← Book details Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel Local reading mode
READING PART 15 OF 108

Sashe 15

Yar Bangar Siyasa Part 1 Complete Hausa Novel · about 8 min read

*Free Pege16*
Uwani ta fito daga kicin tana fad'in"Da alama dai mutumin nan ya gaji da tsayuwa ya tafi haba! jama'a wai babu dama aga Allah ya rufawa mutun asiri sai a dinga bakin ciki! kiga mutum da rigima haka kawai ka ni'ko gari gari ya gari kazo kace zaka dauke min 'yaya saboda munafurci nasan magulamata ne suka kai masa gulma shine shi kuma ya bazamo babbar riga yazo har gidana ya nuna min iko to ni babu wanda ya isa yace zaiyi min iko da 'yayana 'yan uwana ma ban d'agawa 'kafa ballanta wani saboda haka ke Rashida maza maza ki kira Wasila a waya kice tazo yau d'in nan ta dauke mu a mota mu bar nan tunda har wannan tsohon ya soma zuwa shikkenan kuma zai ta daga mana hankali gwara kawai a nemu mu a rasa a unguwar."
Rashida tace"Ni wallahi tausayinsa nakeji gaskiya Uwani banji dadin abunda kikayi masa ba Kamar uba yake a gurinmu kin tozarta shi a unguwa." '' Ayyo kina so ki nuna min kinfi kaunarsa a kaina ni dana tsuguna na haifeki naci kashinki da fitsarin ki shine zaki butulce min shi me ya ta'ba tsinana miki a rayuwa." Rashida tace"Wallahi kafin babanmu ya mutu ya fada min lokacin da aka haifeni da ya rasa yanda zaiyi da hakika can kauye ya nufa gurin Malam mai allo din ya bashi katuwar tinkiya aka rada min suna da ita." Uwani tayi kasake tana kallon 'yar tata ashe kafin mijin nata ya mutu sai da ya fada musu abubuwan da suka faru a baya....."To ai hakika dama dole ce a wuyansu take idan basuyi ba ai sai a kira ki da shegiya gwara ma ki daina wannan magana dan bayan ya bada tinkiya anyi miki rad'in suna babu abunda ya kuma tsinana miki." Rashida tace."Gaskiya dai ki daina ci masa mutunci." Uwani ta fashe da kuka tana fadin"Sai ki zageni Rashida ki fito fili kawai ki zageni yau naga matsayina a gurin ki shiyasa ni Wasila tafi min ke sau dubu duk abunda tasan za tayi ta faranta min rai shi takeyi duk abunda nace tayi tana yi min babu musu ke kuwa fa sai dai ta nemo kudi kina daga kwance kice, to duk rashin mutuncin da kikeyi min sai na fada mata." Tana gama maganarta ta shige daki tana matse hawaye.....Wayarta ta dauka da Wasilan ta siya mata ta hau kiranta....Lokacin suna tare da mai girma governor suna meeting Wasila taga kiran amma bata dauka ba sai bayan sun fito daga dakin meeting din ta kira ta....Uwani na daga wayar ta fashe da kuka "Wasila maza ki zo gida Rashida na nan tana min rashin mutunci duka na ne kawai ba tayi saboda zuwan Malam mai allo."

Rai a 'bace! ta kashe wayar ta nemi numbar Rashidar.....Rashida ta daga wayar tana zumbura baki "Wallahi Rashida ki shiga hankalin ki! dan Kutumar ubanki me malam mai allon ya tsinana miki da har kikewa mahaifiyarki rashin kunya har kin manta irin wahalar da tasha akanmu ashe dama kika bawa malam din yaci mata mutunci kamar yanda ya saba to wallahi sai ranki yayi mugun 'baci! kan hakan." ''Aunty Wasila ki saurara kiji abunda yake faruwa." Rashida ce ke ta magana amma taki sauraranta sai zaginta take cikin jin haushi ta kashe wayar....Wasila ta tsaya tana mamaki! lallai Rashida bata da mutunci ta gama wahala da ita amma ta kashe mata waya....Mahaifiyar tasu ta kira tace"Kinga Uwani na soma zargin yarinyar nan wallahi harda hadin bakinta gurin zuwan Mai allo gidanan dan haka hankalina ba zai kwanta ba komai dare zan shigo unguwar in daukeku ku zauna cikin shiri." Uwani tace"Nima dama shawarar dana yanke kenan dan tunda malam din yazo nasan sauran ma suna tafe haka kawai su rusa mana rayuwa waye zai koma kauye ya zauna? sai dai duk abunda zasuyi suyi." Duk dai magana ta kare ku zauna cikin shiri." Uwani tace "To shikkenan sai kinzo." kashe wayar tayi ta iske inda Camas take zaune tana kallonta.

Har kusan karfe goma da rabi na dare Garba na layin su Wasila cikin matasa yayi basaja so yake yaga ta inda Wasila zata 'bullo, shiru asalima tunda ya zauna ko kare bai gani ba a bakin kofar gidan nasu.....Yananan zaune mutane suka fara raguwa saboda dare kowa na tafiya gida shima sai ya yanke shawarar tafiya dama a Mashin yazo roba roba ya sanya mukuli zai kunna kenan ya hango tawowarsu Wasila jikinta sai walwali ya keyi kasancewar material din dake jikinta mai kyalline wani bala'in kamshin turare ya bakunci hancinsa lokacin data giftashi ta suka shige ita da Camas! wace ta nufi gidansu ita kuma ta hau buga kofar gidan......Matasan dake kusa dashi ne suka fara magana kasa kasa..."Shegiya karuwa kawai ina su Mado nanan da sunci ubanta ta gama guje gujen ta dawo karuwar banza da wofi! ai sai munci ubanta wallahi." Zaginta sukeyi suna kwashe mata albarka garba na jinsu bai ce komai ba yana nan zaune yaga sun fito ita da sauran mutanan gidan.....Gidan suka kulle suka wuce simi simi kamar munafuka...nan yaji matasan dake kusa dashi na fad'in"Ai babu matsiyaciyar uwa sama sa wannan matar duk itace ta sanya ta take wannan rashin mutuncin dazu fa wan mahaifinsu ne yazo suka rufe masa kofa ai wallahi mun kusa tashin su daga unguwar nan." "Kai kasan me zamuyi ma yanzu."? girgiza kai yayi yace." Kone gidan zamuyi dan uwarsu in sun dawo su kwana a waje." Kai wannan shawara tayi kyau abokina." Tafawa sukayi suka mike tare.....Garba ganin sun bar gurin sai shima ya hau mashin dinsa yabi bayan su Wasila can ya hangosu tsallaken titi inda tayi parking din motarta suka shiga a take ya bi bayansu amma yanda yake binsu a hankali ba zasu dauka su yake bi ba.

Dake unguwar masu hannu da shuni ce ko ina haske babu duhu da tarin kazanta daga can bakin titi Garba ya tsaya ya kafe mashin dinsa a hankali yabi bayan motar inda yaga ta nufi wani estete wanda manya manya mutane ke zaune a ciki Garba yayi mamaki sosai babu shakka yarinyar samu kudi ganin motar ta tsaya a bakin gate din wani tangamemen gida ginin zamani, yana kallo mai gadi ya bude gate din ta shigar da motar ciki, sai ya juya da sauri ganin sucurity na nufowa inda yake, da sauri ya tashi mashin dinsa ya bar gurin a guje......A daran ya shaidawa Ahamdu unguwar da Wasila take sam baiyi mamaki ba saboda yasan zasu iya yi mata abunda yafi haka, kudi ne gasu nan a banzace ayi abunda ya dace an'kiyi ana watsar dasu a banza a wofi jirgin sama ma zasu iya siya mata mutukar bukatarsu zata biya.

Uwani da Rashida suka gigice ganin ubangidan da Allah ya mallakawa Wasila suka dinga shige da fice a gidan suna ta'be ta'ben abubuwa Uwani dai kusan zautuwa tayi saboda ta masifar rudewar da tayi taga uwar daula da duniyar da 'yarta ta cikinta ta samu.....Wasila tace "Ko wanne ya dauki daki daya ya ishe shi bukatar rayuwarsa Uwani kinga Abunda Allah yayi mana ko? da kina cewa muje muyi karuwanci shine zamuyi kudi da gaggawa to wannan sana'a da nakeyi mutukar ta karbe ka nan take zakayi arziki yanzu ina da kudi cikin account dina da ban san a dadin su ba kullum 'yan fadar mai girma governor tura min kudi suke bamu da matsalar komai a halin yanzu Allah ya yaye mana kuncin talauci ba tare da mun aikata sa'bo ba.

Uwani tace" Sai yanzu kuma na gane abunda kike nufi Wasila wallahi ni a daukata yanzu babu abunda ke saurin kawo kudi da gaggawa kamar karuwanci ashe akwai sana'ar da tafi wannan to Allah nagode maka da bai sa kun dauki gurguwar shawarar da nake baku ba."

To a ranar dai da kyar su Uwani sukayi bacci dan Wasila dakinta ta shige tayi wanka tayi kwanciyarta bacci mai dadi ya dauketa........A furgice! ta bude idonta tana salati! ta sanya hannu ta kunna fitilar gefan dago tana bin dakin da kallo kamar me neman wani abu....Kafafunta ta zuro kasa suka sauka kan kafet, ta jima a haka kafin ta mike ta nufi toilet fitsari kawai tayi ta dawo ta kwanta ta rufe jikinta da bargo amma banda fuskarta ta kasa kashe fitilar dakin tayi domin gani take kamar zai iya mamayarta kamar yanda ya mamaye ta cikin mafarkinta na yanzu, Tun da take a duniya ba ta'ba ta'ba mafarki wani d'a namiji ba sai yau! shin wai wannan mafarkin me yake nufi ne? meye ala'karta da wannan guy? ita dai tasan ba'kar gaba ce tsakaninsu to mai zai sanya yazo mata a mafarki yana mata murmushi saboda kuma tsabar wuce gona da iri har ya rungumeta yana tatta'ba mata sassan jikinta....Tayi sauri ta sanya hannunta a ramin cibiyarta sai taji tamkar hannunsa ne a gurin a lokacin da yake shafa mata cikin mafarkinta, jin tsigar jikinta ns tashi ya sanya tayi gaggawar cire hannunta daga gurin.....Rufin dakin ta tsurawa ido, itafa wannan mafarkin ya bata tsoro har yanzu tana hango fuskarsa da tattausan murmushi, shin wai abunda tayi masa bai dame shi bane da har zai zo yana mata murmushi, ita ta dauka zasu kulla gaba ne ita dashi wacce tafi ta da tsanani!!!!!!! Juyawa tayi ta rungume pillow tana lumshe ido....."Subahanallahi." Hannunsa taji a jikinsa ta mike a zabure! tana dube dube a dakin........Yau satin ta daya a gidanan amma bata ta'ba shiga tsoro da farga ba irin na yau! mikewa tayi ta zura hijab! ta bude dakin ta futa....Dakin da su Uwani suke nan ta nufa, gani take kamar in ta zauna a dakin ita kadai mafarkinta zai iya tabbata.....Duk suna tare dake bed din babbane su Rashida da Uwani anji Ac sai bacci akeyi, ta samu ta ra'be gefensu ta kwanta had'e da takure jikinta guri guda.......Ta jima a haka kafin bacci ya dauketa.
Chapter 15 · 0% Book details