Sashe 31
Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read
Camas! tayi kwata'kes! itafa duk ta susuce! komai na gidan Ahamdu ya tafi da imaninta kai shi kanshi ma so take taji yanayin Jijiyarsa a jikinta sha'awarsa takeyi sosai da sosai.
"Tabdijam! amma mutumin nan ya karya miki alkadari sai da aski yazo gaban goshi sannan zai miki haka wallahi ki san yanda zakiyi ki fece! daga hannun wannan mugun mugunta zai miki Jiya da muka zauna metteng Governor yake cewa mutukar ya sake samun hawa kujerar mulki ke zai baiwa mukamin mai bashi shawarwari! saboda ya yaba da kokarin ki a wannan tafiyar shine dalilin da yasa ma nayi duk yanda zanyi na shigo gidanan domin in shaida miki abinda ke faruwa Governor da sauran 'kososhin gomnati hankalinsu ya tashi da faruwan wannan al'mari sunce kuyi kokari ku kufce daga hannun Ahamdu ya aure ki ne ba kyakkyawar manufa ba, kuma kema ki zauna kiyi nazari da kyau ki gani sai da dadin yazo sannan zai miki wannan wulakancin ai wallahi ki nemi mafita tun kafin dare yayi miki.
Wata zazzafar ajiyar zuciya ta sauke tace" Camas! na rasa yanda zanyi da mutumin nan Ahamdu! duk inda kike tubaninshi ya wuce nan wallahi! mugu ne! duk wata kafar mugunta da kika sani ya santa, tsakankanin kwanaki biyar din nan ni kadai nasan irin wuyar dana sha a hannunsa sau biyu yana sumar dani.......Har jinya na kwanta, yau ne kawai na dan samu sauki in kin lura zaki gani, babban tashin Hankalina Uwani da Rashida duk da nasan akwai kayan abinci a gidana babu wannan matsalar to amma nasan suna can hankalinsu a tashe saboda rashina."
Camas! tace"Gaskiya kam hankalin Uwani ya tashi sau biyu muna zuwa gidanan dasu bamu samu damar shigowa ba to amma jiya naje can gidan naki na kwantar musu da hankali nace yau zanyi duk yanda zanyi na samu ganinki, A nan take shaida min cewar itama taje Can garinku Garko tayi wa mai allo wankin babban bargo sam! itama bata maraba da wannan auran naki."
"Ai ki bari kawai Camas! babu babban wanda ya cuce ni irin mutumin nan ni nafi zargin kudi ya kuza masa shiyasa yayi min wannan wulakancin......Wai kamar ni budurwa a bani sadaki na dubu biyar wulakancin yayi tsanani."
Camas! tasa dariya tana fadin"Ta'b! amma gaskiya tsohon nan bai da *M* Yo ko ni da nake a fanko ai ba zanyi arha irin taki ba, Wallahi naci alwashin sadakin aurena sisin gold ne da katuwar mota da katon gida......hahahaha kina nan kina 'boye budurci an bada shi kan mafi karancin kudin hahahaha."! Camas! ta dinga shaka mata dariya har da kwanciya.
'Bata rai tayi tace"Kin ga Hadiza bana son iskanci da rashin mutunci! Ki bar dariya Budurcina nan yanda yake dubu biyar din sadaki nan a ajiye ai na fada masa da auran da babu duk daya suke a gurina kar ma yayi tunanin zai samu budurcina shi kuma mai allo duk sanda na kufce daga wannan gidan to ya kwana da shirin garin Garko sai anjimu dashi."
Camas! tace"Da kyau! kawata yanzu wane mataki kike dauka na kubutar da kanki daga hannun *Ahamadu Musa."?*
_*Yawo babu takalmi a cikin ruwa yakan jawowa mace babbar illah! 'Yar uwa ki lura da kyau! Sanyi na saurin shiga ta kafafu ba zaki gane haka ba sai ranar da ya soma yi miki illah! ki tsare jikinki idan zakiyi aikin ruwa kina kokarin sanya silifas domin kare kanki da lafiyarki*_
Littafin na kud'i ne.....!
Kika futar min da book ke da Allah kika karanta baki biya ba kema ke da Allah! Whasap numbar.
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*
[07/08, 11:50 pm] +234 803 238 4602: 'Yr Bngr Sys
*29*
''Kin san Allah Camas! na rasa wane mataki zan dauka na rasa wane tunani zanyi duk kaina ya kulle dana sa'ka wancan tunanin sai na warware yanzu ni ban san yanda zanyi na gudu daga gidanan ba, Ke da kanki kinga irin matakan tsaron daya zuba a gidanan da kyar suka barki kika shigo kuma ina jin sanda yake ce musu mutukar suka bari na fita daga gidan to a bakin aikinsu kuma sai ya dauresu.....Shiyasa jikina yayi sanyi na rasa wane mataki zan dauka a kanshi.
Camas! tace"Kina da kudi a accont dinki ko."? "Sosai kuwa ni ban san ma a dadin su ba." Shikkenan ai magana ta kare kud'inki zasu share miki hawaye.....Kin san abinda zamuyi yanzu."? Girgiza kai tayi, Ki bani Atm d'nki a ciro kudi masu kauri muzo mu yaudari masu tsaron kofar gidan na lura suna da bala'in son kudin tsiya tunda dubu ashirin kacal na basu suka amince su cuci ubangidansu ina mai tabbatar miki da cewar kika basu dubu dari ko dari biyu zasu san yanda za'ayi bi futa daga cikin gidanan ba tare da kowa yaji ya gani ba sai yasu yasu."
Wata ajiyar zuciya ta sauke mai sanyi a take taji zuciyarta tayi wasai! da jin wannan magana ta Camas! tace"Haka za'ayi wallahi ni ko nawa suka ce zan basu amma kin san inda gixo ke sa'kar tun sanda nazo ya dauke mim pose da wayoyina Atm dina na ciki yanzu ya za'ayi."? Camas! tace."Kinji wata matsalar kuma ko da yake babu damuwa nasan idan na sanar da As abinda ke faruwa ko nawa ne zai bayar saboda shima ya damu da rashinki wallahi baki ga yanda duk ya susuce ba."
Da sauri tace."Yawwa Dan Allah ki mai magana Camas! kuma ki shaida masa cewar wallahi ina fitowa to ya sanya ranshi cewa na zama tashi nayi masa wannan al'kawarin." Camas! tace"Kar ki samu damuwa kawata ni zan tafi, kinga har na wuce mintinan da suka bani." Mikewa tayi tana fadin"Don Allah ki gaishe min Da Uwani kice su kwantar da hankalinsu insha Allahu zan fito da wannan kurkun dana fada."
Suna fitowa harabar gidan suka hada ido da Abdulmumini dake bawa shukoki ruwa yayi maza ya ajiye abinda ke hannunsa ya karaso inda take "Madam! akwai abinda kike bukata ne."? Harara ta watsa masa " Bakuwa nayi ko itama bani da damar yi mata rakiya."? Girgiza kansa yayi ya koma bakin aiki. Tsayawa tayi ta fasa raka Camas din bakin gate dan ta lura yaron kamar munafiki ne me yiwuwa idan mai gidan ya dawo ya fada masa ta fito yanxu har shakkarsa takeyi saboda tana jin tsoron kar ya kara yi mata sha'kar mutuwa shiyasa take kaf kaf dashi.
Abdumumini yana bawa shukoki ruwa hankalinsa na kansu amma sam ba zaka fahimci hakan ba......''Camas! Ina ganin da kaina zan fara aiwatar da wannan aikin kafin ki sake dawowa ni zanyi kokari gurun ganin na kar'bi pose dina a gurinshi zan fara yi musu bayani duk sanda na samu sarari."
Camas! tace"Yawwa kema kiyi kokarin yin haka nima mybe jibi ki ganni." Shikkenan ki gaida gida dan Allah kar ki manta da sa'kona gurin su Uwani." Camas! tayi gaba tana fadin"Insha Allahu daga nan can zan wuce domin na isar da sakonki."
Abulmumini na ganin Wasila ta koma ciki sai yabi Camas! da kallo har ta isa bakin gate yana kallon sanda ta dan tsaya suna magana da Sundu'ki! na minti biyar kana taga ya bude mata karamar kofa ta fita....Al'amarin sai ya shiga bashi mamaki ya akayi suka bar wannan 'yar iskar matar ta shigo gidan da kagani ba mutuniyar arziki bace amma babu shakka zai sanya ido sosai a kan lamarin domin shi ba zai yarda a cuci mutumin da ya rufa masa asiri ba.
****
Malam mao allo na komawa gida ya sanya babban danshi ya kira masa Kattime da Habibu domin ya shaida musu abinda ke faruwa.....Lokacin da ya gama zayyane musu irin tujarar da Uwani tazo tayi masa cikin almajiransa, dukaninsu sai suka hasala suka dinga zagin Uwani suna tsine mata, ganin yanda suka fusata yasa ya dakatar dasu da fadin"Ku saurara haka, sukayi shiru suna sauraransa sai mai da numfashi suke....Yace."Idan anbi ta 'barawo to abi ta mafi sahu! hakika muma muna da laifi babba kan wannan al'amarin da yake faruwa, Banga laifin Uwani ba akan abinda tazo tayi min na gane gaskiya kuma na amsa laifina da bamu wofintar da Yayan nan ba da babu abunda zai sanya ta samu damar zuwa cikin almajirai na ta fada mun magana, To d'an adam ajizi ne munyi kuskure sai dai mu kiyaye gaba kuma ni babban abinda ke daga mun hankali anan shine kada ta samu nasarar kashewa wannan yarinya auranta shine babbar damuwa ta."
Kawu Habibu yace."Insha Allahu hakan ba zata faru ba ni da kaina zan kira Alhajin a waya na shaida masa abinda ke faruwa." Malam yace."To alhamdullahi ga hanya mai sauki dama ina ta tunanin ya za'ayi mu sadu dashi tinda da numbar wayarshi kirashi yanzu sai muyi magana dashi.
Habibu ya fito da gudar dari biyu ya baiwa Musa babban yaron malam yace ya siyo masa kati can bakin kasuwa, Ba tare da bata lokaci ba Musa ya karbi kudin ya kama hanya ya tafi.
Suna tsaye tare da Khalifa cikin babban boutique dinshi mai suma *A M B* ma'aikata sun kai talatin ko sama da haka suna ta sauke kaya da alama an shigo da sabbin kaya....Shiyasa gurun ya hargitse da yawa, Wayarshi dake hannun Garba ta soma ringing, Garba Yayi saurin mika masa wayar ba tare da ya kalli mai kiran ba ya daga da sallama a bakinsa.