← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 91 OF 108

Sashe 91

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

goge fuskarsa.....A sanyaye ta mi'ke ta isa inda yake tsaye ta 'karbi towel din hannunsa tana so ta goge masa jikinsa, sai kawai ya bar mata gurin, Ta bishi da kallon mamaki yaje ya nemi guri ya zauna gefan gado yana shafa vasillin a jikinsa, ba tayi zuciya ba ta isa inda yake a hankali ta sanya hannunta ta 'karbu vasilin d'in tana marairaicewa, Ya mi'ke kawai ya barta a gurin........Wardrobe ya nufa domin daukar jallabiyarsa, da gudu taje ta rungume faffad'an bayansa tana shashshekar kuka tace"Kayi hakuri kaji." Ajiyar zuciya ya sauke yana dan jin sassauci cikin zuciyarsa, shima dik abinda yake daurewa kawai yake yi yana dai so ya nuna mata kuranta ne, amma ba dan ya cuzguna mata ba, idan da ta kwantar da hankalinta shima ai yasan abinda yake yi ba zai ta'ba cutar da ita ba, amma ranar nan ya kwadaitu da ita mutu'ka ya kuma nemi ta a gaza masa ta'ki! dashi d'in manemin matane to babu shakka a ranar sai yaje ya biyawa kansa bukata amma haka ya hakura ya cireta daga cikin ranshi duk dan ya nuna mata kuskuranta

A nutse ya jiyo da ita suna fuskantar junansu, kasa hada ido tayi dashi ta sunkuyar da kanta 'kasa tana goge fuskarta, a hankali ya sanya hannunshi ya goge mata hawayen fuskarta ya tallafo fuskarta sosai cikin tafin hannuwansa ya kallonta.
Takasa d'aga kanta ta kalleshi saboda kunya da kuma tsabar kwarjin da Allah yayi masa.
Murya a kasa kasa yace."Me kikayi min kike bani hakuri."? Sai ta dago fuskarta tana kallonsa.

Ya sanya d'an yatsansa saman le'banta na 'kasa yana shafawa a hankali a hankali shi dai yana masifar son le'bunanta.

Kasa cewa tayi komai ta maida kanta 'kasa tasan yana sane yake tambayar ta yafi kowa sanin kan abinda yasa take bashi hakuri.
Murmushi yayi a hankali ya cika fuskarta ya juya ya dauko jallabiya cikin wardrobe yana fad'in "Ina momyna ko tayi bacci."? A hankali ta d'aga kanta tace" Yanzu nan na lalla'bata ta kwanta.....Hannunta ya ri'ke yace."Muje parlo yau ke zaki bani abinci a gajiye nake."

Taji dad'in yanda ya saki jikinsa sosai wannan ya sake tabbatar mata da cewar ya hakura da fushi da ita kuma ta lura dama kamar daurewa kawai yakeyi yana hakuri.

Ya zauna kan kujera yana dan dubawa babbar wayarshi yace."Ki had'o abincin ki kawo min nan zanci." Da sauri ta nufi daining din ta had'a mishi abincin komai da komai ta kawo gabanshi ta ajiye......'Kasa ya sauko hankalinsa na kan wayarshi yana dan juya abincin da cokali, sai ta kar'bi cokalin ta fara d'ebo abincin tana sa masa a bakinsa.......Kar'ba ya din gayi ba tare da ya kalleta ba hankalinsa gabakidaya yana kan wani text da Zeey tayi mishi.
Kafin ma ya gama karanta text din kiran wayarta ya shigo wayar tashi.
Dama tuntuni ya goge number ta cikin test dinta ma dan tasa sunanta ne ya ganeta.
Ganin numbarta tace ya sanya shi daga wayar a nutse yay sallama dake hands free ya bud'e Wasila najin muryar Zeey tana fada'in "Ranka ya dad'e barka da dare yau dai naci sa'a an d'auki wayata."
Gabanta ne ya shiga fad'uwa sai hannnta ya soma rawa tana kokarin sanya masa a bacin a baki cokalin ya su'buce daga hannunta abincin ya zube a jikinsa sa kasan gurin.
Dan dubanta yay yana dan gyarawa hankalinsa nakan maganar da zeey ke masa yace."Zainab ya kike ya gida ya kwana biyu."
Zeey tace"Alhamdullhi yallabai Wallahi kwanaki nayi ta kiran wayarka domin nayi maka Allah ya raya baka dauka ba nace to ko wani laifin nayi.'"?
Murmushi yay a hankali ya dan koma saman kujera yace." Ai ke bakya laifi Zainab mybe lokotan da kike kiran wayar ina da uziri ne shiyasa amma nagode kwarai kuma naji dadi da kulawarki."
Zeey tace"Ai har taron suna nazo sai dai ban dad'e ba na tafi domin a ranar ana bikin wata friend dina ne." Yace."Masha Allah kema ai yana da kyau ki futar da miji kiyi aure Zeey kin kwana biyu fa."
Zeey tayi dariya me shashshe'ka tace"Yalla'bai kenan aini da aure sai dai inga anayi namiji daya nake so a duniya amma ya'ki aurana."
Yasan inda maganarta ta dosa sai ya nuna bai gane komai ba, Yace."Zeey meye abunki? kina da ilimi sosai kana kina da kyau dai-dai gwargwado me kuma ake nema."?
Murmushin takaici Zeey tayi tace"Duk da ina da abubuwan da ka

fad'a yanzu to shi banyi masa ba."
Dariya yasa yana d'an sosa gemunsa yace."Haba dai sai kace makaho ni da ba dan nayi aure ba da kawai na shigo anyi dani." Zeey tayi wata dariya me shashsheka tana sake ma'kale murya tace"Ashe kasan inda maganata ta dosa tunda naga ka d'auko hanya, Yallabai ko yau kazo ni a shirye nake dama ai Ubangiji cewa yay kuyi Hud'u mutukar zakuyi adalci." Ya bud'e bakinsa zaiyi magana yaga ta jefar da cokalin hannunta ta mi'ke rai a 'bace ta bar gurun......Ya bita da kallo har ta bude daki ta shiga ta bugo kofar da karfin gaske.....sai kawai ya girgiza kansa ya cigaba da hira da Zeey inda take ta tsara masa kalamai ita dole sai ta samu shiga a gurinsa........Yace."Ki bari zan duba maganarki a tsanake zan kira ki a waya." Cike da farin ciki da jin dadi Zeey tace"Shikkenan Yallabai ina sauraranka." Kashe wayar yay ya ajiye ta kusa dashi ya gyara zamansa sosai ya cigaba da cin abincinsa.

Koda ta shiga dakin kwanciya tayi kan bed taci kukanta ta koshi ta kuma dauki al'kawarin yi masa rashin mutunci tunda dai shi bai san hakkin d'an adam ba in bansa wulakanci da rashin mutunci ya rasa ma a inda zaiyi hira da budurwarsa sai gidanshi kuma a gabanta lallai zata nuna masa cewar ta san abinda takeyi duk da take jahila to tasan ciwon kanta.

Sai da ya kammala cin abincinsa a tsanake tukkuna ya bita dakin, lokaci har tayi wanka ta kwanta tana bawa baby zahra nono ta tashi daga bacci, yazo ya tsaya kansu yana kallonsu, ganin yanda tayi bala'in shan kunu ne ya sanya ya kasa cewa da ita komai sai kawai ya tsuguna ya mannawa 'yarshi sumba a saman goshinta ya mi'ke ya fita daga d'akin.

Da 'kyar bacci ya dauketa saboda tsabar bakin ciki da takaici, ta tashi da safe cikin rashin walwala har Hajja ta shigo dakin suka gaisa ta shirya zahra har taso ta fahimci wani abu amma dai ba tace mata komai ba itama so take ta cika ar'bain ta tafi ai tayi abinda tayi, Hajja na fita da Zahra ita kuma ta shiga toilet domin yin nata wankan.
Kafin ta fara wankan sai da ta shiga cikin ruwan d'umi tayi minti goma sha biyar sannan ta fito tayi wankanta da sabulai masu kyau da kamshi ta fito daure da karamin towel iya cinyarta.........Ashe yana zaune a dakin ya shigo tana toliet sai ya zauna zaman jiran fitowarta.......Ganin ta a haka fatar jikinta na wani irin she'ki da sul'bi ga santala santalan cinyoyinta a waje dik sai ya rasa nutsuwarsa ya dinga binta da wani mayen kallo har ta wuceshi ta nufi mirror tana zum'buro bakinta tare da sauya salon tafiyarta.
Kasa daurewa yay ya mi'ke ya nufi inda take......Tana sane ta bude towel din wai zata sake d'aurawa aikuwa ya hangota ta madubi hankali a tashe yaje ya ri'ke towel din yana kokarin fuzgewa daga hannunta.
Ta dan tureshi kadan ta bar masa gurin......Matseta yay jikin wardorbe yana rarraba idanunsa a jikinta..........Ta dinga ture kirjinsa tana son yin kuka amma dai ta daure saboda bata so ya dinga raina mata hankali....."Wai dan Allah meye haka bafa girmanka bane hakan da kakeyi ka kyaleni ni nasa kayana, kuma gidan nan dole ne ma na barshi dan ba zan zauna a inda ba'a bukatar dangina ba.'' A kausashe take maganar tana tuttureshi daga jikinta
Muryarshi ba sosai take fita ba yace."Wace irin magana kikeyi ne waye baya kaunar dangin ki da har kike ikirarin barin gidan auranki."
Sai ta fashe da kuka tana wani irin bubbuga 'kafafunta ta tureshi da 'karfi tana haki ta matsa gefe tana kallonshi tace"Eh dama zaka fad'i haka mana yau kwanan Inna Hajara nawa da tafiya ka ta'ba tambayata dalilin tafiyar ta!? Sannan yau kwanana nawa da haihuwa me yasa baka ta'ba tunani koda sau d'aya ne kace bari ka tura d'aya daga cikin yaranka domin yaje ya dauko mahaifiyata kan tazo taga abinda na haifa, na sani dama tuntuni na san da cewar baka dauki Uwata a matsayin komai ba dan da ka dauketa da daraja to da duk inda take kaje ka gaisheta da kanka kuma ka shaida mata na haihu da abinda na haifa.....To nagaji ni ba shashasha bace nasan kuma inda ke min ciwo zanyi tafiyata in yaso sai ka auro wacce kake ganin Iyayenta sune dai-dai da kai da kimarka."
Tana gama maganarta ta bude wardorbe ta duba kayanta t

a dauki riga da sket na wani had'addan swiss less ta shirya jikinta duk yana tsaye kamar gunki yana kallonta da mamakin kalamanta, bude kofar dakin ce ta sanya shi dawowa hayyacinsa, yay gaggawar kallon bakin kofar sai ya hango ficewarta daga dakin tare da jan kofar da karfin gaske.

Littafin na kudi ne!
Idan kika futar min da book keda Allah! Idan kika karanta baki biya ba kema keda Allah Whasap numbar
*07084653262*
*BINTA UMAR ABBALE*alliya:
'Yr Bngr Sys
*77*
Ya jima a tsaye a tsakiyar d'akin yana mamakin irin maganganun da yarinyar ta watsa masa, ransa yayi masifar 'baci sosai ashe raini har ya soma shiga tsakaninsu tunda har zata iya d'aga masa murya! gurin magana tana fad'a masa duk maganar da tazo bakinta tana d'aga masa harshe kamar zata zageshi Idan tana so ta nusar dashi abinda ke zuciyarta ai sai tayi masa bayani cikin fahimta ba da irin wannan sigar ba, dole ne ma ya dauki tsatstsauran mataki a kanta, idan dan wannan abun na jikinta take kokarin zaginsa to taje ta ri'ke kayanta zai nuna mata shi d'an halak ne.
Koda ya fito daga 'dakin bai kalli inda suke zaune ba ya wuce bedroom dinsa ransa duk a jagule.
Chapter 91 · 0% Book details