akayi mata d'aurin mahaifa Dr Aliya ke shaida mata cewar dole ne ta nemi wata hanyar domin biyawa mijinta bukata mutukar ana so cikin jikinta ya zauna lafiya to banda yawan sex da ayyuka masu tsauri, a lokacin da Aliya ke yi mata wannan jawabin sam bata d'aukeshi da mahimanci ba saboda tasan bata da aure lokacin, To da yake duk a gaban khalifa tayi jawabin yasa yanzu ya sake tuna mata kuma ta gane inda ya dosa, tabbas kuwa dole ne tayi taka tsantsar dan tayi bala'in sanin waye Amadu idan ya hauta ya dunga suburbud'arta mancewa yake da kowa da komai a lokacin shi dai burinshi kawai bukatarsa ta biya........Hannunta ya rike zugwi zugwi! ya nufi bedroom dinshi da ita, ya mai da 'kofar d'akin ya rufe da key, sai sannan ya sakar mata hannu, jikinta babu kwari ta nemi gefan gado ta zauna, shi kuma ya nufi toilet domin watsa ruwa.

Ya fito daure da towel ya ganta zaune tana gyangyad'i Gyaran murya yay ta zabura da sauri ta bud'e idonta tana kallonsa, gabanta ya fad'i ras! ganinsa daure da guntun towel! da sauri ta haye bed din ta ja blanket ta rufe jikinta har fuskarta, ita kam ko me zaiyi ba zata bari ya hau kanta ba gani take idan ya sa mata wannan 'katuwar abar tashi zata iya haihuwar dole....Ganin razanar da tayi ya bashi mamaki sai kawai ya girgiza kanshi ya bude sif ya dauko jallabiya da gajeran wando yasa a jikinshi, kana ya nufi ke'bantaccen gurin da yake ibadarshi, kafin ya isa kira ya shigo wayarshi ya dauka yana dubawa Khalifa ne, Yace."Dama dazu ina so nayi maka bayani to babu dama gaban Mutane.....Khalifa ya fad'a mishi sharud'an da Likita ta fad'a kan Wasilan ya cigaba da cewa ko za kayi kar ya wuce sau d'aya dan kar ka wahalar da yarinyar mutane kuma ka wahalar da d'an dake cikinta......Yace."Okey shine naji kuna magana da ita d'azu kuna wani 'boyewa."? Khalifa yace."Meye abin 'boyewa nifa zumud'in da naga kana yi ne yasa na tuna da maganar kai ma kanka ko ba'a fad'a ba ai ka d'aga 'kafa! A hasale yace."Kai kaga ki likita tace ko bata ce dama ni banyi niyyar yin komai ba dan haka sai da safe." Kashe wayarsa yay ya ajeta yana jan tsaki ya nufi kan dadduma......Khalifa kam nashi 'bangaran dariya yasa dan ganin yanda lokaci 'kankani zuciyar abokin nashi ta hasala....Wasila kam tun tana rawar jikin ta daina dan bacci me dad'i ne ya dauketa cikin bargonshi mai cike da kamshin turarirrkanshi masu dad'in 'kamshi da kashe jiki.

Littafin na kudi ne!
Kika futar min da book keda Allah! Kika karanta baki biya ba kema keda Allah! Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*'Yr Bngr Sys
*66*
Nafila yayi raka biyu bayan ya idar da sallahr sai ya bude al'kur'ani mai girma ya karanta iya yanda ya sawwa'ka ya jima hannunsa a sama yana addua sannan ya rufe da fatihatulkitabi ya shafa a fuskarshi, a nutse ya mike ya nufi bed din ya xauna yana kallonta bacci take sosai kuma daga ni tana jin dadin baccin a hankali yaja bargon ya shiga ya kwanta kusa da ita tare da d'an jawota jikinshi ya d'ora hannunshi 'kasan mararta yana shafawa a hankali a hankali bakinshi na motsawa da alama addua yake yi a nutse ya tofe musu jikinsu bakid'aya kana ya ja bargon sosai jikinsu ya rufe idanunsa yana adduar Allah ya taimakeshi bacci mai nauyi ya daukeshi, cikin ikon Allah kuwa baccin ya daukeshi, kuma baccin da ya jima baiyi Irinshi ba.

Wajejen karfe hud'u shaura na asubah ta farka da wata matsananciyar yunwa, jiki na kyarma tayi yunkurin mi'kewa, yay gaggawar rike ta idanunsa ya bude ke kyace dama ba bacci yake yi ba, Amadu bashi da nauyin bacci ko kad'an, a hankali yace."Menene."? Shiru tayi tana mutsika idanunta, sai ya mi'ke zaune yana me cire bargon dake jikinsu ya sanya hannunsa guda a jikinta ya shafa wuyanta, babu alamun zazzabi a jikinta, Yace."Menene? ko zakiyi wani uzirin ne? muryarta na rawa tace"Yunwa nakeji." Yace."Yunwa."? Daga kanta taji hawaye na kokarin zubo mata, Yace."Dama baki ci abinci ba kika kwanta."? "Naci dama duk dare ina tashi naci abinci." Ya shiga girgiza kanshi a hankali ya mike ya sauka daga bed din ya fita daga dakin

Kicin ya nufa yayi dube duben shi babu abinci sai kawai ya jona kettle ya dora ruwan tea yana tsaye yayi ya juye mata a cup ya nufi dakin dashi, lokacin ta fito daga toilet daure da alwala dan an soma kiran sallah." Ya aje tae din kam bedside yana fad'in "Ga tea nan babu abinci a kicin din wallahi." Zumbura bakinta tayi ita me zatayi da wani tea banda ya sata jin wata yunwar, Fita tayi daga dakin Yabi bayanta kicin ta nufa, ya tsaya bakin kofar kicin yana fad'in "Ki koma ki kwanta bari na tashi hajja sai ta sarrafa miki wani abun." Girgiza kanta tayi tace"Kawai tana baccinta sai a tasheta tayi girki nima zan iya." Shiru yay yana kallonta tana kunna gass cocar, Shi da kansa yayi alkawarin daukar dukanin laluranta baiyi tsammanin harda shiga kicin ba, a lokacin da suke tare a can baya bai santa da wannan cin abincin ba yanzu dai yafi tunanin cikin da take dauke dashi ne ya sanya ta, kicin din ya shiga ya kar'be tukunyar hannunta wai zai d'ora mata abincin......Tausayi ya bata ta kar'bi tukunyar taje ta zuba ruwa ta tazo ta dora tukunyar gefanta ta bude taga lafiyayyar miya wacce taji nama zu'ku zu'ku.....Sai kawai ta bud'e sto ta dauko supargetti guda d'aya, yay daurin kar'bar taliyar a hannunta, ta rike tana girgiza mishi kai tace"Ka barshi zan dafa babu wuya fa." Ya d'an tsira mata idanunsa itama shi take kallo tana sake jin wani irin yanayi a jikinta gaskiya ta lura ya mato akan sonta, da girmanshi da komai ya dinga biye mata da dukanin abinda take so.....Yace."Kin tabbata zaki iya." Daga kanta tayi yace."Okey bari nayi wanka da alwala na wuce masjid.'" ya wuce ta bishi da kallo tausayi tausayinsa take ji a cikin ranta.

Tana tsaye taliyar tayi ta tsaneta kana ta juye cikin fulas ta dauka ta nufi daki dashi, lokacin har yayi wanka ya sanja jallabiya hannunsa rike da cazbaha, sai kamshi yake ta matsa mishi hanya shi kuma ya fita ba tare da wani yace da dan uwanshi komai ba.
Chapter 80 · 0% Book details