Sashe 107
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Amadu na gama Jawabinsa gari ya dauka anata hayaniya kowa na fadar albarkacin bakinsa, haka can ma gidan gomnatin Governor Lawan Rabo da mataimakinsa da kuma mabiya bayansu hankalinsu yay bala'in tashi, governor Lawan Rabo ya dinga da ya sanin hukuncin da ya yanke na tura securities da yayi suka dinga harbi, yasan har duniya ta nad'e jama'a ba zasu ta'ba mantawa da zamaninsa, ba, aikuwa yana jikin wannan jimamin kiran mai girma shugaban 'kasa ya sameshi, lallai yau yake so ya nufi Abuja domin yana so ya zauna dashi.
Lawan Rabo ya shiga rudani mutuka yayin da mataimakinsa yayi nasa guri dama shi d'an ba ruwa na ne tunda duk shawarar da zai bashi baya dauka yanzu data kwa'be masa sai y
aje yaji da matsalarsa.
As da sauran jama'arsa ne suka rakashi can fadar shugaban 'kasar.
Duk da suna cikin karkara sai da labari ya samesu, dan Wasila har jawabin mijinta sai data saurara, hankalinta a tashe ta dinga kiran wayarshi domin taji lafiyarsa, wayar bata shiga da alama dai gidan Malam bai da network me kyau.
Sai misalin goma shaura na dare ya shiga gidanshi, yay wanka ya fito palo wanda yay dai-dai da shigowar Khalifa suka zauna suna sake tattauna maganar.........A dai-dai lokacin ta sake gwada kiransa a waya a kaci sa'a wayar ta shiga, zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tace"Habibi sannu da hanya ina fatan ka dawo lafiya."
Yace."Na dawo lafiya lou har yanzu ban samu sukunin kiran wayarki ba."
Tace."Nima tun dazu nake ta neman wayarka network yana hanawa, na saurari Jawabinka dazu kano babu lafiya ashe." Yace."Eh gashinan jama'a nata fama wai sai sun halaka governorn ku Lawan Rabo."
Tace"Dan Allah daina cewa governor mu wallahi na tsaneshi mugu ne." Yace."A haba dai yanzu kin fita daga jam'iyyarsu kenan."? Kamar zatayi kuka tace"Ka bari bana so dan Allah."
Ya dan shafa saisayayyar sumarshi yace."To na bari ina Mommyna." Tace"Tana goye a bayan Bitan." Yace."Wai ita wannan Bitan din bata gajiya da hidima ne."?
Murmushi tayi tace."Mutuniyar kirki kenan." Yace."Ina kaunar matar sosai saboda tana kaunarki gashi yanzu tana gwadawa kan Mommyna." Mirmushi kawai tayi, yace."Kin san wani abu."? Girgiza kanta tayi tana lumshe ido yace."Gabad'ayansu Malam Kawu Habibu Inna Hajara Momynmu da ita Bitan! Dukaninsu zasuje Umara insha Allah sati biyu masu yawa." Wani irin farin ciki ne ya lullubeta kamar tayi masa ihu a wayar sai dai ta daure ta dinga zabga masa godiya da addua muryarta sai rawa takeyi......Yace."Babu komai ai dangina nayiwa meye abin godiya." Tace"Eh duk da haka nagode." Yace."Idan sun dawo zamuje namu umarar." Tace"Tom shikkenan yanzu kuwa zanje na fadawa Kawu wannan albishir din." Murmushi yay yace."Sai Allah ya kaimu gobe ko."? Tace"Tom Allah ya kawo ku lafiya."
Kashe wayar yay yana murmushi, suka hada ido da Khalifa dake zaune ya zuba masa ido, hummm! Wai Amadu ne ke hirar soyayya wanda da idan ance zaiyi sai yace shi bashi da lokacin yin haka.
Murmushi yay yace."Dama kana nan a zaune."? Khalifa ya murmushin takaici yana jan 'karamin tsaki yace."Ai baza ka gane ina gurin ko bana gurin ba tunda idanunka sun rufe."
Ya dan shafa kanshi As'usel da murmushi a fuskarsa yace."Khalifa ina son yarinyar nan wallahi." Khalifa ya mike yana fad'in "Ai ba sai ka fada ba duk ga alamu nan sun nuna." Mikewa yay ya bashi hannu suka tafa suna dariya a tare suka fita daga palon.
Wasila ta sanar da Malam alherin da Amadu yay musu, malam ya shiga tsananin farin ciki mara misaltuwa ya aika aka kira masa Kawu Habibu shima ya dawo gida saboda daurin auran ya tarasu ya shaida musu abinda ke faruwa, Inna Hajara ta dinga rangwada 'buda a gidan tana fad'in "Haihuwa mai rana Yau ni Hajara nice zanje wannan guri sai ta fashe da kuka tana fyatar hanci tace" Allah ya ji'kanka dan uwana insha Allahu kana aljannar furdausi, Bitan tace ta dinga rarrashinta da ta daina kuka domin yin hakan zai sanya su Wasilan hankalinsu ya tashi, da kyar Inna Hajara tayi shiru ta kama Wasila ta rungume a jikinta tana mata addua gami da hud'uba kan zamantakewar aure.
****
Alhamdullhi an d'aura auran Uwani da malam a gidan Kawunta dake Tudun maliki, bayan daurin aurane sai suka kuma nufi can pataskum din domin gaisuwa sannan kuma da dauko amarya, malam sai washe baki yake yana baza babbar riga Shi kuwa Amadu kunya ce take kamashi wai daurin auran Uwar matarshi ake sai dai kawai ya girgiza kansa yana murmushi.
Uwani tayi ado dai-dai gwargwado kuruciyarta ta sake fitowa tamkar bata haifi Wasila ba wani cewa zaiyi yayarsu ce anyi mata kitso da jan lalle tana sanye da sabuwar atamfa 'yar ingila jama'a sun cika gidan Kawu Madu sai hidima ake Kuluwa sai washe baki takeyi tana karbar baki, Kuluwa yanzu ta dan rage kazanta dan Kawu Madu ya soma dawowa hayyacinsa asirin da tayi masa ya karye dan da ya farga da irin kazantar da takeyi yace."Wallahi ta kuka da
kanta idan ya tashi aure zai aure mace mai tsabta 'yar gayu tunda shi ba kazami bane."
Aikuwa Kuluwa ta tsorata sai ta dage da wanka da wani had'e da kitso akai akai kuma garin Allah yana wayewa zata sa brush ta wanke bakinta tun yana futar da jini har ya daina, amma duk da wannan abun da takeyi Kawu Madu bai saduda ba yana nan da bazawarsa 'yar 'kwalisa har sun tsayar da ranar daurin auransu, Kuluwan bata sani ba sai dai jama'a da yawa sun sani shuru kawai akayi mata ana jiran ranar da amarya zata zo aga me zai faru.
Amadu kasa shiga gidan yay sai ya zauna cikin motar.....Kunyar hada ido yake da mahaifiyar matar tashi, to itama Uwanin tunda taji jama'a nata surutu da amabatar sunan mijin 'yar tata sai ta kasa fitowa tsakar gida ta zauna cikin daki abinta
Kawu Madu da kansa ya fita har bakin motar da yake ciki suka gaisa cikin mutuncin da karamci sannan fa mutane suka farga dashi sai suka dinga zuwa daya bayan daya suna gaisawa, ganin hakan kamar bai dace ba yasa ya fito daga motar yana gaisawa da jama'a cikin sakin fuska da dattako.
Karfe shida sun iso gidan......Lokacin Rashida da Wasila sun saka turare mai kamshi a dakin mahaifiyar tasu wanda ya sha jere mai kyau kuma na zamani, katon gado ne da katifa mai kyau sai katuwar sif mai murfi shida akwatinanta akai sai mudubi da drowars guda biyu koran kafet ne malale a dakin labule koraye da net dinsu, dakin yayi kyau sosai.
Su Kuluwa da Ina Tabawa da Ita mai waina suka rako Uwani dakinta Bitan ta karbesu hannu bibbiyu aka gaisa cikin mutunci da mutuntawa............Wasila bata samu sun ke'be da mahaifiyarta ba ya dinga kiranta a waya ta fito su tafi saboda dare ya soma yi....Uwani tace"Ki shige ku tafi daga baya sai ki dawo ina laifi ma da ya barki kikayi kwanaki biyu, Babu yanda ta iya haka tasa yara suka dauki jakar kayanta Rashida kam fujirewa tayi wai tunda babu makaranta ba zata bisu ba sai jarrabawarsu ta fito, Uwani kam bata ce mata komai ba itama zata fiso ta zauna a gabanta.....Wasila ta fito tana sallama da jama'ar dake gidan duk zuciyarta babu dad'i Inna hajara tasa yara suka fitar mata da kayayyakinta wajan motar......Ita Kuluwa fad'i take "Kice ina gaisheshi." Wasila ko kallonta batayi ba ta fice daga gidan, sukayi karo da malam zai shigo sai ta zube a kas tana kuka, Yace."meyasa kike kuka Wasila. Tace"Wallahi Kawu bana so na tafiya yau." Yace."Kiyi hakuri kibi umarin mijinki Allah yay miki albarka." Ta amsa da amin tana mikewa, Yace."Ina Rashidar."? Tace"Wai anan zata zauna sai sanda jarrabawarmu ta fito." Malam yace."Zancan banza zancen hofi! jirani anan na fito da ita."Ya shiga gidan yana baza babbar rigarsa, Rashida na dakin Uwani malam ya shiga gidan yana fadin"Ina Rashida. tace."Gani Kawu." Yace."Maza ki fito ku tafi ni bana son shashanci." Tace."Kawu Uwani ce tace."Na zauna." Sai ya daga labulen dakin yana fad'in "Uwani anya hukuncin nan yayi dai-dai kuwa."?
Ta dago kai ta kalleshi tace" Malam ai ba cewa nayi ta zauna gabadaya ba idan jarrabawarsu ta fito zata tafi."
Yace."To! to ai babu komai Allah ya kaimu." Labulan dakin ya saki Ya nufi dakin Bitan! lokacin ita kuma tana kicin tana ta kokarin raba abinci dan su Kuluwa suna nan basu tafi ba sai gobe tukkuna.
Dama tuntuni Garba ya shigar mata da kayanta cikin motar daga ita sai baby zahra da jakarta ta nufi motar, wanda yana hangota ya bude motar yana kallonta har ta 'karaso ta shiga tana kumbura fuska, baice mata komai ba ya mayar da murfin motar ya rufe, Garba ya shiga da sauri yaja motar suka dauki hanya.
Baby zahra ya kar'ba daga hannunta yana mata wasa sai kyalkyala dariya takeyi,
Yace."Momyna nayi missing dinki da yawa amma na lura ke da momynki baku damu dani ba, kunyi ki'ba kunyi lafiya kwana biyu."
Kallonsa tayi tana dan sassauta murya tace"Allah Habibi ka yanke min jin dadina ina tare da 'yan uwana kawai sai kace lallai sai mun tafi."
Yace."Akwai wani jin dadi wanda ya wuce ace kina tare dani."?
Shuru tayi masa tana gyara fuskarta, Yace."Ina Rashida."? A hankali tace"Wai ba zata dawoba sai jarrabawa ta fito." Yace."To karatun isilamiyyarmu fa." Ajiyar zuciya ta sauke tace."Ni na ma
nta ma wallahi sabida bana cikin nutsuwa kuma dai Uwani ce tace dole sai ta zauna."
Yace."To tunda Momy ce ta yanke wannan hukuncin bani da magana amma dai naso ta dawo yanzu domin mu had'a izifi talatin d'inmu da ita."
Tace."Itace ta jawowa kanta, idan ta dawo na koya mata inda aka wuceta." Yace."To malama." Shuru motar tayi na minti biyar ya dan kalleta yana kashe ido yace."Wane tanadi kikayi min." ? A hankali yay maganar saboda Garba. Fari tayi da ido tace" Kabari muje zaka gani."
Ya sauke ajiyar zuciya a hankali yana Allah Allah su sauka gida yayi masifar d'okanta da kasantuwa a tare da ita.
A daran ranar sunyi soyayya sosai wacce ta sanya su zubar da hawaye dukaninsu suka tabbatar wa da kansu cewar idan babu d'ayansu a cikin rayuwarsu to babu shakka rayuwarsu tana cikin kalubale mai girma.