← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 10 OF 108

Sashe 10

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

Maganganunsa sunyi mata zafi sosai! ta kalleshi tana girgiza kai *"Jagaliya da Banga* yanzu na fara." Tana fadin wannan magana sai tw zuge jakarta ta zaro kudinshi na jiya ta jefa masa "Wannan kudin da ka bawa Mamana da kanwata basu ishemu kallo ba saboda aban bamu wanda yaf.......... Taji saukar Wani bahagon mari a kumatunta! A razane! ta dafe fuska idanunta yayi jawur! Ya dam'ki! wuyanta ya sha'ke cikin hijab.....Ta dinga kyarma! tana kyafta ido!! Ganin idanunta sun soma shagid'ewa ne ya sanya ya saketa sai ta fad'i a gurin ragwajab! tana kakari! tare da rike ma'kogwaronta! kanta 'kas!! ya tsugana dai-d'ai kafafunta, A kausashe yace." Har yanzu baki san waye Ahamadu ba ko! ni zaki jefa da kudi! ke! wai shin ma dame kike takama ne.''!!! Wasila tayi shiru bakinta ya mutu har yanzu ma'kogwaronta suya yake mata wai! sauran kadan ta bakunci lahira......"Wallahi wallahi duk ranar da kika sake gangancin aikata min abu makamancin wannan sai kin raina kanki in yaso su wad'anda suke daure miki gindi su same ni da kansu ni bana tsoron kowa kije ki fada musu basu isa nayi dake ba su zasu zo da kansu mu fafata! mahaukata kawai wadanda suka dauki mulki wata tsiya kije ki fad'a musu ni *Ahamadu* ina jiransu suzo da kansu sa'ko na baki duk ranar da suka sake turo ki to zan huce fushina a kanki Tausayi da jin kai ya sanya nake kyaleki kina min abunda kike so kuma ina baki damarki a siyance okey tunda ke d'in dabbace! mara kishin kanta zan fara cin ubanki idan kin soma ji a jikinki sai kije ki gyara *BANGAR SIYASAR KI* Tashi! maza ki kwashe min wannan kudin da kika watsar a kas! dubban mutane nacan suna nema ke kin samu kina zubarwa saboda kina da masu baki....Ki shirya min kudina tsaf! a cikin kyaure kamar yanda suke tunda bakwa so akwai dubunku masu so."

Wasila ta yunkura ta tashi tsaye idanunta yayi jawur!!! Gefan hijab dinta tasa ta goge gomin goshinta ta ratse shi zata wuce!!! Tare ta yayi da kirjinsa ta dannata a jikin bango (garo) Sai ya zamana ma nuffashi da kyar take futarwa Gaggausan mutum irin wannan ya sanya mata nauyinsa ai sai Allah...."Ni zaki nunawa zafin kai ko."!? Yafada yana sake matse ta a jikin bango.....Kanta tasa ta daki kirjinsa dashi Yace."Idan kukan jini zakiyi anan gurin sai dai kiyi sai naga karshen tashen balagarki kiyi abinda nace kawai shine mafitarki."

Cikin 'kunar rai! tace"Ka matsa daga jikina ka matseni a bango domin ka cimma wata manufa taka akaina to Allah ya isa kudi kuma zan tsince dan karan kaina ba dan wani ba."

Ya matsa daga jikinta yana ya mutse fuska.......Bani da wata manufa da zan cimma akanki saboda na had'u mata iri iri wad'anda suks fiki komai kazama dake mai zanji a jikinki da kike wannan maganar." Shiru tayi masa ba tace komai ba ta hade masa kudinsa ya sanya hannu ya karba da hannu ya nuna mata 'kofa "Fice min a gida wannan shine karo na biyu idan kika kuskura kika sake shigo min gida to kin san abunda zai biyo baya."

Hijab! d'inta ta buge! tayi masa wani irin kallo mai nuna alamun akwai sauran kalubale tayi kwafa ta juya tana tafiya da sauri sauri!!! Hannuwa ya zuba cikin aljihu yana kallo ta tsaya ta daura niqab dinta kana ta murda kofa zata futa......Dake a kulle take daga waje, Hadi yazo da sauri ya bude mata ta fice da sauri tamkar zata tureshi.....Can ta hango Camas tsaye jikin wata bishiya ta nufe ta da saurin gaske sam! bata damu da kallon da mutanan dake gurin suke mata ba, saboda babbar dama ce ta samu domin cimma manufofinta a kansa.....Suna fita suka samu babur kai tsaye government house suka nufa.

*'YAR BANGAR SIYASA!!*
🌺 romantic love story🌺
*NA:*
*BINTA UMAR ABBALE 🍒*
*🌍Manazarta Writes asso*
_'Kungiyar masu nazari da aiki da Ilimi_
~~~~~~~~
*NA KUDI NE.......!*
_Ga masu bukatar karanta book din zasu tura #300 Vip gruop #600 accont din da za'a tura kudin.0542382124.......Binta Umar gtbank....Idan katin waya mutum zai tura sai ya same ni ta wannan numbars din....07084653262_08089965176 sai na fad'i yanda za'a biya kud'in.....Mutanan mu na Nijar idan kuna bukatar book din zaku tura dala dari ta wannan numbars.......90899076_88137740 katin airtal ko orange_

*Free Pege12*
Sai da sukayi nisa sosai Wasila ta cire niqab din fuskarta tana goge fuska Camas tace"Ammafa matar nan taso ta saka ki a bala'i wallahi dan naga guy ranshi ya 'baci sosai ni na dauka ma zan ga kin fito da fasashen baki! wallahi."
Ajiyar zuciya ta sauke tace"Bai fasa min baki ba amma ya mareni ya sha'ke min ma'kogwaro har na soma jiyo 'kamshin mutuwa! ammafa bai daki banza sai na kulla masa sharri nifa naji dadi da hakan ta faru wani plan zan shirya a kanshi ke dai kawai mu bar maganar sai munje gida tukkuna." Camas tace"Shiyasa naga kin fito a furgice! gaskiya Wasila akwai ki da jarumta wallahi da nice da tuni na karaya da wannan harkar akwai hadari a cikinta......"Camas idan kinga na daina banga to na cimma manufofina ne kawai ke dai ki cigaba da take mun baya insha Allahu wannan plan din da zan shirya shine zai janyo min arziki na har abadah."
Camas tace"Allah yasa kawata kice dai mun kusa daina yawo a babur din haya zamu mallaki motar kanmu." Murmushi tayi har fararan hakoranta suka bayyana tace"Ke dai lokaci Camas! Allah dai ya taimake mu." Camas! ta amsa da "ameen" kana suka cigaba da wata hirar.

Koda suka isa government house din Governor da sauran mukarrabansa suna dakin meeting sai da sukayi xaman awa biyu tukkuna suka fito lokacin har magariba tayi duhu ya shigo a gurguje suka gaisa kana Wasila ta fada musu abunda ya faru a gidan Ahamadu tace....Wannan damar tamu itace zata rusa duk wani shirinsa a gaban bainar jama'a al'amarin ya faru saboda haka da kaina zan shiga gidan redio in watsa maganar nasan wad'anda abun ya faru a gabansu zasu gazgata kaga da kanan shikkenan magana ta kare."

Governor Lawan Rabo yace."Mutukar wannan magana taki ta rusa shirin Ahamdu to ni Lawan Rabo nayi miki al'kawarin baki kud'in da zasu gigitaki! zan baki mamaki 'Yar gaske in har wannan plan din da kika shirya kan Ahamdu ya sanya ya janye kudirinsa na zama dan takarar governor a jam'iyyar *CPC."*
"Kar ka damu mai girma governor insha Allahu magana ta 'kare kujerar mulki kam kaine zaka cigaba da zama a kanta."
Tafada cikin karfafawa kanta gwiwa kuma tana sanya ran insha Allah bukatarta zata biya.

Basu dawo gida ba sai kusan karfe goma na dare dan daukarsu sukayi a mota suka nufi wani kayataccen hotel sukayi ciye ciye kana sukayo guzirin wasu, har bakin layi Alhaji Tasiu ya kawo su yana so ya fadawa Wasila munufarshi a kanta ya kasa wani irin kwarjini take masa shiyasa har ya yanzu ya kasa tunkararta yana kallon yanda abokansa ke shakawata da mata sam baya sha'awa amma yanzu ganin Wasila ya sanya yaji yana sha'awarta kuma ya daura aniya a kanta insha Allahu sai ya dandani zumarta yaji ya take....Dama tuntuni Alhaji ma'aruf ke kwadaita masa harkar yana basarwa sai yanzu kuma yaji yana sha'awar yi da Wasila *'Yar gaske!*

****

Bayan mako biyu da faruwan al'amarin Ahamd ya sake fita kamfen dashi da mutanansa alhamdullahi anyi an kare lafiya dan har gidajen redio sai da suka sanyo muryarsa yanda take jawabi da irin ayukan da zaiyi idan Allah ya bashi gwamnati a hannunsa.....Ahamdu yaga masoya ta ko wane bangare dan gurin cika yayi ma'kil! da jama'a 'yan nahiyar birget da kwana hudu, babban abunda zai baka mamaki! shine yanda mata da maza manya da yara suke fitowa suna turmutsutsu da fad'in "Se jam'iyar *CPC* sauyi muke so da *Ahamdu dan Musa* insha Allahu kano takace."

Wasila na zaune kan tabarma anci kwalliya da wani uban les kunnanta da wuyanta gold ne sai sheki yake yi kawai taji muryarsa na jawabi yanda zai kula da gari da ayyukan da zaiyi mutukar Allah ya bashi iko, ta karo murya tana sauraran jawabin nasa da ba'aji sosai sakamakon hayaniyar da tayi yawa, mamaki take ya akayi har ya fita yayi wannan kamfen din basu sani ba.....Cizan lebe tayi ta dauki tafkekiyar wayarta mai tsadar gaske, Alhaji Tasiu ta kira ya daga wayar da sauri tace"Yallabai ka kunna redio kaji abunda ke faruwa mutuminka ya fita kamfen sai alkawarin karya yakeyi jama'ar gari na yi masa ihu.'' Alhaji Tasiu ya kunna redion wayarshi yana saurara......Kiranta ya sakeyi a waya bayan ya gama saurara yace."Yanzu meye matakin dauka." Kwafa tayi tace"Bari bayan sallahr isha'i kazo ka dauke mu muje gidan redion *Salama* zan musu magana idan Allah ya kaimu gobe su sanar da cewar za'a hira dani *Wasila 'Yar gaske* a filin mu Siyasa." Yace." Hakan yayi dai-dai 'Yar gaske insha Allahu zan shigo da wuri sai muje ammafa nima ina da wata bukata da nake nema a tare da ke." Yafada yana wani kashe murya.....Tuntuni ta riga ta gama gane inda ya dosa kawai tana basar dashi ta fahimci yanda yake kulafucinta bai san me cin wannan budurcin nata ba sai ya shirya ji takeyi dashi domin tasan shine darajarta ta gama yawace yawacen ta dawo tilas tasan zatayi aure kuma shine mutuncinta shiyasa take tattala abinta domin ta mika shi ga namijin da yayi nasarar auranta......Amsa masa tayi kawai da shikkenan sai kazo d'in." Alhaji Tasiu ya kashe waya yana me cike da nishadi zai biya bukatarshi gurin Wasila.....A waya ta kira Camas! tace bayan sallahar isha'i ta fito zasuje inguwa. Aikuwa Camas! na idar da sallah tayi kwalliya tayiwa mahaifiyata sallama ta nufi gidan su Wasila mahaifinta na zaune kan tabarma yana shan iska yana kallon fitarta baice komai ba wanda inda dane da tuni ya korata gida amma dake yanzu ta toshe masa baki da kudi shiru kakeji wai malam yaci shirwa.
Chapter 10 · 0% Book details